YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU
NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Notice
Masu karatu na zansa sunan
littafina daga KHADEEJATUL-KUBRAH
zuwa YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU,
cos Daman YAR’RIKO ne suna Da na fara
sawa, sai aka samu wacce tayi. So yanzu
namar dashi YA’YA DA DUKIYA BA’A
K’ETARSU. Yafi ma’ana kuma sakon
littafin akan haka zai tafi.
Pg-26~30.
Ana kiran sallah tayi d’akin su ta
kwanta, kasanewan garin da sanyi
lokacin hunturu ne. Addu’a tayi ta
kwanta ga yunwar da ke addabarta.
Haka har bacci b’arawo yayi awon gaba
da ita.
Dukun-kune take a yar ta barmata gefe
kuma katifar Beeba ne yar k’arama
wanda mutum d’aya zai d’auka. Bacci
take amma sanyi ya dameta. Kiran
Sallah asuba ya farkar da ita da kyar ta
mik’e ta d’ibo ruwa a randa sai d’ari
take yi. Alwala tayi ta koma d’aki tayi
sallah bayan ta idar ta fara azkar d’in
safiya wani bacci ne ya d’auketa kamar
daga sama taji an shek’a mata ruwa mai
sanyi nan take ta fara d’ari-d’ari, duk da
haka Gwaggo bata kyaleta ba wani
ruwan ta k’ara kwara mata. Barin da
takeyi ya tsananta, Gwaggo tace”ke har
kimsami daman da zaki kwanta bacin
safe, uban wa ya baki dama?.
Malam yana karatun Al-qur’ani mai
girma sai yaji kamar ana hayaniya jin
maganan yayi yawa ya fito, yaji d’akin
su Khadi ne da sauri ya sa kai cikin
d’akin ganin Khadi ta fi luuuu zata fad’i
yaje da sauri yana”Salati ya tare ta fad’a
a hannunsa cikin k’unan rai ya d’ago ya
kalli Gwaggo yace” in kin kasheta ae kin
huta, kin san yarinya tana fama da
Pneumonia kuma yayi mata yawa zaki
kwara mata ruwan sanyi, haba hauwa
anya kina tsoron Allah kuwa ae d’a ko
ba kai ka haifeshi ba, bai kamata kina
wula kanta ta ba.( Yan uwa mata kira
gareku, kune jigon gida duk lokacin da
gida yayi kyau kune, kusani Ya’ya da
Dukiya, da Dabba ba’a mugun tar su. A
rauwa ba kasan wanda zai taimake ba,
sai kaga d’an da ka haifa da cikin ka
wani lokacin bai jik’anka ba, wanda
baka san zafin sa ba ya taimake ka
kuma Ya’ya Rahmane dan Allah kuna
kyautata ma yara ba sai naka ba ku
d’auka duk d’aya suke a gunku).
Gwaggo ko a jikinta tayi waje tana
cewa”ni dai dole ta fito ta min aiki yau
ko ta ji a jikinta. Malam ya kali Khadi ta
idanunta suka kafe a sama da sauri ya
d’auketa ya fita waje da ita. Beba da ta
fito daga d’aki ganin halinda Adda ta ke
ciki yasa tayi gun Malam da hanzari
suka fita dake garin da sanyi da kyar
suka samu mai Napep yace”Yaro Asibitin
Murtala zaka kai mu, Malam da Beeba
suka shigar da ita ciki suka d’au hanyar
Asibitñ, sun d’anyi tafiya kafin suka iso
asibitin, kud’in mai napep ya basa kafin
ya d’auki Khadi suka shiga cikin Asibitin
nurse suna hango su, suka tahoda sauri
suka karb’eta. Emergency aka nufa da
ita, Dr Abdul ke bakin aiki, da sauri
“nurse suka sanar masa an kawo patient.
Yace “ok! I’m coming now”.
Bata dad’e da isa gun su Malam sai ga Dr
Abdul nan ya iso. Dubata ya soma yi
yaga tana wani yanayi numfashinta na
shirin d’aukewa, tai makon gaggawa aka
bata cikin ikon Allah suka samu
numfashinta ya dai-daita. Magunguna ya
rubuta ya mika wa Malam yace”Baba
gashi kaje Pharmacy ka sayo, in ka dawo
ka bawa nurse sai ka same ni a office
d’ina. Malam ya amsa da rawar jiki ya
nufi pharmacy.
Taku a kulum mai k’aunar ku .
ﺭﺍﺷﻴﺪﺓ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻛﺮﺩﻡ
Tuesday, 18 April 2017
Home »
» 'YA'YA DA DUKIYA..... 26-30
'YA'YA DA DUKIYA..... 26-30
Popular Posts
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(AUGUST 2016)* ...
-
MOTAR KWADAYI RASH KARDAM Duk launin kalan idonta, sun canza izuwa ja. Hannu tasa a tsakanin cinyanta tana mammatsewa,Bad Boy yana ga...
-
AMANA TA CE By ©Rash Kardam 1 Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassa...
-
🐾🐾Raheenat🐾🐾 1 Yarinya ce yar kimanin shekara 12 ta yanko a guje ta fada jikin Dad...
-
MOTAR KWADAYI By Rash Kardam 21-25 Jan motar yayi, suka bar cikin Silver Sand Hotel, bai zarce da su ko ina ba, sai gid...
-
BAZATA By ©Rash Kardam 1 Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan l...
-
[6/5/6:30pm] 🌲RASH KARDAM🌲🌲 & 🎋SADEEY S ADAM🎋 ...
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(JULY 2016)* ...
0 comments:
Post a Comment