New Post

Friday, 3 March 2017

RAHEENAT 49-50

🐾🐾 Raheenat🐾🐾

Rash Kardam💃🏻👈🏻

            4⃣9⃣-5⃣0⃣

Cikin bacin rai:( ta naga hannunta, da niyan kai mishi mari👋🏻, komai ta tuna sai ta sauke, haayene ke bin fuskanta, shiko ko gizau bai yi ba, illa kallon ta da ya ke yi da mamaki, idonsa ya canza kala zuwa ja. A mardiya ce ta fito cikin bacin rai ta soma mata fada, don taga abunda tamasa lokacin tazo wucewa zuwa kicin, hakuri ta soma ba ma Sani, heenat ko da gudu tayi dakin su, kan gado ta fada ta saki kuka mai ban tauayi, azuciyarta tana cewa mai yasa zai zo ya dameta itakam, tayi Ritayar soyayya💔 don ta wahala. A mardiya ta ce masani ya zauna ba musu ya zauna, hakuri ta kara bashi kafin tace ya yi ma Heenat uzuri don a kwai dalilinta ankin amince masa nan ta bashi lbr irin walaha da tasha akan soyayya❤, ya tausaya mata sosai kuma baiga laifinta ba akan abunda tamasa sai ma sonta da yaji💑 ya kara shi ganshi, yace Aunty ba komai zanyi ta hakuri da duk wani fushinta harta sauko, tace bakomai nima zan maka iya kokarina, godiya yayi sosai, tace ba komai Allah ya dai daita tsakanin ku ya amsa da ameen, kafin ya mata sallama ya tafi.
       Waye Sani Baba Waziri

Sani haifafen dan Misau ne Babansa shine Wazirin Misau mai saruwa ya rasu tun sani na karami, sai Babban yayansu dawo dasu Kaduna gurin aikinshi, nan suka cigaba da rayuwansu, haka maifiyarsa Sani ta kula dàshi har ya girma yayi degree disa a ABU Zariya Businesses ya karanta, yanzu yana aiki a company su, na sai da motoci shida yayansa.

Heenat tayi kuka sosai ga tunanin da ke da munta hartana jin kirjinta na nauyi, haka har’aka kira Sallah magriba tayi sallah ta bayantabidar tayin nafila taro ki Allah ya kawo mata sauki a Al’amuranta, bata tashi a sallaya ba sai da tajira Isha’i, tana idarwa tayi shafa’i da wuturi, ko ta kan abinci bata bi ba tayi kwanciyanta lamo a kan gado, har gari ya waye, taje ta gaida A Mardiya, da Abban Sophia, kafin tafito tayi yan aiki da zatayi bayan sun karya, ta wanke kwanukan da suka bata, A Mardiya ne ta aiko a ka kirata, taje ta sameta a daki tamata nasiha sosai ga me da abinda tayi ma sani jiya, tace baki san wanda Allah ya zaba miki ba in kika wulakanta sa fa kuma ya zama shine mijinki fa, ta dan rarrasheta tare nasiho, jikin heenat yayi sanyi hakuri ta bata, tace bazata kara wukanta shi ba, A mardiya taji dadi ta sanya mata Albarka, san na suka canz hira, ba laifi ta dan saki jikinta ko ba komai ta dan samu sa ida.haka tayita walwalanta yau kana 2 da zuwan Sani duk da bason soyayyan takeyi ba amma tunaninsa ya hanata sakat.

Sani ko tunda ya bar gidan duk da baisamu karbuwa agun sahibarsa ba, amma yaji dama dama, ko don karbar da Aunty mardiya ta masa yasan xai samu nasara da ikon Allah, bai yi tunani komawa gidan washe gariba sai bayan kwana2 yayi shirinsa, cikin shadda brown yayi matukar kyau, yana fitowa, a gida sai da ya biya kasuwa yayi masu heenat sayya, sosai da sophia, ya kashe kudi ba kadan ba, kafin ya kamo hanyan gida, yana isowa bai samu wata matsalaba mai gadi ya gane shi dan haka ya je ya sanar da A Mardy, tace ya shigo dashi, sun gaisa suka danyi hira sosai, kafin tace masa ta nazuwa, dakin su heenat taje ta sameta tamata nasiha sosai sannan ta shaida mata sani ya zo yana falo, kuma bata yarda ta masa abunda zai bata masa rai ba, to ta amsa hijab dinta tasa, tafita, fa sallama ta shiga ya amsa fiska sake😄 ta nimi guri ta zauna, ta gaida shi, ya amsa, bata sake cemasa komai ba ta sunkuyar da kanta, gurin shiru kafin sani ya daure ya ce Heenat ya kk? lfy ta amsa, yace ina mai kara baki hakuri nasan nayi miki laifi amma kiyi min afuwa, uhummm tace ya ciga ba surutu shi bata amsa ba,bai dade ba ya ce zai wuce takira masa Aunty Mardy sukayi salla

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts