New Post

Tuesday, 18 April 2017

'YA'YA DA DUKIYA.... 6-10

[9:12PM, 9/14/2016] Rash Kardam:
YA’YA DA DUKIYA BA’A K’ETARSU
NA
©RASHEEDAH .A. KARDAM.
Pg-6~10.
Gwaggo sai da tayi likis ma Khadi kafin
ta ky’aleta, tace”wlh sai kin gama
wankin nan yau ko na miki dan banza
duka, sha-sha kawai, mts tayi tsaki ta
nufi cikin d’akinta.
Khadi kam kuka tasha ga wani
yunwan da ke murd’amata ciki. Kama
cikin tayi ta tamke da d’an kwali abunka
da Khadija maganin Maza cikin dakiyar
zuciya ta fara wankin
, da ikon Allah kafin akira Sallah la’asar
ta gama.
Gwaggo ta fito da abinci a d’an
k’aramin kwano wanda ko d’an yaro
bazai ish’esh’i ba. Ta turo mata kwanon
ta juya tayi d’akinta ko tausayin
Yarinyan nan bata ji ba. Ga uban aikin
da ta mata a cikin gidan kamar jaka.
Malam Ahmadu ne ya sh’igo da
Sallamansa, in donsa ne ya sauk’a kan
Khadi dake kwance tamkar wanda aka
d’aura ma dutsin dala da gauron dutsi
aka.
Da sauri ya k’arasa gurinta cike
da tausaya wa, ya tallabo ta yace “Mama
na ya dai? Mai ya same ki na ganki
haka? .
Gwaggo ta fito cike da masifa
tace”komai ne ya same ta ko zaka karb’a
mata ne, sai in sani.
Cike da b’acin rai Malam Ahmad
ya nufo ta, yace”kee Hauwa wlh ki
kiyaye ni zan sas-saba miki akan
Khadija sam ba kya tausayin yarinyan
nan.
Gwaggo tace “ina ko zan tausaya
mata ba sanin zafinta nayi ba bare na
san miye tausayi.
Malam yace”duk aikin da take
yi a gidan baky’a gani ko?. Kuma ba
ky’a sanya yar cikinki.
Wannan yarinya Yata ke a gun mu, duk
irin rikon da muka mata Allah zai
tambaye mu, Hauwa kiji tsoron Allah.
Gwaggo tace”ehehe wa’azi
zakamin ai tsoron Allah kulum cikinta
muke, yar wani ba yata bace nawa
kawai na san, fuuu tayi d’aki in ka gama
sai ka sanar min.
Taku a kulum mai k’aunar ku
ﺭﺍﺷﻴﺪ ﻋﺒﺪﺍﻟﻠﻪ ﻛﺮﺩﻡ

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts