: AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
11
Suna hira da Malam har suka dawo gida,….
da daddare basu wani hiraba sanadin hadarin da ya hadu, daki suka shiga suka kwanta ba a dade ba ruwa ya sauko sosai, haka aka kwana ana ruwa, da asuba malam sukaje sukayi sallah, inna da zainab sukayi acikin gd, haka suka yi koko da kosai shuka karya, bayan sun karya sukayi wanka,..
Bayan sun kan mala komai lokacin gari ya dan sha, kafin suka fito gidin biyar kofar gdn kasancewar garin ba mutane da yawa, don gida daya na da rata tsakaninsa da wani gd,..
bayan sun zauna malam ya bukaci ammar da ya cigaba da lbr sa…
Ammar ya cigaba da cewa bayan na mai dugri mun dau hanyar kaduna, sai dare muka iso kaduna don driver ma na gudu sosai, ko da muka isa garin kaduna, mun sauka a kawo, nan kowa ya fita don ya tafi girin da yazo, ina ina tsaye ni da wani a gefena sai ga mai taxi yazo, yana fadin Abuja Road Magajin, nan mutumin yace nan zaije, take nima na shiga taxi din munyi tafiya mai nisa ina kale2 don yanayin garin yayi kyau sosai, ahaka dai muka iso magajin gari nan mutum ya sauka nima na sauka, ko da na fito na rasa inda zani, hakan yasa nazo masallaci nayi sallah kafin na bar masallaci don na fara jin bacci, kofar wani shago na samu na kwanta don na gaji sosai, kwanana 3 a gurin ganin kar mutanen gurin su zargeni yasa na dau ledata na fara tafiya, nayi nisa sosai kafin naga wani guri mai gine2 na sama ga jama a sosai, daga nesa naga an rubuta “CHE CHENIA MARKET” da manyan harufa, nan nasamu na kutsa, kusa da shagon mai takalma na zauna.
na kwana biyu ina zama a gun har na dawo dan aika a gun, abinda na lura a kwai wani shagon takalma da less da material, saman shagon an rubuta “ZAINAB FASHION DESIGN” a bunda na lura akwai wani alhajin da ke yawan zuwa da yarsa wata kyakyawa na karshe, suna sayan kaya ne ko mai sukeyi ban sani ba, tun da na kalli yarinya naji ta kwanta min a rai ina sonta da kanwa, hakan yasa duk randa zasu zo in sun sai kaya zanje in dauka musu in gaida alhajin ko da babanta zai bani kudi bana karba, sai yayi da gske nake karba, hakan ya mana masa dadi, har yasoma tambayata inane unguwan mu, nan nasoma hawaye ganin haka Alhaji ya kama hannuna muka nufi motarsa, munyi tafiya mai nisan gske, har na fara tsoro ko dan yankan kaine, nan nakama adu’ah neman tsari, mun isa wani unguwan da ba mutane sosai, sai da mukazo kofar wani katon gd mai kyau horn yayi aka bude kofar, gate din, gd ba laifi kam yayi kyau sosai.
Munshiga cikin gd mata kyakyawan mace ta fito da murnanta, tana sannu da zuwa Alhaji, nan ta kalleni, tace Abban Auta ina kasamo wan nan yaro mai kyau haka, Alhaji yace bari mu zauna tukun.
®WHW®
Rash Kardam
ABUBUWA BAKWAI (7) ABIN KULA GA DAN'ADAM
1. Duniyar da za a barta, me ya kawo hadama? 2. Dukiyar da za a lissafa daya bayan daya, me ya kawo tarata? 3. Rayuwar da zata kare, ina wani farin ciki? 4. Yarintar da tsufa zai zo mzta, me ya kawo takama? 5. Ana sauraren mutuwa, ina wata walwala? 6. Jikin da zai zama gawa, me ya jawo dagawa? 7. Karshe dai makomarsa kabari, me zai sa alfahari? Wanda ya manta da wadannan a ina ya bar hankalinsa? Allah yasa mu dace, yayi mana kyakkaywan karshe. Ameen!
KADA KA RAMA CUTA GA WANDA YA CUCEKA!
Kar kayi wani abu mummuna don ka cutama wani, amma idan wani ya munana maka, kai kayi hakuri. Zaka samu abu biyu sakamakon hakan; * Na farko zaka samu ladan hakuri a wurin Allah. * Sannan zaka samu kwarjini a wurin wanda ya cuta ta maka.
KADA KA BARI ZUCIYARKA TA ZALUNCEKA!
Kada ka sale zuciyarka ta zalunceka, tabbas zaluncin zuciya ga gangar jiki yake komawa, idan akayi wasa ya zamanto ya shafi rayuwa. Assasa bak'in tunani, yawan zargi da rashin tabbas akan wani aiki, zato, shakku ko kokwanto akan wani al'amari batare da tantance gaskiyarsa ba, shine zaluncinzuciya akan dan Adam. Maza ka hana zuciyarka don akwai hadurra dubu akan hakan.
MAHAKURCI MAWADACI
Tabbas ba kowane dandanon magani ne ke da dadi ba, amma babu shakka shine abu mafi dacewa ga dukkan mara lafiya. A lokuta da dama rayuwa takan dakeka da guduma ta jefaka acikin wani mawuyacin hali, kayi ta fama amma tayi maka tutsu. Amma idan kayi hakuri sannu ahankali zata kwaranye. Hakika ba duk abinda rai yake so yakan samu ba, amma bukata bata taba sauyawa ba kuma bata taba karewa ba. Don haka ka shirya bukatunka da kyau ka bisu daya bayan daya sannu a hankali, kayi gwa- gwarmaya, sannan kayi juriya. Tabbas mafarkinka zai zama gaskiya.
KO KA SAN?
Rayuwa bakin alqalami ce tana bukatar kaifi sannan tana son tsini. Kaifin don ka yanki magauta, tsinin kuwa don ka soki makiya. Haka zalika rayuwa kamar randar ruwan sanyi ce ta kasa tana bukatar tanaji da adani, kodn wata rana ka shayar da masoyanka. Da kyau ka lura da abu biyu a rayuwa; 1. Ka lura da mai zaginka mai aibantaka wata kila wata rana zai iya zama masoyinka mai yabonka 2. Ka lura da masoyinka na kusa mai yawan ambaton alkhairinka, wata kila wata rana zai iya zama makiyinka mai zaginka.
Friday, 17 March 2017
AMANA TA CE 11
AMANA TA CE 10
: AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
10
Bayan anyi zana idarta matan da babana ke gidan ta karbe ni haka ta raineni har na girma na kai 15 yrs lokacin ina secondary school, haka zamu fita aiki mudan samo abunda zamuci sam baba na yaki aure, ana cikin haka malam suka shirya komawa garinsu, don suma mazuwa ne, yan jalingo ne, tunda suka shirya tafiya, mahaifi na yace na shirya muje muga yan uwansa,
tunda ga ranan ya nimi kudin motan tafiya muka shirya ranan asabar 12 /3/ 2012 muka tafi mai duguri tun a hanya mahaifina ya ke cemin gabansa na faduwa, ko da muka isa mai duguri, muka shiga motar gwaza, muna isa yaga masarauta ya canza nan ya samu lbr rasuwan iyayensa, mahaifiyar sa ma bata dade da rasuwa ba, gidansu ya watse nan mukayi kuka tare, daga nan yace mu wuce cikin mai duguri, washegari muna zuwa, cikin garin mun sauka a tasha, kenan nace ma baba na ina jin fitsari, nan yace inje bayan gidan tashar na tafi kenan,
kafin in dawo naji karan wani abu dammm, gurin ya dau hayaki asai bomb ne ya tashi tare da mahaifina,
Innalilahi wa inna ilaihi raji’un, abunda na furta kenan nan aka tattara wayanda suka tarwa tse ki gawan mahaifina ban samu gani ba tun daga nan na shig gararin rayuwa, kwana na 2 a mai duguri a tasha na dan samu taimakon kudi na hada da nawa, nan ji a tasha ana mitar Kaduna haka kurum naji garin ya min,
nan nashiga motar,
Kiran sallah da akayi ne ya sasu mikewa malam jikinsa yayi sanyi alamar tausayi, inna kam harda hawaye Auta kam kuka takeyi shabe2 don sai yau tasan tarihin Ammar,
Bayan sun dawo daga sallah malam yace su huta sai gobe yaji lbr Auta da zuwan ammar kaduna, nan inna ta daura musu abinci,..
ta girka musu, dan waken dawa da wake ba karamin, dadi yayi ba, don sunyi santi inna ta iya daka yaji, don harda yar bushahen namanta, takesawa acikin yaji sai yayi zakwakwai, gwanin santi,
Da la’asar haka sukayi sallah sukazo zauna malam yace zashi dibo ruwa nan Ammar yace zan bishi, suka dau jarkuna zuwa rafi, suna yar hiran duniya akan abunda ke tafiya gar suka dawo saida sukayi sawu 3 nan inna ta dafa musu ruwan zafi sukayi wanka,…
Malam suka fita zuwa wajen gd,
suna fita suka hango yan matan kauyen sun taru a dandali, tun daga nesa suka fara gulman Ammar yau malam ya samo santalelen saurayi, wan nan tafara naa ne wancan na nawane, najaat tace kai kustsaya kuga duk cikin ku kunga da wanda ya dace sai ni, dake duk suna tsoronta ba wanda ya tanka, nan malam fa Ammar sukazo suka wuces7 zuwa shagon kauyen, garin suka sayi taliya, malam kenan akwai kokari.
®WWA®
Rash Kardam
AMANA TA CE 9
AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
9
Bacci tayi sosai akan yar katifan inna, sai magriba ta farka tayi sallah, bayan ta idar inna ta kawo musu tuwon dawa mai laushi miyar danyan kubiya yaji man shanu, sai kamshi takeyi,nan suka ci suka koshi, sai da sukayi isha’i kafin Auta ta dingisa kafarta tashiga daki ta kwanta, bata dade ba bacci ya dauketa, Ammar ma dakin suka shiga shida malam suka kwana,
Auta bata farka ba dai asuba da inna ta daga ta tayi sallah bayan sunyi sallah,
ta gaida inna ta din gisa zuwa dakinsu malam ta gaidasu ta dawo ta zauna, don ba halin taya inna girki,… Bata da lfy,
inna ta musu dumame da kunun tsamiya, nan sukaci duk da damuwan da suke sai da sukayi santi don inna gwanar iya girki ce,…
sai bayan da suka karya kafin malam ya umurci Ammar da ya basu tarihinsa dana Auta, ammar ya gyara zama nan take idonsa ya kawo hawaye, da bai zubo ba ya fara dacewa,
Sunana Ammar Saad Saraki, ni haifafen dan maiduguri ne iyayena yan mai duguri ne, kenan su Barebari ne gaba da baya, baba na ya kasance dan gidan sarkin Gwaza ne, su biyar mahaifinsu ya haife su, Uku mata biyu masa matan akwai Ya fanna, da da hajja gana da Yakura, sai wan babana sunasa hashim sai babana mai suna Sa’ad, mahaifina ya taso cikin kulawa da kaunar mahaifinsa kasan cewar yana da nutsuwa sabani yaya shi da suke uba daya wato hashim,
hakan yasa suka tsani baba na da mahaifiyarsa don shikadai ta haifa sauran hudun duk yayan kishiyarta ce Hajiya faima,…
duk tsanar da suka masa bai damesa ba ya nimi ilimin boko da na addini bayan ya kammala karatun degree dinsa ya dawo gd,
sai mahaifin sa ya masa Auren gata da mahaifiya ta, Hakimin liman kara, hajja faty mahaifiya kenan ta kasance mace ce mai kamala da kyautatawa ga hakuri da juriya ga sanin darajan dan adam, lokacin auren kudin da sarki Abdallah Saraki ya kashe ba karamin tada hankalin hajiya fatima yayi ba, nan tace ita mai yasa baza ayi auren danta ba, sarki yace a yanda bai nitsu ba shine shaye2 yar wa za a hada shi da ita,
tun daga wan nan lokacin suka dau tsan gwama suka daura ma kakata da da mahaifiya ta, duk da hakan bai damesu ba,
kwanaki sun ja yau wata 5 da auren mahaifina da umma na nan ta fara laulayin ciki, gashi yazo mata da laulayi, bata son shan ruwan fanfo sai na rija tunda suka lura da hakan, sukayi makircinsu aka bata ruwan gdn gaba daya don karta samu na sha, haka kullum sai anje nimota ta a gari don in bata sha ba tashin hankali ne, haka rayuwa tayita tafiya.
Sarki Abdallah Saraki, ya yanke shawaran sauka a mulki sai daura dana Sa’ad Saraki akan mulkin gwaza, tun daga randa sarki ya yanke hukunci, hankali hajiya fatima ya tashi, nan suka soma shiga bokaye, sai da suka san makircin da sukayi mahaifina ya dau mahaifiya suka bar garin bashi tun daga lokacin ba asan inda mahaifina yake ba, bayan tafiyan mahaifina bakin cikin yasa yagamu da ciwon hawan jini, harya makance da ganan kuma Allah ya karbi abunsa,……
Mahaifina na barin gari bai zarce ko ina ba sai kanon dabo tunbin giwa ko da mai kazo anfika,….lol…. Amma basufi yan Bauchi ba fa,
nan ya samu wani mutumin kirki ya rikesa a unguwar Dakata, haka yayi ta rayuwansa da umma na harta cikinta ya kai na haihuwa, nan laraba ta tashi da matsanacin ciwon mara nan sukayi asibiti, ana kaita ta haifi danta, tubarkala ko kalon dan batayi ba Allah ya karbi abunsa, asai masalan da aka samu lokacin tana mai duguri, maganin da aka a rijiya ta sha don karta haihu dake Allah yayi zanzo duniya sai da ta haifen lokacin ya mata illa sosai, shine sanadin mutuwarta.
®WHW®
Rash Kardam
AMANA TA CE 8
: AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
8
Bayan Auta tasha maganin, sai aka dawo kan Ammar nan shima ya kunce daurin da yayi ma ciwonsa, tsohon nan da naji inna laure nakira da malam, ya dauko wasu magun guna, ya wanke masa ciwon da wani farin ruwa, nan ya haungo karamin glass ya shiga hannun, sai da ya dauko aska ya ciro glass din, duk da Ammar na miji ne sai da na ga indonsa yayi jajazur da alamar yana jin zafi sosai, baran ciwon ya kwana shiyasa, Auta kam kasa jure gani tayi sai kifa kanta tayi tana kuka maras sauti…,
wai yau itace a kungurmin kauyen da ko wuta babu bare ruwan fanfo, kafin asauko gun kwanciya mai kyau, nan take kalaman Dad dinta ya fado mata, inda yake mata nasihan sa na karshe akan ta yi hakuri a duk inda tasamu kanta, sabida yanayin rayuwa.
Allah sarki duniya kenan wai ace su baba sani su zasu kashe iyayenta akan dukiya da son duniya, mai suka maida zumunci ne ga cin “Amana” wan nan wani irin rayuwa ne sam tausayi ya kaurace a idon jama’a basa tunawa zasu mutu su koma ga Allah, in har kayi mai kyau zaka taras, kwanciyan kabari ma akabar mutum dashi babban aiki ne bare ace ka aikata mumunan abu har akaika wutar yasalam!!… Innalilahi wa inna ilaihi raji’un duniya tazo karshe wayan nan abun duk alamun karshen duniya ne Allah ya kyauta yasa mudace da karshe mai kyau ameen.
Hawaye ke gan garimata daga idonta, tayi nisa cikin tunani, sai ji tayi ana share mata hawaye, tana daga ido taga Ammar ne, shima hawayen yakeyi sai alokacin tasamu tasaki kuka mai ban tausayi, shima kukan yasaki, an rasa mai rarrashin wani.
Malam da inna laure sun zuba musu ido sai kallonsu sukeyi, tabbas ko basu fada musuba suna cikin tsananin tashin hankali, nan take ina kaure ta fara hawayen tausayi, malam idonsa yayi ja sosai, malam kenan akwai tausayi ga taimako.
malam yace bawan Allah kai na mijine ka kasance mai juriya a kowani hali duk da bansan mai yasame ku ba aman da alama kuna cikin tashin hankali, kuyi hakuri, kusani duk tsanani yana tare da sauki, kuyi hakuri ku bar ma Allah komai, zai yi muku saukin Al’amarin, haka rayuwa take kowa da irin jaraban da ubangiji ke masa kuyi fatan Allah ya baku ikon ci, Ammar ya amsa da ameen.
Inna ta mike ta debu ruwan wanka a yar bahonta da tsage aka nane shi ta surka kafin ta kaima auta bayi, sai da ta taimaka mata kafin ta kaita bayi tafito ta barta nan ta dauraye jikinta, don ruwan da dumi sosai ya gasa mata jiki kuma ta samu dan karfi, bayan ya fito inna tasake sama Ammar ruwan ta kaimishi shima wankan yayi, bayan yafitoa wanka suka shafa mai dake lokacin da mina ne, a kwai dan sanyi kadan.
Malam ne ya hau kekensa yaje can kauyen da gabansu anan ake samu shago, yasayo musu suga, yadawo inna laure ta musu surki mai dumi sosai, don ya ware musu hanji, abinci ta dauko musu dambu tayi daman, kuma ta danyi da yawa, san nan Malam ya karamusu da nashi, aiko sunci danbun sosai don yunwa sukeji, sai da suka gama cin abincin, san nan sukayi godiya ga Allah da ya kubutar dasu, san nan Ammar ya juyo ya gode ma Malam, cikin kulawa malam yace karkada mu ni domin Allah na muku, ita rayuwa bakan wa zai tai make ka nan gaba, kuma dukiya da dan mitum, da dabba ba a musu keta, ku kara gode ma Allah ammar sai da yaji kwalla, asai ana samun irin wayan nan mutane a zamanin yanzu, Hamdalah yasakeyi ga Allah da ya ciyar dasu.
Inna laure ta gyara daya dakin nan dama da kyausa, in sunyi baki anan suke kwana, ta kwantar da yar katifar bonun da ke dakun tayi shinfidi akan gado, inna laure kenan duk da acikin kauye suke tsohuwar akwai tsabta, komai nata tsab2 gwanin burgewa, ga kamala da kyautawa.
Malam yace ga daki an gyara zamu kwana da kai inna laure kuma sai su kwana da kan warka, kafin in Allah ya kaimu waye wan gari, sai kubamu tarihin ku da abunda ya
AMANA TA CE 7
: AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
7
Nan yasaki kuka mai ban tausayi, jijigata ringayi sai yaga tasaki ba ko alamar motsi atare da ita, da sauri ya dauketa yayi gun rafin da ita yana isowa yaga wani dan tsoho yazo diban ruwa a gora, tsohon nan, ganin halin da Ammar ke ciki yasa yace subhanallah bawan Allah mai yasa meta Ammar kasa magana yayi sai hawaye:'(:'(wani na bin wani, tsohon na ganin halin da Ammar ke ciki ya dibi ruwan goransa tare da bisimillah ya watsamata sau 2 nan take ta saki ajiyar zuciya mai karfi, muryan ta ya dishe, ga jikint ba kwari duk ya mutu, ahankali take magana sai da Ammar ya sunkuyo dai2 bakinta kafin yaji mai takecewa wayyo kafarta, ammar da sauri ya riki kafar sai a lokacin tsohon ya lura da kafan yace yasalam mugani ya rike kafar wan nan ae cizo kunama ne ya daneta, yace yanzu ku biyo ni in taimaka mata, ammar ya dauketa suka bi tsohon.
A cikin garin kaduna kuwa, su baba sani sun shiga sabon rayuwa mai dadi da dukiyar da suka dade suna mafarkin samunsa, Sadiya sam nataji dadin yanda Abbanta ke zakewa akan dukiyar dan uwansa ba, tunda ba a ga Autaba kuma hakan bai tabbatar da cewa ta mutuba, abin duniya duk ya isheta, haka rayuwa ta kasance musu cikin nishadi har sun manta da wasu wai su Al-hassan da fatima da wata diyarsu Zainab bare Ammar dan kallo.
Ammar ko haka yabi tsoho nan sunyi tafiya mai nisa sosao kafin suka shigo wani karamin kauye wanda gidajen ciki baifi a kirga ba, in kazo gida daya sai kayi tafiya mai nisa kafin ka iske diga daya, ko da suka isa kofar wani diga an masa rufi da da ciyawa sai katangan kara aka dan zagaya gidan naki biyu ne a gidan sai dakunan kaji da baru yan kanana da agwagi , suna sallama wata yar tsohuwa ta fito daga dakin danake zaton nan ne gurin kwanan su, tace lale maraba baki mukayi, ganin Ammar rike da joda ga jini ajinsu duka yasa tace lfy kuwa, suwaye wayan nan, tsohon nan yace bakine da sauri ta dauko taburman sakar kaba ta shinfuda musu, ammar ya kwantar da Auta tsoho nan daki ya shiga ya dauko wani yar jakar fata, ya dauko magani da nan ya kama kafar ya matse gun cizon saiga karin ya fito nan ya sake matsewa har sai da Auta tayi kara ta kan kame Ammar sai zufa tayi, saida yacire yashafa mata magani, san nan yasa inna laure ta dafa
Musu ruwan zafi ta kawo masa kadan a kofi ya saka magani yabama Auta da kyar ta iya shan maganin tana runtse ido.
®WWA®
Rash Kardam
AMANA TA CE 6
: AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
6
Motar suka shiga nan mutum min yace subada 1500 kudin mota sai a lokacin ya tuna basu da kokisi, innalinahi wa inna ilaihi raji’un abunda ya furta gashi sunyi nisa sosai, sun shiga jeji don sun bar cikin garin kaduna sosai, jiki ba kwari yace wa driver dan Allah ka tai make mu wlh fitowar gaggawa ne ya kama mu bakosisi ajikin mu, driver ya narko ashar yayi, aefa baka isaba zan dauko ku a bati ne ba ko sisi mai na tsada kuma niman kudi na fito, waya sani ko dan iska ne ma kai kasato musu yarinya inazaka da wannan yar gashi jikinta duk jini, kalala ta mata rayuwa, ko sayarta zakayi, nan take ran Ammar ya baci don tunda yake ba abundaya tsana kaman zargi ko kazafi, shi da ya tsani zina a rayuwansa mezaisa ya aikata cikin bacin rai yace kaii Malam ya isheka in har bazaka taimaka min ba karka min wan nan zaton, nan mutumin yace anyimaka kuma zata fita anan ba wlh sai kabani kudina, nan ran Ammar yakara baci wai shi dayake nima da guminsa ga kuma Zainab yar gata gabada baya wai yau sune a wulakance ga shi an kashe su Alhaji shikenan Zee sa ta dawo “MARAINIYA”nan take yaji hawaye:'(:'(:'( wasu na bin wasu, sai a lokacin ya kalli agogon hannusa mai kyau yace ma
driver bani da kudi amma ga agogona in zaka karba yafi karfin kudinka, driver yace nagani ko da ya karba yagani yasan zaiyi tsada dayawa nan yace to shikenan yanzu in kaiku saminaka ne ko zaku sauka anan tsabage bacin rai yace barin musauka anan, ya dauki Auta suka fita, gefen hanya ya kwantar da ita lokacin gari ya waye sosai, sai alokacin yaga kafarta ya kumbura sosai fa bakinta ma ya kumbura sosai, gashi yayi ja abunka da farar mace, gindin wata katuwar bishiya yaje ya shinfida fallen zani ya kwantar ta, ga yunwa yasoma damunsa ga hannusa yana masa zafi sosai, bayan ya kantarta, yasoma dube2 ko zaiga ruwa don yasha yakuma ji alwala.
Acikin garin kaduna kuma Alhaji Abubakar ko ince Inspector Abukar shiyatsa akan gawan su dad har akayi zana idarsu aka kaisu makwancinsu na gsky, kafin kace me lbr ya baza gari, yan uwan dad sun taru a gidan ko da Sadiya yar Baba sani taji lbr ba karamin girgita yayi ba baran da taji ance ba a ga Zee ba tashiga tashin hankali don suna shishiri sosai,
Inspector Abubakar daya koma gd ya tausaya ma yarsa bulkisu don kawar Autace sosai tayi kuka kuma nan ta dauki aniyar saita dau fansa akan duk wanda ya aikata abun, bayan kwana uku da rasuwan su Dad yan uwansa sukace su duk wanda yayi abun nam sun barshi da Allah, sirutu kala2 su ka rinkayi har saida Inspector Abubakar yaso ya ganesu, bilkisu kuwa ranan kwana na uku, tasami Abbanta akan ita ta canza ra’ayi daga kan Science courses, yanzu Law zata karanta don tazama barrister don ta nimo ma Kawarta Ameeniyar ta, hakkunta da cutar da ita da akayi, kuma tace Abba ni ajikina inajin Zee bata mutu ba ko ga yanayin statement din da aka samu kuma kaga ba aga Ammar ba nisan yana tare da ita kuma bazai cutarta ba da yardan Allah don yana da hali mai kyau, Inspector Abubakar yaji dadin maganar yarsa Bilisu wanda ake kita da futuhatul-khai, yamata Adu’an Alkairi da fatan nasara.
Su baba sani nan suka fara kiciniyan raba dukiyar dad har yaso su samu sabani da baba isiya akan wanda zai zauna a gidan dad da kyar Baba isiya ya hakura akan shi za a bashi motar dad babban ya rike.
Rayuwa kenan wai naka najikinka shiyake son ganin bayanka basa tunanin suma zasu mutu ba tsoron Allah wan nan wani irin zamani ne burin wasu mutanen su ci “Amana” yan uwa muji tsoron Allah musani Amana tana gefen siradi da Zumunci duk wanda ya karya daya aciki to yasan makomarsa, don ranan kiyama akwai wasu kugiyoyi a kasan gadan siradi duk wanda yaci amana ko ya bata zumunci ko da ya kusa karshen haye gadanne haka kugiyar zata finciko shi wasu kafin su isa duk sun yaga naman jik
AMANA TA CE 5
: AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
5
Ko da sukaje gidan kawu isiya wanda tutun nufawa, ba kowa aciki kuma ba nisa sosai da gidan Alhaji marigayi, nan suka shiga ko da suka zauna nan baba sani yace yau burin mu yacika na gama wa da Al-hasan da iyalansa, kamar yanda mukayi Alkawari zamu ba ku 400k kowa zai dau 200k kenan gumus ne yace oga mungo amma munaso aba mota koda kwaya daya ne ehhh musamu na yawo a gari, ko wani aiki kuke so zamu muku cikin sauki kawu isiya yace aaa bazai yuba abun yaso ya dawo musu rikici baba sani yace ba matsala za a duba in komai ya lafa abaku, nan ya ciro 300k ya basu yace kurike wan nan kafin komai in ya lafa zamu sallame ku, gaba daya nan sukayi sallama kowa ya kama gabansa.
Da safe yan unguwa suka fito don wasu sunji karar tsayuwar don haka suka yi cirko2 gashi jiya anyi ruwa sosa, mukwabcin dad wani mai suna Alhaji Abubakar yace yan uwa yau ban ga Al-hassan a masallaci ba kuma duk rintsi in ba jinya yayi tsanani yana zuwa sallah amma yau shiru, ko lfy wani mai suna Alhj kabir yace ni jiya fa kamar an shigo unguwan nan don duk da karan ruwan sama dake zuba naji ihu san nan naji harbin bindiga sun dade suna jimami kafin wani acikinsu yace kamata yayi mu shiga gidan mugani, nan suka dun guma suka shiga tun a kofa sukaga masu gadi an daure su, da sauri suka isa wajansu, bakinsu an toshe da tsumma, kunce su sukayi nan Alhaji Abubakar ya fara tambayan lfy, sun wahala yasa ba wani amsa don dauri da aka musu mai kyau ne hakan shi ya gala baitar dasu, da sauri suka nufi cikin gidan bayan sunshiga a falo suka tarar da gawan Alhaji da hajiya nan suka soma jimami masu kuka suka fara, alhaji abubakar makocin dad police ne nan take ya kira ja mi’an tsaro suka fara binjike nan sukaje dakin Auta inda suka ga yanda aka baza kaya da alamar kare kansu da sukayi da kuma fasa window da akayi gashi ba auta ko da suka zaga nan sukaga jini da kuma alaman harbin da akayi ta waje, Alhj Abubakar yace cikin daya biyu ko sun kashe Zainab ko sun dauketa ko da suka dawo gd sai alokacin ya tuna da ammar nan ya nufi dakin da ke tsammanin nasa ne sallaya tagani a shin fide da alamar anyi sallah akai ki da suka fito suka nufi kofar baya nan sukaga an tura kofar anshiga duk binciken da sukayi ba wani amsa nan suka kira Alhaji sani da baba isiya suka sai da musu, ko da suka iso gidan kuka sukeyi sosai kai ka rantse basu da hannu aciki har sani na ikirarin imyasan wanda yayi kisan nan sai ya dau fansa, kawu isiya kam ko mace iyakaci yanda yake kuka. haka police suka tafi da gawarwakin don kara bincike.
Ammar da auta kuwa tafiya yayi sosai, sun shigo cikin gari kuma dare yayi sosai don asuba ya kusa, nan yasamu inda ba ayi ruwa ba ya kwantar da Auta ya yagi zanin dake daure a saman kayan baccinta ya kulle hannusa sai runtse ido yakeyi alamar zafi, ya daure hannuta ya dauketa suka cigaba da tafiya sunyi nisa sosai, sai ga wani mai mota yazo wucewa nan ya tsare shi sam yaki tsaya haka ya cigaba da tafiya sai ga wani da alamar wan nan irin yan taxi masu zuwa gari zuwa gari har yaki tsayawa komai ya tuna ya dawo daukarsu, nan Ammar nace ina zan kaiku Ammar yace ban sani ba mutumin yace to ni saminaka zanje yanzu, yace muje ka ajiye mu a hanya.
®WHW®
Rash Kardam
AMANA TA CE 4
: AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
4
Ammar ya ma rasa ya zaiyi ga Auta numfashin ta na kokarin daukewa da sauri ya suguna akasa ya ajiyeta acikin tabo ga jini yana ta zuba daga hannunsa,
Gumus suka nufo su da sauri nan ya harba bindigan ya sake harba wa yaji bullet ya kare cikin jin haushi yace oh ya wurgar da bindigan akasa ya nufosu ko da yazo daman Ammar na ankare yana isowa suka fara kokuwa cikin ukon Allah karfin yazo ma Ammar ya wurga shi a wan nan ruwan, aiko dan uwan gumus na ganin haka dake yana haskasu da touch light, ga shi gumus nata fanjam aruwa dake shi bai iya ruwa ba, kuma ruwan da dan yawa, da sauri yayi gun ruwan ko ta kan su Ammar baibiba ya je gun dan uwansa don ceto rayuwansa,
Ammar na ganin haka ya dauki Auta yasa gudu sai da yayi nisa ga ruwa ya soma tsagaitawa, ya samu wani rumfa ya ajiyeta ya huta, basu dade sosaiba ya auta sai hawaye:'(:'(take tayi ko da ya laluba kafarta yaji ta kubura suntum, taba kafar dayayi har sai da tayi ihu haka ya dauketa suka cigaba da tafiya.
Su gumus ansha wuya da kyar aka ciro shi don har yasoma shan ruwa, yana dawo wa hayyacinsa yake tambayar mugum ina suke yace sungudu, mtssss bahaka nasoba nan yace naga abunda ya faru kar ka sheke zuwa lahira da wuri shiyasa na ciroka kai kajimin wayan nan sai kace mutuwar nima izini takeyi, mikewa sukayi gumus ya karbi wayar mugum don nasa ruwa ya bata, baba sani ya kira ya tambayesu suna ina yace yanzu zasu bar gidan Alhaji kenan sukace gasu zuwa.
ko da suka isa nan suka samu baba isiya da sani sun daure sale mai gadi da musa, don daman sunyi akan zasu daure su sabida ace barayi ne suka zo, hakan sukayi, ko da su gumus suka iso nan sukaga abunda ke faruwa dariya sukayi sosai sukace Alhaji baku da dama,
Baba sani yace ya ina fatan kun sheke su cikin sauri gumus yace ai har gawan ma sai da muka yardasu inda ba mai gani, nan kawu isiya yace aikin ku na kyau, gumus yayi murmushi yace oga sai kudin fa baba sani yace ina zuwa cikin gidan suka shiga dakin dad suka duba drawer nan suka ci karo da damin kudi sai dasukayi dariya sosai kafin suka diba nan suka fito falo, baba sani yazo cikin izgilaci yace su Al-hassan yau an sheka kiyama to ina naira kai dan taurin kai yau zamu facaka da dukiyar da kake ta kama dashi, yana zuwa kan hajiya sai da ya shureta da kafa, ke kuma yar iyeye yau munyi maganinki da yar da kuke so, harda dauko bare wanda bakusan daga ina yake ba ku fifita shi akan mu gashi yau duka bakwa nan mun kuma samu dukiyar cikin ruwan sanyi sai ya kece da dariya sosai, nan suka fita suka shiga mota suka tafi don suke su sallami su gumus.
®WHW®
Rash Kardam
AMANA TA CE 3
: AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
3
Ya balle window din ya fara fitar da Auta kafin ta zo fita wani kwalban glass a jikin window din ya yanke shi ya shiga sosai, ya ji zafi harsai da yace washhhh, dai2 lokacin su baba sani suka balle kofa suka nufo shi cikin zafin nama ya dirka ga jini sai zuba ya keyi sosai, da sauri Ammar ya yakwanta a kasa ta gefen window, cikin hantsari ya fisgo Auta ta fadi kasa wanda faduwar wata ya dai2 da wani dutsi nan ta buge bakinta sai ga jini, kara tasa yayi sairin toshe mata baki, su gumus da kawu isiya suna isowa harbi suka fara amma bai kai ta inda su Auta suke ba, baba sani ne ya ciza yatsa don ya ji haushi ga window ya musu kankanta baza su iya fita ba da sauri yace ku zo mu zaga mu bisu da sauri suka fita ga ruwa haryanzu zuba yakeyi sosai.
Ammar na ganin sun bar window yayi kokarin rashi ga jiri na debansa don jininsa ya zuba sosai, ga Auta kuma jiki ba kwari, ya mike yana tan gadi ya dagata kasa tsayuwa tayijijjigata yayi da kyar sai ta sauke ajiyar hrt kafin ya mikar da ita suna mikewa suka hango motar su baba sani sun nufosu, nan ya fara janta da gudu tunda daga hayin rigasa layin waya suke gudu sai da suka wuce kantin yawo, kafin suka kara gudu dai2 zasu fita a hayin rigasa, Auta ta fadi da sauri ya dauketa ganin in yace zai miki hanya zasu kamasa sai yayi gurin wani sabon gini wanda dogayen ciyawa sun bullo agun gabansa kuma katon ruwa ne wanda ya taru, nan ya kaisu gun ya tsuguna ya tare Auta da numfashinta ke shirin daukewa
abunka da rashin sabo ga razana don Auta in banda girki da take taya hajiya bata wani wahala, tasaba da rarrafen carpet tun tube da waya, baran da ta rage ita daya ma Dad da Hajiya ba irin gatan da basa mata.
Su baba sani da suka iso gurin nan suka fita ga ruwa na sauka sosai duk dube2 da sukayi basu gansu ba,
Ammar kuwa suna gurin a tsugune da ke Auta ce ta jikin garu, nan wata kuna ma ta fito sabida ruwan da ya dameta a gidanta tana fitowa kuwa kafar jidda ta hau sai da tazo kusa da gwiwanta ta danna mata cizo, har saubiyu duk da zafin da taji tayi saurin damke bakinta , Ammar na ganin haka ya kara matse bakin nan kuwa kunamar ta kara yanka mata cizo, sai murkususu take tayi, gumus da duna sukace alhaji ku tafi kawai mu zasu tsaya mu ne mesu in baku mu kawo maka gawarsu ba to zamu maka da lbr mutuwarsu, nan suka tafi da motar suka bar su gumus a gurin, sun dade suna dube2 sosai agun kafin suka soma fita,
Autakuwa wuya yayi wuya bata san lokacin da ta kwace bakinta ta saki kara da sauri su gumus suka juyo nan suka fara nufo gurin da sukaji karan,
Ammar na ganin haka ya mike yasoma jan Auta suna kara gaba kawai suka ga kato kogin ruwa ne a gabansu ga su gumus sun nufosu.
Abun gwanin tausayi nikaina Rash bansan lokacin da na fara zubar da hawaye ba .
Allah sarki su Auta da Ammar Allah ya kwace ku a hannu wayan nan Azzalumai din Ameen.
Sai dare zakuji ni
Taku a kullum mai kaunar ku
®WHW®
Rash Kardam
AMANA TA CE 2
: AMANA TA CE
By
©Rash Kardam
2
Tass kake ji karan harbin bindiga nan take Auta tasaki razananen kara, da sauri suka juyo girin da sukaji karan suna fadin suwaye, suka nufo gun, Ammar yana ganin haka yaja Auta tana turjewa ita sai taje gun su Dad da Hajiyarta, dakyar ya shigarda ita dakinta yasaka key ya kullesu, ga ruwa sai sauka yakeyi ana tsawa, nan yarasa yanda zaiyi Adu’ah ya tuno na ne man tsari daga abokan gaba ya fara karantawa, autakan sai kuka take, ana cikin haka su Kawu Sani suka iso kofar nan suka fara jijjiga kofar, Auta ko kara sautin kuka takeyi Ammar bai san lokacin daya daka mata tsawa tayi shiru don kukanta har cikin zuciyar shi yake tabasa, nan ta damke bakinta , duk ya rue yarasa ya zaiyi gashi ba hanya, kasu Baba Isiya da sani su jijjiga kofa ga harbin suketayi, kiris yarage su balla kofar nan take dabara ta fado masa da sauri yayi gun Waldrop, ya zazzagar da kayan ciki kasa da kyar ya turo ya jawo ya kawo zuwa bakin kofar ya tokare, nan ya janyo dress miro shima ya tokare nan ya dafe kansa sai ga wasu zafafan hawaye:'(:'( ke zuba yana kiran sunan Allah ya kawo musu mafita.
A bakin gate kuwa mai gadi da sale suka leko ganin su Alhaji an sheka kiyama suka sheke da dariya sukace yau ina kudin ka ya dawo namu, gumus ne ya fito yace kuba mu karfe ina tunanin akwai wasu agidan nan zamu balle ko fa, don yar Alhaji na tare da wani Sai a lokaci idi yace kai:oops::oops:munyi kuskure daya da muka bar dakin Ammar bamu fara ta kanshi ba barinje na dubo shi, ko da yaje dakin ba ammar nan yace duk yanda akayi Auta tana tare da Ammar amma bazasu gudu ba, don gidan nan na rufe ba gurin tsira dariyan mugunta suka farayi, wani katon karfe suka samo wanda duka daya zasuyi wa kofar su balle, nan suka nufo cikin dakin da karfen.
Ammar kuwa adu’o’i yakeyi can ya tuna windo dakin na glass da sauri ya mike nan ya fara dube2 ba wani karfe a dakin wanda zai fasa ga shi sukuma sun kusa balle kofa duk ya kalli ko ina na dakin ba wani abu, sai can ya kalli Bedside drawer, da sauri ya dauko ya zubar da kayan ciki, ya nufi windon da karfin ya buga tare da bissmila bugu biyu yayi mai kyau wundon ya balle sosai yanda zasu wuce sai da ya leka ta baya yaga ba kowa kafin ya dauko Auta ya sanyota ta waje tasauka kenan yana shirin fita wani kwanban da bai gama balle ba ya yankeshi nan sai ga jini sosai gashi kwalbar ya shiga sosai har sai da yace washhhhh, lokacin su baba Sani suka balle kofar suka nufoshi.
Sunday, 12 March 2017
AMANA TA CE 1
AMANA TA CE
By
©Rash Kardam
1
Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassan ne ya fito daga dakinsa cikin manyan kaya, yayi shiga ta alfarma, dining yaje ya zauna hajiya fatima ne zaune tana jiran mai gidanta, bayan ya zauna ta masa sannu, ya amsa cikin sakin fuska ya kalleta yace Fatima ina Auta take, tace tana sana’arta har yanzu inaga bata farka ba, cikin kulawa ya kalli fatima yace hajiya ina fada miki kulum ki ringa kula min da Auta, cikin daure fuska tace Alhaji kulum haka kacewa yarinya duk ta san garce sakalci ya mata yawa ta girma aman kamar wata jaririya, Alhaji ya nisa yace hmm fatima akwai maganar dana ke so muyi da Auta da Ammar, ana cikin haka sai ga Ammar ya shigo cikin ladabi ya gaidasu, suka amsa da sakin fiska, ya kalli Hajiya yace Mum ina Auta tace tana daki tana sana’ar ta na baccin sage barinje na tasota, Ammar ya mike da nufin komawa falon Abba yace aaa Ammar bama haka ai kaima dana ne don ina jinka ajikina kazauna mu karya tare, ana haka sai ga Mum tafito Auta na biye da ita, yau anyi sa’ah harta yiwanka da wuri bata tsaya baccin gadonta ba, cikin zazza kar muryanta ta gaida Dad dinta da Mum san nan Ammar cikin kulawa ya amsa, kusa da Dad ta zauna suka karya bayan sun gama suka koma falo, dad ya zauna mum na gefensa Ammar na kasa tana zaune, Autar Hajiya na kusa da ita, Abba ya dago cikin muryansa mai sa sanyin jiki kalo daya zaka masa ka gane yana cikin taradadadi, Zainab ya ambata, Autar Hajiya sai da taji sunan har cikin ranta tasan dad baya kiran sunan ta haka kurum sai da dalili, ta amsa da na’am dad, Dad ya kalle ta yace Zainab ina son insanar dake wani abu, sanana inaso ko bayan raina Auta kikasance mai hakuri da biyya ga wanda zakiyi tarayya dasu san nan ki rike mutuncinki, karki sake kiyi watsi da tarbiyan da muka miki, nasan ki amma ina son ki kara rike mutun ciki, ki rike Adu’ah a duk inda kike, Zainab idonta duk ya ciko da kwala don tun da take da dad bai taba mata zance makamancun haka ba,maganar dad ne ya katse mata tunani, Ammar ya kira ya amsa, dad yaci gaba dacewa Ammar kai kadai na yarda da kai acikin wayanda mukayi tarayya, kaine ka rike min “AMANA” ta don mutane yanzu ba yarda, san nan ko bayan raina banyarda ka bar Zainab ba ga “AMANARTA” na baka kai kadai nasan zaka kula min da ita, cikin sanyi jiki Ammar yace dad mai yasa kake irin wan nan maganan Dad yayi murmushin manya yace Ammar da Zainab atare, yace kukadai zan sanar da maganan nan kusani akwai wayanda suke min barazanan kashe ni da iyali na akan dukiyata, da nanema da gumi na, nikuma naki amsamusu sabida mutuwa da rayuwa tana hannun Allah, ba wanda ya isa ya kashe wani face da izinin Allah. Cikin damuwa Auta da Ammar sukacewa suwaye dad murmushi yayi yace ka kyalesu kawai zan sanar muku amma bayanzu ba, hajiya ma tayi musu nasiha sosai, dad ya mike ya fita hajiya tayi daki Auta kuka takeyi Ammar ne ya rarrasheta sai da tayi shiru kafin ya fito harabar gidan nan sale suka fara masa kallon bansa da kuma zaka sani yau, musa kam dariya yayi sosai kafin yace mun kusa ganin karshen wan nan rigima taka da kafafa kamar gidan ubanka, an samu gidin zama sai nuna isa kamar dan gd ko ta kansu bai bi ba ya wuce dakinsa shidai yana fatan Allah ya tsaresa da sharrin masu sharri.
Dad bai dawo ba sai kusan 10 lokacolin Auta tayi bacci hira sukayi sosai da Hajiya kafin yace bari ya watsa ruwa bayan yayi wanka hajiya fatima tafito cikin kayan baccinta mai daukar hankali ta nufi dakin Alhaji sun yi hira sosai kafin suka kwanta, Misalin karfe 2 gari yayi shiru sai sai hadirin daya hadu gari yayi baki2 nan take ruwa ya tsinke sosai kamar da bakin kwarya, kowani mutum na gidansa yana bacci, wata bakar jeep ce mai bakar glas na ga tanufo gaye din gidan Alhaji Al-hassan sai da suka fito duka kwan kwasa wa mai gadi ya bude musu suka shiga, duk da ruwan da akeyi bai dame
dame musuba kalo daya zaka musu kasan ba alkairi bane, atare dasu, sun rufe fidkokinsu da marks bakinsu da kwayan ido su da kofar hancinsu ke waje, magana sukayi tsakaninsu wanda sukazo a jeep dasu sale da musa, da alaman dai sun san da zuwansu, bayan sun gama ne, suka nufi cikin gida ko da suka shiga dakin Alhaji suka nufa suka samesi da hajiya suna tare,
Ammar ko yatashi tun karfe daya yasoma sallah nafilan da yasabayi duk dare bayan ya idar duk da ruwanda da akeyi yaji alamar shigowan mota da sauri ya leka nan yaga wasu da bakaken kaya sun rufe face dinsu duk abunda sukayi na kallonsu nan yaga sun ciro bin diga, yana kalon sun shiga ya bude kofar dakinsa cikin sanda ya kwanta a kasa yadoma tafiya da ciki kamar yanda soja suleyi a fagen yaki cikin fulawas ya soma bi ko da yaje ta kofar baya ya shiga yayi sa’ar kofar abude take nan ya tura a hankali, daman duk wanda yashigo ta baya dakin Auta zai fara samu don haka ya tura kofar a hankali.
yaganta tana bacci, a hankali ya soma tashita, cikin ikon Allah ta mike ba gyan gyadi, ihu zata sa ya toshe bakinta yace Auta kina jina wasu mutane sun zo gidan nan da kuma da alamar wayanda dad yafa da.suna son kashesa ne, nan cikinta ya fara rawa idonta ya ciko da kwalla, yace dau hijab diki mu leka muga don musan abinyi, kasa dauka tayi shi ya daukar mata ko ta kalmi bata tsaya dauka ba suka nufo falo a han kali suka leka, nan suka ga abunda ya razana su dad ne aka samasa bindiga da Hajiya suna kara lekawa nan suka ga fuskan Baba Sani da yayansa iyaka, alokacin suka dana kuna mar bingigan tass kake ji karan harbin bindiga, nan take auta tasaki kara atake suka juyo gurin da sukaji kara suna fadin suwaye suka nufo gunsu.
Yan uwa amin afuwa za ku ga ban2 dana farkon dana soma sakewa, yanzu na dawo da lbr daga tsakiya ne amin afuwa inaga hakan watakil zaifi.
Shin su Autar Hajiya da Ammar suna kubuta daga sharrin mutanen nan? bacin gashi gate din gdn a kulle.
Suwaye wayan nan mitanen?
Mai nene alakarsu da Dad?
Waye Ammar?
Don son jin amsarnan kubiyo Yar Gidan Kardamawa .
Taku akulum mai kaunarku
Friday, 3 March 2017
RAHEENAT 97-98
🐾🐾 Raheenat🐾🐾
©Rash Kardam💃🏻👈🏻
9⃣7⃣-9⃣8⃣
Sanye take cikin wani shadda brown yasha aiki ta kashe daurinta wato kudu maso gabar ta sha turarenta sai kamshi yake tashi cikin sallo da yanga ta fito falo tazo ta bayan MY ta rungumeshi tana yar dari tace My Yasir kullum kara sonka nakeyi mai do ta kan cin yar shi yayi yace babyna kulum kara kyau kikeyi dai dai lokacin sukaji sallama amsawa sukayi tana kokarin tashi ya riketa wata sukaga an turo a keken guragu, kallo daya suka mata suka ganeta asai Sadde ce ciki fushi yataso ke mai ya kawo ki gidan nan ko daya ke ni ne na manta ban sanar kiba na datse igiyar Aurena Uku dake kanki kukan fa take boyewa ne ya fito nan taso ma nimar gafaransa daki yatafi ya barta, heenat ne tazo kusa da ita tace Aunty Dadde ki share hawayenki zai yafe miki ba komai ya wuce nan ta roki gafaranta ta yafe mata, can ta hango Heedat dake wasa nan tace babyn kine tace eh ayya gata mai kyau Allah ya rayata heenat tace ameen, nan tace ina zuwa daki taje tasamu.MY saifa tamasa nasiha kafin ya yarda yafito yace ya yafe mata kudi yabata sosai taki karba sai da ya sake cimata ta karba kafin ta karba, heenat ma tafito mata da atamfofi da lees da kayan make up ta bata nan tamusu sallama ta tafi tana mai jin jina rayuwa wato haka take in kashuka mai kyau to zakaga mai kyau shiyasa akeso mutum ya kasance mai yadda da kadara da imani da Allah, gashi yanzu kowa nata ya gujeta, nan ta fashe da kuka.
Alhadulilah!!!.
Nan na kawo karshen wan na littafina mai suna Raheenat.
SADAUKARWA
na sadaukar da littafin nan ga iyayena abun Sona da Kauna na
Alhaji Abdullahi Yunusa Kardam da Hajiya Khadija Aliyu Abdullahi
YAYA NA
khadija Umar da Ja’afar Umar Musaddiq)
Godiya gareki Maman Safwan da irin Sharwarin da kika ban
Sister Maryam S Bello ina jin jina miki da irin kwarin gwiwan da kika ban gurin rubuta littafin an,
Godiya ga yan group dina
Zaujin Nuhr
Rash Kardam Hausa Novels
Marmue Home Of Novels
Hausa novels3
Ladies Vision
World Writers Association
Duniyar Littafin Hausa
Falmi Hausa Novels
Hausa Novels Book
Suhana Hausa Novels
Da duk sauran wayanda ban samu daman rubutawa ba.
Sai kun jini a Sabon
Littafina Mai
RAHEENAT 95-96
🐾🐾 Raheenat🐾🐾k
©Rash Kardam💃🏻👈🏻
9⃣5⃣-9⃣6⃣
Ko da su ka fito godiya ga Allah sukayi suka gabatar da kansu tabbas duk wanda yaga jameela to yaga heenat ko da suka gama su Abba suka fito suka mika godiyarsu ga Allah da ya hada heenat da iyayenta daga nan aka soma dibar abinci bayan aci ansha aka watse ciki da farin ciki, haka su heenat suka dawo gida ko da suka koma side dinsu wanka tayi tayi sallah, sanna sukaje babban falo inda kowa yake aka soma cin abinci cokali daya heenat ta kai bakinta nan taji zuciyarta ya suma tashi dan haka ruwan zafi kawai ta sha ko da dad dinta da su Abba suka tambayeta tace bakomai, haka sukayi hira adaddafe takoma dakinsu nan zazzabi ya rufe ta hankalin MY ya tashi matuka kasa mata wani abu yayi arude ya kira wayar cikin gida aiko A A ne ya dauka nan ya sanar amasa heenat bata jin dadi a rude suda su abba suka shigo likita ya kira bai dade ba ya zo ya dan dubata da tambayoyi, nan ya dauki fitsarin ta yace bari yaje lab komaiye zai dawo ya sanar musu allura ya mata tasamu bacci kafin ya tafi MY tagumi ya zuba ya sata agaba yana kallonta, ko da likita ya auna gwajin farko sakamako ya gwada ta na dauke da ciki wata biyu da kwanaki cikin murna ya kira A A yasanar masa duka sunyi murna, haka suka kwana washe gari likita yazo ya bata yan shawar wari, haka rayuwa mai dadi sukayi a yola ga soyayyan da suke ba da MY abun ba acewa komai saida sukayi sati uku kafin A A ya daukar musu jirgin da zai kawo su Bauchi ko da suka iso Bauchi daman yana da gida akarin dan haka gidanshi ya sauka, haka ya bar duk abunda zaiyi ya yi sati guda ko da ya tashi tafiya, Ya dauki takardun alkawarin da yayi ya mika ma Abba, shi kuma yace ba zai karba don allah yayi sai da AA yayi ta rokonsa kafin ya karba ya kuma rokeshi da ya ya rubuta takardan barin aiki sai ya dawo sucigaba da kasuwanci, ya debi kudi masu yawa ya ba ma H Maryam da Murja ya dauki duk dukiyarsa yayi signed kancewa ya mallaka ma heenat ya debi wasu masu yawa ya ba ma Suwaiba da company biyu, haka suka rabu cikin farinciki, akan duk karshen wata su heenat zasu na zua gaida su, haka gidan Alhaji Muhammad Dalhat ya kasance cikin farin ciki.
Ina lbr Sadde tun bayan barinta bauchi duka shirya suka je gun boka ko da sukaje suka tarar da boka bayida lfy inta kaice muku kafin su bar gun ya mutu gashi mutuwar wulakanci da kaskanci haka suka baro kauye batare da tayi nadama ba, bayan sun dawo suka sake daukar hanyan katsina gun wani boka a hanya sukayi hatsari yanzu haka kafar Sadde an yake ta hannunta kuma ya bar amfani sai a keken gura gu ake turata Karema kuwa an sheka lahira, sai dai fatan Allah ya yafe mana kura kuren mu na amsa da Ameen
Kwanaki sunja yau cikin H Maryam ya cika wata tara gashi ta tashi da wani matsana cin ciwon baya gani halin da take ciki yasa su heenat suka kaita asibiti cikin ikon Allah suna zuwa basu dade ba ta zan kado kyawawan yaranta biyu mace da na miji masu kama da Abba gasu kyawawa, bayan an gyarata suka dawo gida,
Haka gidan ya cika makil da yan gaisuwa lokacin cikin heenat ma ya fito su Aysha ma kulum sai ta zo, haka sukayi ta shirin suna, sai da ana gobe suna Aimana ta zo gida ya hadu gasu cikin farin ciki, ranan da Aimana tazo Ranan su H Jameela da Suwaiba suka zo AA Yola ba karamin barin kudi yayi ba baran ma da yaji marikiyar yarsa, haka sukayita aiki har washegari inda yaran suna, namiji aka samasa Muhammadul Akbar, macen kuwa aka samata AmatulRasheed, haka akayini gashi duk dan gin da suka zo sai an gwada musu iyayen heenat yakumbo mata zo ganin iyayen heenat bakaramin girgizatayi ba don tayi na damar abunda tamata daman duk lokacin da heenat ta samu manemi ita take turawa a fada musu yar tsuntuwane, kafin su ya kumbo su bar bauchi saida tanimi yafiyar heenat da maryam, haka aka watse a taro cikin farin ciki, rayuwa mai dadi sukeyi in kaje gidan Abba sai abun ya burgek
RAHEENAT 93-94
🐾🐾 Raheenat🐾🐾
©Rash Kardam💃🏻👈🏻
9⃣3⃣-9⃣4⃣
Kuka sosai jameela da heenat sukayi, AA Yola ne, yace muje muyi sallah, sai muci abinci, masalacin gidan sukaje, sukayi sallah sai bayan isha suka dawo duka aka hadu a dining aka ji abinci, hira sosai sukayi kafin aka kai su abba side guda shida MY, su h maryam ma daki aka ba ma kowa, heenat ko ita da mamanta suka kwana, washe gari da safe bayan sunyi sallah asuba, waje karfe goma kararrawa, ya buga, lokacin breakfast, yayi, ina da ga gefe naji kararrawar, tana cewa, “hy the food is ready😜😜 abun gwanin burgewa, kusan atare suka fito, kowa kaga fiskansa dauke da fara’a duk kansu sukayi breakfast, bayan sun kammala, A A Yola yace suje main fal, ko da suka isa ya daga waya ya kira suwaiba, yace tazo ta same sa, a main falo, sai da taji damm jiki ba kwari ta fito ko da ta iso, ta ga bakin fuska a falon nan take kanta ya kara daurewa, ganin h jameela a zaune bakara min mamaki taji ba nan jikinta yayi sanyi gumi yasoma tsatsafo mata, kusa da jameela ta zauna sai a lokacin ta lura da heenat, wani irin firgici ta shiga, wanda lokaci daya zaisa ka gane rashin gaskiyanta, A A Yola fara bude taro da Adu’ah bayan sun shafa ya sake gaisawa da Abba, san nan yace wa suwaiba ke ce baki san maike faruwa ba, ya nuna mata heenat ga diyata Allah bayya nar mana da ita, ga kuma wanda ya tsince ta nan jiya kece baki d lbr, don haka yanzu ina son Abba zai ba mu lbr, yanda abun ya kasance, abba yayi gyaran murya kafin ya fara basu lbr yanda akayi ya samu heenat da kuma yanda h maryam ta riketa harda rashin haihuwarta, kuma a sanadin hakurinta da rikon amanar da tayi yanzu haka ta na dauke da juna biyu, AA Yola ya jinjina al-amarin yayi godiya masu Abba san nan yace kamar yanda yayi Alkawari in Allah ya yarda zai cika don haka zai a kira yan sharidu su sanar ma duniya ya samu tilon yarsa ran jumma’a za’ayi kayetacen liyafa wanda ake gayyatar kowa da kowa, ko wa ka ganshi a falon fiskansa na dau ke da fara, ila suwaiba wanda take yake jikinta yayi sanyi tayi na damar abunda ta aikata, baran da taji lbr H Maryam ya za mo mata darasi a rayuwarta nan ta fara ni man gafarar uban giji ta kudiri aniyar niman yafiyansu Abba.
A A Yola yasa aka sanar da gayyata a kwai walima naranar Jumma’ah na murnan samun yarsa.
Duk inda kaza ga a 9ja maganar liyafa ake ni na dan tattaro kayan kasan akwati na don baza’ayi bani ba, zanje in ba ma idona 👀hakinsa,.
MY da heenat wani kula na musamman AA Yola yake basu, side guda ya sa aka ware musu abba da iya lensa, duk wani kayan da zasu sa a ranar liyafan yayi odarsu, MY da Heenat nasu blue da yellow colour yayi da Abba da iya lansa green da milk colour, A A Yola nasu kuma fari sol amma da da, shiri akeyi sosai, Suwaiba ko tana dari2 tana ga kamar za’a ganeta, haka sukayi ta shiri sosai.
Rana bata karya…… yauta ke jumma’ah
Duk wani mai naira ko hannu ra shuni sun halarci taron nan, maza da mata, gurin ya ka watu sosai, giri ya tsaru duk in da kaduba matan manya ne ko da na iso gun rasama ta ina zan zauna, daga nesa na hango ta wagar faty fashion lady, da irin su, Heedat da maman Safwan, hauwa sa’adu,ruky ma’aji, salima, ina juyawa na hango Pinky Lady aci gayu sai zuba taku take, su hajiya Fanta an sha kyau ba acea komai, Hadiza Hardawa, Faiza Y Ladan,ge fen damana kuma Yan®World Writers Association ® sai zuba kamshi suke, irin su Maman khairat, Raheynert, Billy Saraki, rookie sadau,Maman Aleesha, Zahra, ge fen hagu kuwa online writers na gani abun ba acrwa komai, su sis Marmu aci gayi kamar za’a zaban sarauniyar kyau, gasu Nuceeyluff, Teemaluff, Sheed
RAHEENAT 91-92
🐾🐾 Raheenat🐾🐾
©Rash Kardam💃🏻👈🏻
9⃣1⃣-9⃣2⃣
MY, Heenat, H murja suka mike, murja tace lfy mai ke faruwa, h maryam kasa magana tayi sai hawaye da ke bin funkanta, Abba ya ce ku zauna tukun, yace Maryam rigan da muka tsinci Raheenat, ya na nan ko ta ce eh, Alhamdulilah, yake dauko min jiki ba kwari ta tashi, h murja ta sake tambayar meye nan Abba ya mika mata jarida tasoma karanta wa harta gama tukum ta dago yace murja bari kiga wani abun mamaki ma tukun, MY da heenat sukam basu fahinci ko meyeba kansu ya daure,
H maryam ko da taje daki tayi nimar duniya ta rasa riga, jiki ba kwari ta zo ta fada ma Abba, yace aiko dole a war gaza dakin don shine shaidar mu ta farko, tukun, h murja tace ni fa ban gane ba nan ya basu lbr komai, heenat da take jin lbr ya mata wani iri kamar lbr, abba yace kutashi mushiga dakin nan muduba, ko da suka shiga suka war gaza dam n basu samu ba, sai can H maryam tace kutsaya a kwai wani karamin a kwatin da na boye a kasan gado ina ga acikinsa yake aiko aka daga gado sai ga akwati, nan suka bude tabbas ko ko kwanto babu heenat itace uar gidan AA Yola, nan hawaye kukan farin ciki tasoma Alhamdulilah yanzu ta gane ita ba yar shege bane yar halak ce, Abba yace yanzu dole sai mun hakura gobe yayi muje muyi booking din jirgi kwai gaba daya sai mu wuce baza mu tafi a mota ba ma don zai ja lokaci, haka heenat ta kwana farin ciki MY na makale da ita shima murnan yake, ko da gari ya waye Abba da MY suka je ABUKAR TAFAWA BALEWA AIRPORT, sukayi bookinh din zuwa yola, sukayi sa’ar an samu jirgin da zai je yola a ranan, haka suka je gida suka shirya karfe 2:12 driver ya kaisu airport suna zua ba da dadewa ba jirgi ya daga su sai yola,
koda suka isa address din jikin jari dar suka bi ko da suka je da farko an hana su shiga company ni AA Yola, sai da suka dau lokaci kafin abba yace dan allah su taimaka masa yazo ma AA Yola da muhimin lbr, aiko da security suka isar masa da sako sai da yayi ta fada yace bana ce kubar wula kanta mutane ba, mai yasa kuka hanasu shigowa, ko da aka zo da su duk ba yan gurin ba wanda ya lura da heenat, sun gaisa da Abba kafin yace yana son suyi magana da shi game da yarsa da ta bata, nan take A A Yola ma maida hankalinsa, abba yace ina son in maka wasu tambayoyi ne yace ina jinka malam,
Abba yace ko zaja iya tuna ranar da yarka ta bata, jimm ya danyi kafin yace22/Jan/1997, mamaki ne ya bayya na a fuskan Abba, yace ikon Allah ni kuma 23/Jan/1997, na tsinci wata yarinya, nan ya kwashe lbr ya fada ma AA Yola da irin jaridar da ya gani sannan, Yace ma MY ya miko masa akwatin, MY ya fita zuwa gunsu H Maryam da suke waje ya karbo, A A Yola mamaki farin ciki ya hana sa magana, ko da aka kawo akwati ya bude nan ya ciro kayar ba shaka sune nan AA Yola yace ma Abba ina yarinyan yace tana waje da sauri ya mike yace muje in ganta, ko da suka fita gun su h maryam suka je Abba ne yace Raheenatu a san yaye ta dago kanta, tass ta daura idonta akan AA Yola, suna hada ido bakinsa ya sima rawa ya na nuna ta da ya tsa don ko ba musu wan nan kamar ma ka dai ta isa shaida, nan ya zube a gun a sume abbane yay kansa da gudu nan security suka zo mai ke faru wa Abba yace ku taima ka min ko meye zakuji da ga baya, ruwa gora suka kawo aka yafa masa nan ya far fado, idonsa ya cika da hawaye, yace Alhamdulilah Allah abin godiya asai zanga diyata aduniya, nan ya tashi ya riko heenat kamar wani zai kwacet, yace muje kiga maman ki tan nan tana ta jiran dawowar ki, ya juyo ya kalli su abba yace kuzo muje, nan ta ke security din sa da body guard, suka rufa musu baya, mota ka bude musu suka shiga yayinda heenat da AA Yola suka shiga daya, wani katon ka tafaren gida na ga sun shiga, suna ajiye motarsu a parking spaces, ya rike hannuta suka fito, ko da suk shiga gidan masu aiki kall
RAHEENAT 89-90
🐾🐾 Raheenat🐾🐾
©Rash Kardam💃🏻👈🏻
8⃣9⃣ -9⃣0⃣
Da sairi ya isa kofar ya tura, bakaramin razana yayi da gani su Sadde ba ko far ya kulle, Sadde jikinta ne ya soma bari yar da bullan sukayi, heenat ko da gudu tayi bayi, don zafin bulalan ya shigeta key ta sa don tana ga zasu sake dukanta, Saddeqa yace wato ke baki da hankali ko mai ta miki kika zo har gida, kina dukanta ba Abba ya mi ki warning da zuwa gidan nan ba, jikin sadde sai rawa yakeyi tasan yau kashinta ya bushe don ransa ya baci sosai, tafiya yakeyi kamar wani zaki🐅 ya isa in da suka yarda bulala duka biyu ya hada, sannan ya zaro belt dinsa jibgarsu ya fara kamar wanda aka aikosa, sai da yasu jina jina, ihun da bb mai gadi yaji yasa yazo da guu yaji kofar arufe nan ya fara dukar kofar amma MY bai bude ba, ganin kar ayi kisa yasa ya kira abba ya fada masa, yace gashi zuwa, ko da Abba yazo sunyi yjuyin duniyar nan ya bude kofa ya ki ganin haka yasa shi, zuwa dakinsa ya dauko key ya bude dakin nan yaga jini yaga duk ya bata dakin, yana zuwa sai da ya mari MY yace baka da hankali ko zaka kashe su ne, nan ne ma yaga waye ido ya zaro mai ya kawu ku gida na ke👈🏻 bana ce kar kira zuwa ba, yace kuwuce fifita min da gani anan, sumu2 suka fita abba yayi ma MY fada kafin ya tambaye shi, mai ke faruwa nan ya fada masa abba yayi mamaki wai sadde wacce irin fitinaniya ne gidansa na lfy, tana so zata ruguza masa farin ciki, yace ina heenat din MY yace tana bayi abba da kan shi ya mata magana kafin tabude taci kuka😭😭 idonta har ya kumbura, abba yace dau hijab dinki mu tafi asibiti ko da sukaje tunda h murja sukaji abunda ya faru h maryam ta ce ita a sallameta ai tunda jikin da sauki nan doctor ta basu sallama su ka dawo gida, yan gidan Alhaji Muhammad Dalhat yanzu sun kasance cikin farin ciki da kaunar juna sun dauki kulawa soyayya sun daura akan cikin H Maryam, abun gwanin burgewa, MY kuwa da heenat soyayya suke sha ba na wasa ba kula na musamman yake bata, kuma ko a gaban su abba baya jin kunyar nuna mata soyayya ko ya rike hannunta dan haka Abba yace slzasu tare a sabon gidansa da ya gina acikin GRA layinsu daya gida uku ne a tsakani, MY kuwa ya tura takardunsa India a sabitin da ya musu aiki don yanzu hankalinsa ya koma can zai koma da aiki.
Sadde da Zubbe tun da suka bar gidan gidan su Zubbe suka wuce nan sadde tace kano zata je don ta koma gun boka, Zuber tace ki bari jikinki ya warke in kinje dole a tambayeki mai ya sameki tace hako za ayi. ta zauna zaman jinya.
Jarida da aka sake ya baza ko ina cikin ikon Allah ya iso bauchi kyauta ba da kudinka ba za’abaka,
Abbane ke tafiya kan hanyarsa ta zuwa kobi street, dai dai ran about din winti, market, an hada go slow a han kali suke matsawa sabida cikowar da akayi, Wani ne yazo dab glass din motar abba ya miko masa jarida oga gashi kyauta ka karanta dai dai lokacin go slow ya ragu mutumin ya wurga masa a cikin motarsa, ko da abba yaje yayi da muwarsa bai duba jaridar ba hasalima ya manta da ita, haka ya dawo gida,
Kwanaki sun ja yau cikin h maryam ya kwai wata biyar, yayinda heenat kuma tai wani kyau ta kara fresh, heenat suna ta shirin tarewa a gidansu ba wani abunda akasaya tunda dama tun tuni an sai mata komai yanzu sai zuwa randa zasu koma amata jere, tsakani ta da MY kuwa kulum cikin bama juna kulawata musamman yanzu a dakinsa take kwana in bata je h maryam zata kura ta tafi, duk wanda ya san heenat a da to yanzu ta canza ta kara cika tayi kyau, ni dai nace ko ta samu rabon gidan Abba😜😜.
Abba ne ya dawo gida a ko da yazo nan ya kunna TV tai dai lokacin da ake hira da AA Yola, kusan karshen maganansa yake cea mun ba da jarida an raba kyauta duk wanda Allah yasa ya ga yarnan ko lbr ya taimaka sai a lokacin Abba ya tuna da jaridar, da sauri ya
RAHEENAT 87-88
🐾🐾 Raheenat🐾🐾
©Rash Kardam💃🏻👈🏻
8⃣7⃣ -8⃣8⃣
A hankali ta bude ido taga shine, wani ajiyar zuciya ta sauke, cikin kunne ta ya darada mata kin cika tsoro da yawa, za me jikinta tayi, tayi sauri dauko himar zata sa, abun dariya yaso bashi, rike himain yayi yace mai zakiyi, tace zansa, yace ni kuma banso a samin yanzu cikin jin kunya ta sake da sauri tayi bayi tasa kayan bacci, tazo ta zauna tana jiran ya tafi, amma shiru han kusan goma da rabi, kafin tace Yaya bacci nake ji zan rufe kofa yace, ok barin rufe mana anan zan kwana ido:oops: za ro, mikewa yayi ya rufe kofar yana zuwa ya kashe wutar dakin:idea: dakin zuwa yayi ya janyo ta jikinsa suka kwanta ya musu Adu’ah, a haka har baci ya daukesu, da suba saida sukayi wanka kafin sukayi sallah, tare suka shiga kitchen suka hada breakfast, sun gama suka fito lokacin Abba ya fito suka gaida shi, yaji dadin ganinsu, yace su yi su shirya don su tafi asibiti, to suka amsa MY yaje dakinsa ya debo kayanda zaisa yazo ya samu heenat ta hada ruwan wanka🛁nanfa yace tare zasuyi
tace ya shiga in ya fito sai tashiga, bai tsaya saurarota ba ya dauketa cak sai bayi ya musu wanka ya fito ya shafe su da mai ya mata kwalliya kai in kaga MY ka dauka da ma can ya iya kwaliyar sosai tayi kyau shi ya dauko mata kayanda zata sa, pink din less ne heenat ba karamin kyau tayi ba, ya sanya ka yansa suka fito dining tare da Abba sukayi breakfast kafin sukaje asibiti, suka gaida h murja sanan suka gaida h maryam, heenat ta su ba ma h murja abinci haka h maryam ma suka ci suna santi, sai a lokacin Abba ya mika ma h Maryam results din test ko da ta karanta saida ta sake murtsuke 👀 taga ba mafarki takeyi ba nan wani dadi ya rufeta adu’ah tayi sosai, haka sukayi cikin farin ciki da daddare ma H Murja tace ma heenat su tafi, haka su dawo gida, dakinsa ya wuce yayi wanka, yau kam ya kudi aniyar mai da heenat cikakiyar mace, ko da yafito dakinta ya nufa ya samu har ta kwanta zuwa yayi mata kiss kafin ya bude sif dinta ya dauko fallen zani da hijab dinta, daukarta yayi kamar yarinya, ya wuce dakinsa ya na ajiye ta ta mike kamar mai shirin kuka, ya ce banson magana je ki dauro alwala, ba musu tayi alwala, tazo sukayi nafila, ya mata tambayoyi ta bashi amsa, ya nike sallayar kamo ta yayi suka hau gado ciki da bara ya fara shafarta suna hiran, inda sabo ta saba, kuma bata kawo komai ba, can ya soma canza salo, gani MY yasoma fita a hayyacinsa yasa na yamusu kofa🚪 na baro dàkin,
Sai kusan asuba ya saurara mata kafin ya kaita ya musu wanka🛀🏻 suka fito da asuba shi da kanshi yayi girkin ya jera a dining, nasu ya kawo daki shi da kanshi ya rinka bata har ta koshi, yace ta zauna shi zai je asibiti sai da rana zataje batayi musu, ya kaita dakinta ya kwantar ya kaimusu abinci asibiti haka suka yini sai yamma ya dawo lokacin ta dan warke, amma sai dai tafiyanta bai dawo normal ba, sai da ya bata abinci kafin ya dauketa ya kaita mota, ya jasu zuwa asibiti, ko da suka je h murja ta lura da tafiyarta shiyasa ma ta hanata yin komai da dare yayi suka musu sallama suka dawo gida, daren ranan ma MY bai barta ba, sai da ya mori dare, tunda ya dan dani zumar heenat yaji ta daban da Sadde nan ya gane matan ma suna suka tara akwai zara a cikisu, wa shegari da ya ga ta gaji yace sai dare zasu asibiti, batayi musu ba din bacci takeji sosai, nan ya mata sallama ya tafi.har yayi nisa ya tuna da yayi mantuwa ya jiyo da motarsa.
Sadde kuwa tun da ta bar gidan,gidansu zubbe ta tare don ta dau alwashin sai sunyi dukan mutuwa wa heenat kafin ta koma kani gurin boka, haka sukayi ta hada target, har suka gane yanzu ba a zuwa asibiti da heenat don haka suka sayo dorinarsu masu kyau suka basu mai, suka samo nikaf, suka shirya su biyu ita da zu
RAHEENAT 85-86
🐾🐾 Raheenat🐾🐾
©Rash Kardam💃🏻👈🏻
8⃣5⃣ -8⃣6⃣
MY ya kira Abba ya sanar masa, yace gashi nan zuwa, ba a dau lokaci ba Abba ya iso, kalo daya zaka masa kaga tashin han kalinsa karara, nan ya tabamye su tana ina suka shai da miji likitici suna dubata, suna tsaye suna jiran doctor, sai da aka samu kamar awa guda sai ga doctor Ikleema ta fito dauke da murmushi da wani pepper a hannunta, tunda Abba ya hangota ya yi saurin mikewa tsaye, ta iso ta kalli Abba tace sannu kufa, Alhaji congratulations, cikin rashin fahimta yake kallonta, cikin murmushi tace matarka tana dauke da shigar sabon ciki har na wata 3, Abba bai san lokacin da yayi kabbara ba nima nace ALLAHU AKBAR, Abba bai san lokacin da yayi “SUJUDU SHIKUR” nan ya fara jero kirari ma Allah, Heenat da idon ta ya kawo kwalan murna hawaye yana zuba murnatake ga hawaye ga dariya, H Murjama murna zaka gani afuskanta, godiya sukayi ma doctor, sannan Ikleema tace za’a bata gado, don yanayin cikin maisa ta laulayi ne, dakinda aka kwantar tar suka nufa, tana bacci, sai kusan awa biyu kafin h maryam ta farka ta ganta a asibiti, ta yun kuro da niyar mikewa taji jikinta ba kwari, H Murja ne ta taimaka mata ta kaita bayi tayi brush, sanan ta dauro alwala tayi sallah, kafin ta idar kuma heenat ta hada mata tea, ta kawo mata dai dai lokacin Abba suka shigo shi da MY, rike da kulolin abinci, ko da heenat ta miko mata tea kalo daya h maryam tayi ma tea din taji zuciyarta na tashi amai ta soma ji, da sauri tayi hanyan bayi garu ta dafa ganin haka yasa h murja ta riketa suka isa bayi daida tayi amai kafin suka, fito, kwanciya tayi akan gado, tana mai da numfashi a hankali, Abba yazo kusa da ita yana mata sannu, kai ta daga masa, yace to mai zakici, maryam, sai da ta danyi shiru kafin tace, towo nake so, abba yayi murmushi yace, da sauki gashi ko munzo da tuwon, aiko aka samata tuwo taci sosai harda kari, da daddare h murja ta ce ma MY su tafi gida da heenat ita zata zauna da hajiya a asibiti, hakan yayi ma Abba dadi, abunda yake buri da fata Allah ya cikamasa,
Ga maryam dinsa da juna biyu ga shi matan sa sun hada kai suna zaman lfusu, Alhamdulilah yace gaskiya ba abunda yafi zaman lfy dadi, Allah ya kara hada kawunan su na amsa da Ameen.sallama sukayi masu hajiya Abba da MY da Heenat suka nufo gida.
🍀Yola🍀
Yau take ranar da AA Yola zaiyi zama da yan jaridu, da marubuta, duk sun hallara, ba a dau lokaciba aka bude taro da Adu’ah, masu recoding nayi masu shooting nayi, marubuta kuma na hannu sunata aikinsu, AA Yola, ya soma basu bayani tunda ga haihuwar matarsa har daukan yarsa tillo daya sannan ya sa aka fara rarraba photo da aka dauka, sanan kuma ya karashe zance da cewa duk wanda ya kawo yarsa yayi alkawarin sai raba dukiyarsa gida uku kashi daya na wanda ya samu yar ko ya dauketa, amma kuma duk wanda zaizo ya tabbatar da kwakwaran shaida, kuma sanna yarsa tana kama da uwarta ne don kamar tayi kakinta, haka taro ya watse inda ya rarraba ma yan jaridu kudi masu yawa, bada wasu aka kai masalatai a tayasa da rokon Allah, hada da sadaka ma gajoyayu, kana biyu da yin zama su, aka soma sake jaridu daily trust, vanguard, rariya, aminiya, e t c, na karshen wanda na hango kuma A A Yola, yaji dadin yanda suka iya rubutu, da tsara magana kuma rubutunsu zai dau hankalin mai karatu, wato sune ®WORLD WRITERS ASSOCIATION ® sunyi rubutu mai tsari da kaya tarwa, AA Yola, ya sake musu kudi sosai don sun burge shi, nan aka sake jaridar ciki da wajen 9ja, duk inda kazaga zancen irin dukiyar da yasa da kuma tausaya ma halin da ke ciki.
Ko da su MY suk baro Asibiti suka dawo gida Abba ya wuce side dinsa, yayi da heenat ma ta wuce dakinta, MY ma dakinsa ya nufa, wanka yayi yasa ka ya
RAHEENAT 83-84
🐾🐾 Raheenat🐾🐾
®Rash Kardam💃🏻👈🏻
8⃣3⃣ -8⃣4⃣
Adviser yace ina da number shugabar kungiyar®WWA® zan kirata yanzu, sai musa date time, don su zo mubasu lbr da pic din babyn, ko ya kagani, well done hakan yayi, ko da ya kirata ba’a samu wata matsala ba, sun kuma sa date, 11/Jan/2016, 10:30am, zasuyi zama, AA Yola ya kima gida yana mai farin ciki da fatan bayya na diyarsa daya tillo, ko da ya isa gida, ya sanar ma jameela yanda sukayi, ba laifi taji dan dadi, tun daga ranan suka dun kufa Adu’ah sosai, Allah yasa suyi nasara, na amsa da Ameen.
MY ko cikin kwanciyar tunda ya shiga da heenat dakinsa, yake jagwalgwala, jikinta ko ina rawa yake hawaye nabin idonta, tana son yin kuka amma bata samu damar haka ba, don ya hada bakinsa 💏da na ta stitsa yake kamar ya samu sweet🍬, kamar da ga sama sukaji muryan H Maryam ta na kiran Heenat, Heenat, nan jikin heenat ya rawa, shiko ko ajikinsa, han kali ya mata magana a kunne, baby kin cika tsoro dayawa, dubi yanda jikinki ke rawa in ta gan mu ae ba komai, kina tare da mijin ki ne.
Bai sake taba sai da yaji alamun H Maryam ta koma dakin ta, jikin heenat bai bar rawa ba ta fito sai sanda take kamar muna fuka, sai da ta iso falo, dai dai nan h maryam suka fito ita da Abba suna, yar dariyansu, h maryam tace ina kika shiga ina neman ki?, ya naga idon ki yayi wani iri? kafin tace wani abu MY ya fito, turus yayi ganin su abba a falo nan yasoma sosa keya ya fara kame kame, Abba murmushin manya yayi, don sun ganosu, h maryam tace kije kikarasa aikin ki heenat, to tace da sauri ta bar gun don kunya yagama lulubeta, Abba yace son yau ba gai suwane, ah…ah…da.. man… Ina kwana Abba, cikin sakin fuska ya amsa, ya gaida h maryam ma ta amsa, cikin jin kunya yace bari ya tafi gida, don ya gane sun ganosu, ko dayatafi, h maryam tunda taga haka ta kara himma gurin gyara heenat.
Shikuma MY saransa kenan sai ya fakaici ba koma a falo sai ya lallabo yazo dakin heenat ya jagwal gwala, ya tafi abunshi, don shi ko a hakan da yatsaya farin ciki yakeji sosai,
Rayuwa haka tarinka tafiya cikin gidan Alhaji Muhammad Dalhat cikin kwanciyan hankali, basu da wani matsala don yanzu kan matan sa a hade yake, heenat ko da MY kulum da munta ya ke, itakuma ta kasa sakin jiki dashi,
Duk wani hanya da sadde taso tabi don jin wacece amaryan MY sam ta rasa, abunda ke da munta kulum MY a gida ya ke kwana, ko fita in yayi ta dau motarta tabi bayansa gudaya ne daga gidansu, sai gun aiki, wan nan abu ba karamin daure mata kai yayi ba, Zubee ta samu ta sanarta komai, zubee tace kinsan ya za’ayi, tace aa zamu samu wata mutura gidan matsayin yar aiki in anyi sa’a sun karbeta, to za musata tana lura da komai, Sadde tace haka za’ayi.
Sun nimo yar aiki ko da suka turata, da sallama tashiga gidan tayi sa’a h murja d maryam suna falo, ta gaidasu bayan sun amsa ta shaida musu bukatarta, da h maryam tace basu bukata, don ita bata faye son yan aiki ba, amma sai h murja tace ina ga zamu dauketa kinga ta rage ma heenat wasu aiki kafin ta tafi gidanta, h maryam bazata iya musu ba musanma kuma do heenat dinta aka dauka nan tace shi kenan sun tsayar a wata zasu na bata dubu goma zata na musu wanke wanke da shara, sukuma zasuna abincinsu, sukace yaushe zata fara zuwa tace gobe nan tamusu sallama ta tafi, koda jummai mai aiki taje ta sanar masu sadde sunji dadi, nan suka bata kudin aikin da zata musu 20k sukayi sallama akan sai sunzo jin bayani.
Washe gari jummai ta fara zuwa aiki tayi komai sai yamma ta bar gidan, aikinta take sosai ita dai har yanzu bataji ance na da wani gida ba, abunda ya dameta daya ne, yanda MY ke rike hanun heenat ko ya run
RAHEENAT 81-82
🐾🐾 Raheenat🐾🐾
Rash Kardam💃🏻👈🏻
8⃣1⃣-8⃣2⃣
Cikin baka ramin daga ma suwaiba hankali yayi ba, tunda ga wan nan rana ta kudiri aniyar zubar da cikin ko ta wani hali,.
Hajiya ko kamar ta san mai suwaib take shiryawa, tattari kayanta ta dawo gidan A A Yola, kula na musamma take ba ma Jameela, abinci ma ba kowane take ci ba ko da zata ce ta ga abu tana so to bara ta bari taci wanda ta ganinba don sai dai ta mata wani, hakan ya dami suwaiba har take zargin ko hajia ta gane tane, ka warta, Asmart Adam takira ta sanar mata mai ke faruwa, Asmart tace kar ki zubar da cikin nan yanzu za’a gane abu tasha kuma za’a iya tuhumanki, ki bari ta haihu ko a asibiti ko a gida ni zan san yanda za’ayi a dauke jaririn zai a yar dashi, tace haka za’ayi.
Kwana ki sun ja watani sun tafi yau cikin jamila, ya kai wata tara, in kaga cikin ka dauka twins zata haifa yayi girma sosai, kulawa kuwa guri Hajia da Suwaiba ba a magana kai ka rantse da zuciya daya takeyi, in tana kula da Jameela sai ka rasa tsakanin ita da hajiya da Alhaji wa yafi wani son cikin, duk wanda yaga yanda takeyi ba zai kawo da mungun nufi a zuciuarta ba, yau take jumma’ah tun da da rana Jameela take jin ciwon mara, haka tayita daurewa har zuwa dare, can tsakar dare ciwon ya tsananta, nan ta sanar da hajiya, hajiya ta kira suwaiba, ko da ta sai da mata haibuwane, nan tace bari ta dau ko key din motarta su tafi asibiti hajia tace driver fa tace yana bacci kyaleshi kawai, hajia tace ko za a fada ma Ahmad ne suwaiba tace yanzu in mun fada masa hankalinsa zai tashi muje kawai, ko da suwaiba ta shiga daki sai da takira Asmart Adam ta fada mata tace karki damu yanzu kuje asibitin, tace to, tace kar ki bari kuje asalin asibitin ku kuje wani tace ti ko da ta fito suka saka jameela a mota sukayi asibiti ana zuwa basu dade ba ta haihu, koda nurse suka gyarata, suka gyara baby, sauran suka fita nan akace suje su kawo kaya asa ma baby din, suwaiba tace yana mota, Suwaiba tace bara dauko ba, ko da suka kawo kaya aka sa ma baby take aka sallame su, duk yanda suka so su saci yarinya basu samu da ma ba haka suka hakura.
Ko da suka dawo gida tasa aka kira mata AA Yola nan ta saida masa Jameela ta haihu kar kuso kuga murna a gunsa, washe kari ya dawo, haka a kasoma shir shiryen suna, gashi kulum gidan da baki da ma yau ba jama’a sosai, subaiba ne sukayi waya da Asmart mai suka kitsa ni dai shewarsu naji, nan Suwaiba ta tafi dakin hajia hira sukeyi sosai, a gate kuwa masu gadin AA Yola, ne zaine bakin gate, sai wata mata da nikaf da doguwar riga, da goyo a bayanta tashigo, masu gadi suka tambayeta da ga ina tace ita yar uwar Jameela ce ta yola da zama, ganin matar oga basu kawo komaiba, suka barta ta shiga, ko da tasiga gidan side jamila tawuce bata ga kowa a falo ba, uwar daki ta nufa nan ta ciro abunda ke bayanta, asau tedy ta goya, ta wurgar, ko da ta leka, ta hango Jameela da alaman wanka zata shiga, amma digital camera ce a hanun ta yar karama, zuwa tayi ta ta daukar baby a photo, yarinya mai kyau mai kama uwart, kana ganinsu ka ga fulani asali, ko da ta gama daukata, tasa camera a sif, tashiga wanka, matar nan na ganin haka da sanda tazo ta dauki yar ta goyata, tafito ko da ta fito masu hadi basu zargeta ba tafita abunta, ko da tafita motar bauchi tashiga irin kananu motar nan take suka dau hanya, sai da sukayi tafiya mai nisa kafin har kusan takwas na dare kafin suka iso Bauchi, ko da ta iso bauchi hitel taje ta kama, yarinya yunwa ya soma damunta, don dai ma tana da hakuri ne, mafaran yara tasoyo a wasu shop da ke hotel din na cikin gari,nan ta ba ma yar yasha sosai, ksfin suka kwanta, ko da gari ya waye, bayan ta karya, fitowa tayi, ta tsari mai tazi yakaita tashar gombe, anan ta shiga mota, ko da su
RAHEENAT 79-80
🐾🐾 Raheenat🐾🐾
Rash Kardam💃🏻👈🏻
7⃣9⃣ -8⃣0⃣
Ki yi hakuri nima da kika gani Jameela daurewa ka wai nakeyi ace yata daya tilo wacce nake ji da ita, Adu’ah kawai zamu kara tsatantawa, Allah ya bayyanata, amma duk wanda nasan da sa hannunsa abatar, bazan yafe masa ba don ya ruguza mana farin cikin mu na shekara da dama, amma ba komai Allah na tare da mu, Allah ya bayya nata Ameen ta amsa cikin muryan rashin lfy, tashi yayi yafita ya nufi dakin Hajiya Suwaiba da sallama ya shiga ta na ganinsa, ta mike daga kwanciyar da take, sannu da zuwa, cikin kulawa tace Alhaji ya na ganka haka, karasa zama yayi yace ae dole, batar yarin yar nan yana so ya dawo min sabo don na daure amma haka kurum jikina ke ban zamiyi nasara za a sameta, gashi ciwon Jameela sai gaba yakeyi, lamarin sai dai Allah ya kyauta, cikin zuciyar suwaiba tace ba Ameen ba, afili kuma tace Alhaji ni dai da zakubi nawa da an hakura kawai yau shekara sha takwas fa, wani khafa yayi tare da mata wani mugun kalo, yace ko kin manta cewa ita kadai Allah ya ban duk abun da na tara ace banda magaji, kuma ko yanzu a wani hali take oho ban saniba cikin jin dado ko wahala, wasu hawaye ne suka zubo masa.
Waye Alhaji Ahmad Aliyu Yola
Alhaji AA Yola sha hararen dan kasuwa ne mai ji da nera a 9ja ciki da waje ba wanda bai sanshi ba, shine na daya acikin Masu kudin 9ja, daga shi sai Aliko Dan Gwate, wa yanda ake ji dasu ta fanni business, AA Yola, Allah ya azurta shi da kudi sosai, yana tare da Matarsa Kwaya daya Hajiya Suwaiba Wasiri, yar asalin yola ce itama, sun debi sheka bakwai da Aurw amma shiru ba lbr haihuwa, nan hankalinsu ya tashi, amma AA Yola duk da haka yana kwantar mata da hankali, kulum sai ta dameshi suje asibiti, Visa ya shiry ya suka fati Egypt don duba lfyta ko dasu ka je likitoci sunyi binci kensu sun tabbatar matsalar daga gareta ne bazata samu haihuwa ba, sabida zuciyarta ba zai dauki nauyi yaro ba, hajiya suwaiba ba karamin kuka tayi sosaiba, duk da haka bata daddara ba tace ma Alhaji suje Saudiya akara duba ta, bai mata musu ba, da ga Egypt suka wuce saudi, d same abudaya aka fada musu abban asibitin saudia, tun daga wan nan rana tashiga tashin hankali sosai amma AA Yola yace ta kwantar da hankalinta, ba zai kara aure ba, haka yayi ta lalabata har suka dawo 9ja.
Haka sukayi ta rayuwa cikin soyayya da kauna har suka samu 2 years bai taba nuna mata damuwarsa, suna cikin shekara na uku bayan dawowansu, Maman AA Yola, ta daga masa hankali sai daifa ya kara Aure don ita bazata ita zama bata jikanta ba, kulum sai ta masa magana amma sai dai yayi ta bata hakuri, data ga abun ba yibane, takirashi ko ya kara Aure ko kuma ta tsine masa, nan yashiga tashin hankali ba kadan ba, ko da yasamu suwaiba da magana, bata bashi wata matsalaba ta goya bayan yayi Aure ya bi “UMURNIN UWARSA”.
a san yaye yace mata shi ba zai iya zuwa nimar mace ba amma zai samu hajiyarsa duk yansa tace haka za ayi.
Ko da ya sanar da hajiarsa tace abu mai Saul ne a kwai kawarta, yar Niger ce Maradi sunyi zamar mutunci, kafin su koma Nijar amma suna waya da ita akai akai don haka ina ga yarta jamila zaka nima gata da kyau ga ilimi ga hankali, yace ma hajiya Jameela gidan Malam Ja’afar kike nufi tace ita fa, sau da ya danyi jim kafin yace shikenan, tace to kashirya sai kuje Kuma bana son abata lokaci zan yi waya da ita Maman Jameela.
haka ko akayi ko da sukayi waya, sun amince, ba bata lokaci sukaje Niger, basu samu matsala da Malam Ja’afar ya basa jamila akan sati mai zuwa za’a daura aure, kuma ya hutar dasu yin komai zaiyi sun yi godia, ko da sati yazo bata lokaci aka yi aure ya taho da amaryansa.
Hajiyansa da kanta ta hadasu dukansu, jameela da Suwaiba ta musu nasiha sosai, game d suyi zaman
RAHEENAT 77-78
🐾🐾 Raheenat🐾🐾
Rash Kardam💃🏻👈🏻
7⃣7⃣ -7⃣8⃣
Ko da ta isa gidan su Zubee ta sanar musu sun jajanta Al-amarin bakadan ba, nan suka ta bata munanan, shawara tace ni yanzu kano zan tafi, Zeenat tace kafin ki tafi ki koma gidan kiyi ta hura masa wutar kuma kisan wacece Amaryan don muje mu mata rashin mutunci da iyayenta, nan tace ko kin bada shawara kuwa, gida takoma tayi kuka iya isarta, san nan takudiri aniyar bazaman lfy tsakanita da MY da kuma iyayensa.
Abba cikin bacin rai ya wuce dakinsa tabbas baitaba sanin rashin kunyan Sadde ba sai yau kulum lbr ya ke ji nan ya gode ma Allah da ya kawo heenat rayuwansu, don yasan dansa ya samu mace ta gari da zaiyi Alfari da ita, H Murja ma daki ta nufa, MY yabi bayanta hakuri ya bata sosai, yayi shiru yana son yaji wa’aka aura masa, sai da ya dade a gurin, h murja kuwa ta yi duk abunda zatayi kafin, ta dawo falo ta ga baitafi ba, zuwa tayi ta zauna, kusa dashi tace lfy dai ko, cikin sanyin murya yace Mum dan Allah wacece Abba ya Auramin sai da ta danyi jumm kafin tace kanwarka, cikin rashin fahimta yace wata kan wata, tace Raheenat mana, ido ya zaro:oops: waje cike da mamaki yace wacce mum cikin tsawa tace Raheenat nawa ne a gidan nan, yace mum ko kun manta ba Aure a tsakanina da ita, murmushi tayi kafin tace da Aure mana, kansa duk ya daure, sunansa ta kira kafin ta fara basa lbr abunda ya faru ba karamin murna yayi ba sosai, aziciyarsa, asai daman zai samu Raheenat kuma daman ba Ubansu daya ba, tabbas yanzu yasan yayi Aure ya Auri wace ya keso, muryan H Murja ya dawo da shi daga tunani, ka rike yarinyan na da amana kaga bata dakowa sai mu, gata da hankali nasan bazaka taba da nasanin Aurenta ba.
Allah ya maka Albarka Allah ya baku zuri’ah na garinya amsa da Ameen, ransa yau fari kal sai karfe tara na dare ya bar gidan, duk yanda yaso yaga heenat sam taki fitowa baranda ta gane yau ya san matsayinta a gunsa da gidan, duk sai taji kunyan su Abba takeji
Ko da ya isa, sai da yayi Nafila ya gode ma Allah, kuma ya kudurta a ransa daga ranan ya dawo yin kiyamul-lail, don na da matukar amfani ga dan Adam san na ko wacce Sallah sai ya mata nafila, ila la’asar da ba a mata, ya kwana 2 yana zuwa amma sam bai samu ganin Heenat ba duk yanda yaso ya ganta buya takeyi.
Haka a gida sam yafita harkan Sadde ta manta da wata ab wai Sadde. itako duk wani hanyan da zata san waya Aura ta rasa haka zata zo da niyar tsefe masa rashin kunya inta ga yanayin sa saita tsorata ta koma, ni Rash nace ” asai kura yasan gidan mai babban sanda,😜😜
heenat ke ta aikinta kasance wan yau Asabar ba aiki, duk mutanen gidan, suna bacci, riga da skirt ne ajikinta sun kamata sosai, don ko hijab bb ajikinta don tasan ba mai shigowa, aiki take sosai, can taji alamun an shigo kafin ta juya, taji kamshin turarensa ya bugi hancinta, ko ba shakka ta san na MY ne, kafin ta juyo sai ji tayi an rike mata kugu tabaya,aiko tana jiyowa, suka fiskanci juna har yana iya jiyo numfashita, so ma kiciniyar kwace kanta tayi amma ta kasa, ganin haka yasa ya rungumeta sosai, a hankali ya soma jan ta zuwa dakinsa, na gidan ganin zata bashi matsala, yasa ya dauketa cak kamar yar tsana, bai direta ko ina ba sai kan katuwar katifan da ke dakin cikin rawar murya ta soma bashi hakuri shhhhh yace mata, mai kike tsoro ko kin manta cewan kina tare da Mijinki ne, zatayi magana, ya hada bakinsa saida ya tsotsa san ransa kafin ya gan garo zuwa kunneta, harshesa yasa ya fara mata waa dashi acikin kunnenta, jikin heenat in banda rawa ba abunda yake, ko ganin sun shiga duniyar masoya yasa na jawo musu kofar dakin nafito,.
Yola
Wani kata faren falo ne, mai dauke da kujeru jajaye da baki haka labulayen ciki duk wasu kayan alatu
Popular Posts
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(AUGUST 2016)* ...
-
MOTAR KWADAYI RASH KARDAM Duk launin kalan idonta, sun canza izuwa ja. Hannu tasa a tsakanin cinyanta tana mammatsewa,Bad Boy yana ga...
-
AMANA TA CE By ©Rash Kardam 1 Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassa...
-
🐾🐾Raheenat🐾🐾 1 Yarinya ce yar kimanin shekara 12 ta yanko a guje ta fada jikin Dad...
-
MOTAR KWADAYI By Rash Kardam 21-25 Jan motar yayi, suka bar cikin Silver Sand Hotel, bai zarce da su ko ina ba, sai gid...
-
BAZATA By ©Rash Kardam 1 Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan l...
-
π»π»π»π»π»π»π»π» ππ»BABBAN KUSKERENππ» ππ»DANA TAFKA ππ» π»π»π» ππ»ππ» ...
-
[6/5/6:30pm] 🌲RASH KARDAM🌲🌲 & 🎋SADEEY S ADAM🎋 ...
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(JULY 2016)* ...
-
π»π»π»π»π»π»π»π» ππ»BABBAN KUSKERENππ» ππ»DANA TAFKA ππ» π»π»π» ππ»ππ» ...