AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
19
Jikin auta yayi zafi sosai ga ciwon mara, ammar duk ya rude yarasa me ke masa dadi ga kudinsu ya kare gefen wani shagon daya ga ba a budewa yaje ya kwantarta lokacin gari yayi haske sosai ya cire yar rigansa na janfa ya luluba mata nan yace auta kiyi hakuri barin fita neman kudi ko zan samu sai in saya miki magani kai ta daga masa hannu sa ta riko cikin muryan marasa lfy tace Yaya na Allah ya ka fita sa’a ya amsa da amin, ya fita
Shagon dako yaje yayi sa’a an kawo kaya nan ya yasoma aikin kwasan kaya tun bakwai yagara sai karfe shadaya ya gama nan aka bashi kudin aiki 200 dake kayan ba masu nauyi bane shiyasa, hamdalla yayi yana shirin barin layin masu kayan zai wuce yaji wasu suna neman mai zubar da shara nan yayi aikin ya gyara musu gurin tass suka bashi 50 daya layin ma sun kitashi nan ya fara musu aiki aka soma kiran sallah ya bari da sauri ya ce zaije ya dawo yana fita chemist yaje yasayo maganin mura dana zazzabi yabi yasayo musu shinkafa auta harda tea irin na masu yawo suna hadawa yasa mata da murna ya kama hanya zuwa gunta.
Futha bayan ta huta washe gari tacr ma Sady tana so su hadu akwai abunda takeson sani, nan sady tace zasu acikin Kad poly haka ko akayi da yamma suka hadu bayan sun gaisa futha take bata lbr abunda ta gani Sady tace nima abun ya daure min kai don pinky bakara min busha take ba kuma Abba na nima yace wai ya sai min mota ba a shigo da ita bace ni kaina futha yanda suke bushasha da dukiyar su Auta abun har na razana ni kuma har yanzu sunki yarda ayi binciken akan wayanda sukayi kisan nan da kuma inda Auta take, futha tace kar kidamu sannu a hankali komai zai zama tarihi Allah ya toni asirin duk wannda keda hannu a wannan al’amarin Sady tace Ameen nan suka yi hira gameda karatu har sai magrib suka rabu.
Baba sani ganin Sady da futha suna neman dinkrwa yasa ya baza mata kan tsaro duk inda sady tayi ana biye da ita don kar futha ta gano sirrinsu don bai yarda da ita da mahaifinta ba suna masa shigan sauri akan al’amarin, su baba isiya yanzu abun nema ya samu hankalinsa kwance ke cin kudin da bana saba har in anzo neman taimako gunsa yana ikirarin sunsan wahalar dayayi yasamu dukiyar su asama kawai suka gansa da kudi, kutaya ni ji wai har yana cewa sun san wahalar dayayi, baba isiya har wani yar tumbi yasaka yayi fresh ko mai ya dai2 har ya manta da wani alhaji Al-hassan.
A bauchi kuwa Ammar da murnar sa ya nufo gun Zee Auta ya musu samuwa don shi ko ta kansa bayayi yafiso yaga ita taci kafin sai yaci, yazo tsallaka titi har ya kusa tsallakawa sai ga wani mai mashi ya yanko aguje ji kake kiiiii mai mashin ya shiga da Ammar da sam idonsa ya rufe baya ganin hanya.
Yan gurin nan suka dau salati suna tafa hannu wasu suka yanko da gudu suka zo ba da taimakon gaggawa Allah sarki kowa da irin jarabawar da Allah ke masa a rayuwa kamar yanda Ammar da Zee suka shiga haka wasu ke cikinta kowa da kalar nasa ya Allah ka jarrabe mu dai2 da karfin imanin.mu Ya Allah kabamu Abin da zamu iya Ameen Ya Allah.
Saturday, 1 April 2017
Home »
» AMANA TA CE 19
AMANA TA CE 19
Popular Posts
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(AUGUST 2016)* ...
-
MOTAR KWADAYI RASH KARDAM Duk launin kalan idonta, sun canza izuwa ja. Hannu tasa a tsakanin cinyanta tana mammatsewa,Bad Boy yana ga...
-
AMANA TA CE By ©Rash Kardam 1 Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassa...
-
🐾🐾Raheenat🐾🐾 1 Yarinya ce yar kimanin shekara 12 ta yanko a guje ta fada jikin Dad...
-
MOTAR KWADAYI By Rash Kardam 21-25 Jan motar yayi, suka bar cikin Silver Sand Hotel, bai zarce da su ko ina ba, sai gid...
-
BAZATA By ©Rash Kardam 1 Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan l...
-
[6/5/6:30pm] 🌲RASH KARDAM🌲🌲 & 🎋SADEEY S ADAM🎋 ...
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(JULY 2016)* ...
0 comments:
Post a Comment