AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
37
Wani mugun kalo yamata, yanzu tsoron ammar ta ke baran da ta tuna nashin da ya mata da sauri ta dawo da baya, ta sauko sai da ta bashi hanya ya fita, sannan ta haura ta debi duk abunda zata diba ta dau poss dinta dake tana da kudi aciki ta nufi asibiti, tana zuwa ta nimi gu ta zauna ta zuba tagumi tana kalonsa, tana fatan Allah yasa ya tashi.
Ammar ko yana fita ya nufi dakinsa ajiye ki din mota, don shikam yabar amfani da abun gidansu kuma yau zaisa afara nima musu gd, don tabbas shine silan ja ma auta wan’nan abun, in da bai yarda yazo gidan nan ba da ahyan bai mata haka ba, ko da ya fita abokinsa auwal ya kira yace masa gd yake so mai dan saukin kudi, amma ba wanda yake da mutane da yawa ba, auwal yace an gama zuwa gobe zakaji “feedback” nan sukayi sallama ya nufi asibiti, yana zuwa yasamu H mamu suna inda suke sun zuba tagumi, nan yaji tausayinta, gsky tayi masa karamci gashi tilon danta na miji ta wasa abunda bata tana zaton zatayi ba, bata so kanta ba ta bama dan ta laifinsa, gaskiya hajiya mamu tacika mutuniyar kirki uwa ta gari, wacce take son yayan wasu ta kuma kula dasu tsakaninta da Allah, Hajiya mamu Allah yasaja miki ya biyaki da rikon gsky da kika mana ameen, amma bazan iya cigaba da zama’a cikin gidan ki ba, don tunda yasoma kuskuranta, nan gaba zaiyi abunda yafi haka ni daman hankalina bai kwanta dashi ba, cikin zuciyarsa yake magana, sai da yaji H mamu tace ammar sannu da dawowa, firgigit ya dawo hayyacinsa, Murmushi ya kakalo wanda yafi kuka ciwo yayi, ammar duk yaba ma hajiya tausayi lokaci daya duk ya canza kamar bashi ba, kausar tamasa sannu, ya amsa ya tambayesu ya mai jiki sukace haryanzu dai ba lbr, kayan ya mika musu yace ya kamata su je gd su huta, h mamu tace ina ae ba inda zata zata kwana da auta, tace kausar taje gd, ido ta zaro don auta bata tsira itama tanaga intaje abunda zai mata kenan bare uwansu badaya bare uba, don da aure a tsakaninsu, ajiyar hrt tayi kafin tace mum kata kafarki, h mamu dake babbace ta gano kausar kuma sai taji badadi azuciyarta danta yau ake gudu,(umm tsakanin uwa da danta sai Allah duk da taga laifinsa amma sai da taji wani iri, yan’uwa ya kamata mu na tausaya wa iyaye mu kyautata musu, don sun sha wahala ba kadan ba akan mu ya Allah kaba mu ikon tausaya musu da jin kansu, kaman yanda suka mana muna kanana Ameen).
Su hajiya mamu da kausar suka kwana a dakin masu jinya, shiko zama yayi a kofar dakin akwai chair azaune ya kwana da safe bayan sunyi sallah yaje ya sayo musu abinci, suka karya sai ga Dr ta zo nan suka gaidata, suka tambayeta ya mai jikin tace musu da sauki nan ta wuce office dinta, wayarsa ce tayi kara yana daga wa yaga auwal da sauri ya dauka, bayan sun gaisa yace my man an samu gida ku biyu ne aciki amma yace min daki2 ne in kana da tym sai kazo muje a nan dutsin tanshi ne, yace ba matsala na gode sukayi sallama ya kashe wayarsa, sai kusan 10 ya bar asibiti direct gun auwal yaje, sun duba gd ba laifi yayi gashi daki dadai ne, ko wan’ne da bayi aciki san’nan akwai kofa a tsakiya, sai ta waje ma akwai kofa kamar na falo ta wajen gidan sai yar karamar gate dake gun, kuma gidan na da kyau sai na dayan yana tsam’manin ciki da falo ne da bayi, sai kitchen da wani karamin daki na saka kaya, dake bauchi muna da arahan haya kudin ba masu yawa bane, 60k ne kawai nan yaga arahansa don inda a kaduna ne abun sai a slow, nan yace zaibada kudin zuwa jimawa san’an yasa aka kira masa almajirai ya biyasu yasa su wanke masa dakin don yau zai kwaso musu kayansu ko gobe.
Yana fita bank yaje ya zaro kudi a account dinsa don duk wata hajiya mamu na sallamansa da 30k kudin da take basa gashi yau kusan shekaran su 2 da wani abu, a gidan kunga ya dan samu wani abu, duk abunda ya kamata ayi anyi, yaje gida dakin auta ya kwaso mata kayan ta dake sif dinta wanda yasan’nata ne, shima ya dibi nasa, ya ajiye, kasuwa ya shiga ya sayo musu katifa manya guda 2, yazo ya ajiye, ya gaji likis gashi yanzu magriba ta kusa duk da yana lekasu ya tambayi lfy auta, yanzun ma asibitin ya nufa.
Munay tana zaune ta zuba tagumi, ahyan yasoma bude idonsa, yana kalon dakin da kyau, sannu a hankali ya komai yasoma dawo masa, kara yasaki yana kiran no! no! no!, ( nikam nace to no! Din na me nene ko yaso sai ya gama biyan bukatar sa ne? oho, ko haushin da mum dinsa ta gansa ne? Oho zamuji koma miye nan gaba).
Taku a kulum mai kaunar ku
Rash Kardam
Saturday, 1 April 2017
Home »
» AMANA TA CE 37
AMANA TA CE 37
Popular Posts
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(AUGUST 2016)* ...
-
MOTAR KWADAYI RASH KARDAM Duk launin kalan idonta, sun canza izuwa ja. Hannu tasa a tsakanin cinyanta tana mammatsewa,Bad Boy yana ga...
-
AMANA TA CE By ©Rash Kardam 1 Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassa...
-
🐾🐾Raheenat🐾🐾 1 Yarinya ce yar kimanin shekara 12 ta yanko a guje ta fada jikin Dad...
-
MOTAR KWADAYI By Rash Kardam 21-25 Jan motar yayi, suka bar cikin Silver Sand Hotel, bai zarce da su ko ina ba, sai gid...
-
BAZATA By ©Rash Kardam 1 Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan l...
-
[6/5/6:30pm] 🌲RASH KARDAM🌲🌲 & 🎋SADEEY S ADAM🎋 ...
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(JULY 2016)* ...
0 comments:
Post a Comment