AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
23
Ganin tayi nisa yasa ya bi bayanta da gudu sukeyi da mai mashin amma ta musu nisa sai da sukaje G R A adjacent da government house naga naga sun nufi wani katon kwalta ne a shimfede kafin suka iso kofar wani hadadden gd harda security a kofar ginan tun daga kwanar shiga gidan zaka ga arubuta Hajiya Maryam Alkali house, da manyan zane, nan ya sallami mai mashin ya basa N100 kudin mashi mai gadi suna ganinsa suka tashi nam sukace wajen wa yazo yace gurin wacce tashiga da mota mai gadi yace ka bar gurin nan bazaka shiga ba nan suka fara iskanci ma ammar ransa har ya baci ya juya zai tafi sai daya mai gadin yazo ya tambayesa nan yace wacce ta wuce da mota yanzu baka mai gadi yace ai gidan nan masu tuka mota suna da yawa nan ya sake duba sunan yace Munayshat ok lfy dai ko yace lfy wa za a ce mata nan yace ace Ammar mai kayan fruits nan security ya shiga nan yayi karo da Aunty Mamu a falo ga Kausar a gefenta nan yace Aunty wani ne yazo gun munayshart wai Ammar mai sayarda fruit nan hajiya maryam ta fadada murmushinta ayya ammar lfy daiko yace eh wai abu yakawo ta nan aunty mamu tace kaje ka shigo dashi, kausar mikewa tayi ta nufi kitchen don dauko mult mai sanyi tasha,
Bayan ya koma ya shigo da ammar gasky gdn ya tsaru a kwai naira a gdn sosai don ya hadu iya haduwa da sallama suka shiga cikin falon da yasha blues da yellow da bakin labule ga kujeru luntsuma luntsuma suma colours din blue yasha gyara ga kamshin da yake tashi ya duka ya gaida ta nan yace shaidata mata yarta tazo sayan kaya gashi ta yar da poss dinta nan tayi godiya ta karba hauwa mai aiki ta kira tace ta kawo masa abinci yace ya gode hajiya ta bata rai ammar ae mun zama daya ka dauken tamkar uwa a gunka cikin jin dadi yayi godia hauwa ta kawo masa zobo daman shi ma aboci zobo ne ya sha kayan hadi nan ya dauka ya sha gashi da sanyi nan ya wani lumshe ido alamar jin dadi,
Kausar ta fito rike da malt a hannunta tun da ta nufo falo ta hangi wani hadadden saurayi ajin karshe ga kyau sai da ta furta woow a zuciyarta nan take taji ya tafi da ita amma jin kai ta danne ta shigo da sallamarta dake ita tana da hankali sosai ta gado halin Aunty Mamu ne gefen mum dinta ta zauna cikin isa tace masa sannu da zuwa yauwa yace a takaice dai2 nan munayshart ta shigo cikin wasu matsatsun kaya riga da wando na English wears tayi kyau sosai don suna da kyau ba laifi sai dai matsalar rashin gashi don sai da ta hada dana doki tun da taga ammar tashiga wani yauki tana karairaya wanda shi bai san tanayi ba ma nan Mamu ta bata poss dinta nan tace la ban lura ba ko da ta bude taga kudinta ba a tabasu ba 80k ne a ciki don harda zonen gwal dinta da yakai 60k aciki kirar dubai sai daukar ido ya keyi nan tace lah mum gsky na da AMANA kiga ga kudi kusan 80k ga zobe na nagode duk da nasan koda bata sukayi banda wasu matsala amma gsky da kanuna naji dadi nan ya mike da nufin tafiya cikin sanyin murya yace hajiya zan tafi tace angode kausar kam kasa motsi tayi sabida zakin muryansa amma dake ita tana da kamun kai ga jan aji shiyasa take buyewa har ya kai kofa Aunty Mamu tace Ammar in bazaka damu ba ina son zan tambayeka cikin ladabi yasoma takowa ya dawo in da ya zauna ya sake zama kansa a kasa ammar dan Allah ina son kafadan gsky waye kai daga ina kake don daga alamar baka dade da fara sayar da fruit ba don na dade ina zuwa gun bana ganinka san nan yanayinka baiyi kama da wahala ba a kwai wani boyayen sirri atare da kai cikin nutsuwa ya daga fuskansa nan suka hada ido da munaysharr da ke wurga masa shu’umin kallo Kausat ma kallonsa ta keyi ajiyar zuciya yayi kafin ya sake sukiyar da kansa cikin nutsuwa ya fara magana.
Happy Jumma’at Mubarak 2 All My Muslim Sisters n Brothers
Saturday, 1 April 2017
Home »
» AMANA TA CE 23
AMANA TA CE 23
Popular Posts
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(AUGUST 2016)* ...
-
MOTAR KWADAYI RASH KARDAM Duk launin kalan idonta, sun canza izuwa ja. Hannu tasa a tsakanin cinyanta tana mammatsewa,Bad Boy yana ga...
-
AMANA TA CE By ©Rash Kardam 1 Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassa...
-
🐾🐾Raheenat🐾🐾 1 Yarinya ce yar kimanin shekara 12 ta yanko a guje ta fada jikin Dad...
-
MOTAR KWADAYI By Rash Kardam 21-25 Jan motar yayi, suka bar cikin Silver Sand Hotel, bai zarce da su ko ina ba, sai gid...
-
BAZATA By ©Rash Kardam 1 Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan l...
-
[6/5/6:30pm] 🌲RASH KARDAM🌲🌲 & 🎋SADEEY S ADAM🎋 ...
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(JULY 2016)* ...
0 comments:
Post a Comment