New Post

Friday, 17 March 2017

AMANA TA CE 3

:   AMANA TA CE 
                 By
©Rasheedah .A. Kardam
  
        ®WWA®
     3                  
Ya balle window din ya fara fitar da Auta kafin ta zo fita wani kwalban glass a jikin window din ya yanke shi ya shiga sosai, ya ji zafi harsai da yace washhhh, dai2 lokacin su baba sani suka balle kofa suka nufo shi cikin zafin nama ya dirka ga jini sai zuba ya keyi sosai, da sauri Ammar ya yakwanta a kasa ta gefen window, cikin hantsari ya fisgo Auta ta fadi kasa wanda faduwar wata ya dai2 da wani dutsi nan ta buge bakinta sai ga jini, kara tasa yayi sairin toshe mata baki, su gumus da kawu isiya suna isowa harbi suka fara amma bai kai ta inda su Auta suke ba, baba sani ne ya ciza yatsa  don ya ji haushi ga window ya musu kankanta baza su iya fita ba da sauri yace ku zo mu zaga mu bisu da sauri suka fita ga ruwa  haryanzu zuba yakeyi sosai.
Ammar na ganin sun bar window yayi kokarin rashi ga jiri na debansa don jininsa ya zuba sosai, ga Auta kuma jiki ba kwari, ya mike yana tan gadi ya dagata kasa tsayuwa tayijijjigata yayi da kyar sai ta sauke ajiyar hrt  kafin ya mikar da ita suna mikewa suka hango motar su baba sani sun nufosu, nan ya fara janta da gudu tunda daga hayin rigasa layin waya suke gudu sai da suka wuce kantin yawo, kafin suka kara gudu dai2 zasu fita a hayin rigasa, Auta ta fadi da sauri ya dauketa ganin in yace zai miki hanya zasu kamasa sai yayi gurin wani sabon gini wanda dogayen ciyawa   sun bullo agun gabansa kuma katon ruwa ne wanda ya taru, nan ya kaisu gun ya tsuguna ya tare Auta da numfashinta ke shirin daukewa
abunka da rashin sabo ga razana don Auta in banda girki  da take taya hajiya bata wani wahala, tasaba da rarrafen carpet tun tube da waya, baran da ta rage ita daya ma Dad da Hajiya ba irin gatan da basa mata.
Su baba sani da suka iso gurin nan suka fita ga ruwa  na sauka sosai duk dube2 da sukayi basu gansu ba,
Ammar kuwa suna gurin a tsugune da ke Auta ce ta jikin garu, nan wata kuna ma  ta fito sabida ruwan da ya dameta a gidanta tana fitowa kuwa kafar jidda ta hau sai da tazo kusa da gwiwanta ta danna mata cizo, har saubiyu duk da zafin da taji tayi saurin damke bakinta , Ammar na ganin haka ya kara matse bakin  nan kuwa kunamar    ta kara yanka mata cizo, sai murkususu take tayi, gumus da duna sukace alhaji ku tafi kawai mu zasu tsaya mu ne mesu in baku mu kawo maka gawarsu ba to zamu maka da lbr mutuwarsu, nan suka tafi da motar suka bar su gumus a gurin, sun dade suna dube2 sosai agun kafin suka soma fita,
Autakuwa wuya yayi wuya bata san lokacin da ta kwace bakinta ta saki kara da sauri su gumus suka juyo nan suka fara nufo gurin da sukaji karan,
Ammar na ganin haka ya mike yasoma jan Auta suna kara gaba kawai suka ga kato kogin ruwa ne a gabansu ga su gumus sun nufosu.
Abun gwanin tausayi nikaina Rash   bansan lokacin da na fara zubar da hawaye ba    .
Allah sarki su Auta da Ammar Allah ya kwace ku a hannu wayan nan Azzalumai din Ameen.
Sai dare  zakuji ni 
Taku a kullum mai kaunar ku  
            ®WHW®
    
Rash Kardam

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts