[9:12PM, 9/14/2016] Rash Kardam:
’YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU
NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-126~130.
Hajiya Suwaiba suna komawa, suka
sanar da Mum d’in Umar yanda sukayi,
tayi mamaki sosai ashe da gaske haka
halin Gwaggo yake. Nan tace” hmm ni
gwanda His Excellency ma ya dawo ayi
bikin, yarinya ta huta.
Hajiya Suwaiba tace”yaushe zai dawo?
Mum tace” nan da 5days zai dawo. Hira
sukayi tayi da yanda biki zai kasance.
Gwaggi ko ta hana su Malam bacci sai
ihu take, ko sallah anki bud’eta tayi.
Khadi tayi murna tayi godia ma Allah da
zab’in da ya mata, take ta kira su Farhat
B Haske ta fad’a mata, Farhat ma take
bata labarin tayi sabon saurayi, Sunansa
Abdul-wasilu Humble, Khadi ta mata
fatan Allah ya dai-daita su.
Tana kashe wayar ta kira Queen Neenah
ita ta fad’a mata, daga nan takira Hajiya
Jamila Abubukar ta sanar mata, tayi
murna sosai da sosai, takuma bata
shawarwari da yanda zata kula da Umar
kasancewa Hajiya Jamila ta girmesu,
tana kwance dasune don taga suna da
hankali shiyasa.
Malam ganin iskanci Gwaggo zai wuce
gona da iri, da safe yaje ta windoq duk
ta wargaza d’akinta, yace”Hauwa ki
nutsu, wallahi kinji na rantse, matsawan
baki bar haukan da kike ba to yau zan
rubuta miki saki, don ba za’azo biki ina
matsayina na Surkin Gwamna a ga
mahaukaciya a gidana ba, kuma
haukanta akan bakincin take ma Surkan
Gwamna. Ni Rash nace”hmmm Malam
da biyu yayi maganan nan, don ya kuna
Gwaggo ne.
Gwaggo tace” eh dole kace haka ae dama
baka sona don yanzu kaga Khadi zata
auri d’an Gwamna dole kamin haka.
Malam yace” kene bazaki gane ba ina
sonki sosai, halinki ne bana so, ya fita
abunsa.
Gwaggo jin saki ta nutsu ko da tafito,
jummai k’anwarta tayi mata nasiha
tace”Yaya matsawan baki kwantar da
kai ba, ina fad’a miki zaki wahala don
yarinyan nan tayi gaba. Kiyi hak’uri
kawao.
Gwaggo tundafa wannan rana ta dawo
kamar bata gidan yanzu bata dai
magana da Khadi, amma ta bar
hantaranta ko sabganta tabar shiga.
Khadi ko kulum suna mak’ale da waya
ita da Umar, suna waya ne yace”gobe
Dad zai dawo ki shirya, in ya dawo ke da
Beebah zakuzo ku gaidashi.
Cike da murna tace”sai mun tambayi
Baba in ya barmu.
“Kedai nasan Baba bazai hana kizo ki
gaida Surkinki ba. Haka sukayita
hiransu mai cike da ni shad’i.
Washe gari da safe inna ta d’aura ruwa
a hita, dai-dai kusa da d’akinta a kwai
soket, ya tafasa ruwan ta kashe, taje
d’auko boket kenan ta sukuya tana
d’aurayewa, sai tebur d’in ya karye yana
shirin zubowa akan Gwaggo.
Khadi tafito da ga d’aki karaf idonta ya
sauka akan tebur, “kira ta kwala ma
Gwaggo, ganin bata gane mai take nufi
ba, da sauri tayi gun don ceton Gwaggo.
Tana zuwa ta ture Gwaggo ta hantsula
gefe kagin ta kauce ruwan ya juye mata
ajiki, wani razanane k’ara tasaki, ta
fad’i agun tana shure-shure. Gwaggo duk
ta rikice, Beeba da Rabee sai Jimmai
kanwar Gwaggo suma ihu suka saki, ana
haka sai ga Mal da gudu yayi kan Khadi,
wanda azaba yasa ta suma, d’aukarta
yayi waje yafita da gudu yashiga Napep,
Gwaggo ma da gudu duka bisa, Beeba
kam sai kuka take, tana fad’i”wayyo
Adda na!. Gwaggo sai hawaye takeyi,
tabbas yau Khadi ta gwada mata yar
halak ce ita, gashi taje ceton rayuwana
itakuma zata rasa nata. Tabbas yau na
yarda da kalman nan ta ‘YA’YA DA
DUKIYA BA’A K’ETARSU, bakan wanda
zai tai makeka ba.
Suna isa asibiti Dr Abdul suka samu
gani halin da take ciki, akayi Emergency
da ita, wayan Dr Umar yakira.
Dr Umar suna Airport shida Mum da
Ilham sunje d’auko Dad d’insu, don har
jirginsu ya sauka, Dad ya sauko kenan,
sun rungume juna, wayar Dr Umar tayi
k’ara gani Dr Abdul yasa yad’aga da
sauri “hello yace”.
Daga d’aya ban garen Dr Abdul
yace”kana ina, kazo ba lafiya Khadijat ta
kone bansam ko garin yaya bane, amma
ina zati ko Gwaggo nane ta konata
sabida halinta.
“What ina bazai yuba sai na d’au
mataki.
Mum tace”Kai da wa?.
Cikin muryan kuka ya fara basu bayani,
His Excellency yace” what muwuce
Asubiti yau matan na zata gane ita
bakomai bane.
Suna zuwa Asibiti ta ko ina ya amsa da
jiniya.
Dr Umar da Gwamna da gudu suka fita
duka shiga Emergency, Umar na ganin
halin da Khadi ke ciki, kara ya saki ya
fad’i sume. Mum da Ilham sai kuka suke,
Gwamna ya fita kiran Doctors suka d’au
Umar shima. Yana fitowa yaga su Malam
yace”ina Gwaggo da take?.
Malam ya nunata da yatsa, His
Excellency da gudu yayi kanta wani
damka ya mata, ya fara kwara mata
kyawawan mari, yace”wallahi in har na
rasa d’ana d’aya tilo, da abar qaunar sa,
to kema sai kinyi mutuwar wula kanci.
Kisani ‘DA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU.
amma ke munguwa nai bakin hali zaki
gane kurenki. Ball yakeyi da ita, yana
fad’an magan ganu, da kyar aka rik’e
shi, sijoji yace atafi da ita CID agana
mata azaba. Basu tsaya jiran komai ba
Women police suka d’au Gwaggi sama
aka sata a mota, aka nufi CID da ita.
Ni ko Rash tsaban gulma ina leka motar
naga bakin Gwaggo har ya kun bura,
fiskan taji marin manya, tamkar ba
Gwaggo mai bala’i ba.
ﺭﺷﻴﺪﺓ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻛﺮﺩﻡ
[9:12PM, 9/14/2016] Rash Kardam:
Tuesday, 18 April 2017
Home »
» 'YA'YA DA DUKIYA.... 126-130
'YA'YA DA DUKIYA.... 126-130
Popular Posts
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(AUGUST 2016)* ...
-
MOTAR KWADAYI RASH KARDAM Duk launin kalan idonta, sun canza izuwa ja. Hannu tasa a tsakanin cinyanta tana mammatsewa,Bad Boy yana ga...
-
AMANA TA CE By ©Rash Kardam 1 Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassa...
-
🐾🐾Raheenat🐾🐾 1 Yarinya ce yar kimanin shekara 12 ta yanko a guje ta fada jikin Dad...
-
MOTAR KWADAYI By Rash Kardam 21-25 Jan motar yayi, suka bar cikin Silver Sand Hotel, bai zarce da su ko ina ba, sai gid...
-
BAZATA By ©Rash Kardam 1 Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan l...
-
[6/5/6:30pm] 🌲RASH KARDAM🌲🌲 & 🎋SADEEY S ADAM🎋 ...
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(JULY 2016)* ...
0 comments:
Post a Comment