New Post

Friday, 3 March 2017

RAHEENAT 71-72

🐾🐾 Raheenat🐾🐾

Rash Kardam💃🏻👈🏻

           7⃣1⃣ -7⃣2⃣

MY na fita daga gida, restaurant yaje, yaci abinci sosai, san’nan ya biya kudi ya zaga gari, don yanzu baya son yawan magana sosai, ko da yagama ya wonsa sai dare ya koma gida, daki ya shiga ya kwanta ko nimar Sadde baiyi ba kuma, haka kurum yaji baya son zuwa gida don in yaje hankalinsa zai tashi in ya tuna Heenat tazama mallakin wani, bashiba, nan sai yaji abu ya tokari kirjinsa, haka ya shafe, sati guda ba inda yaje kuma ko da wasa baya yarda su hadu da sadde.

Asibiti kuwa heenat yau kwana ta biyar, H Maryam d Mardy da Aimana kulum a asibiti suke zama duk sun rame ga idonsu ya kumbura, sabida kuka, kulum sai sunyi, Abba ma ya rame sosai, sai dai donshi na miji ne yake daurewa.

Zaune suke sunyi jugum a bakin dakin da heenat take, ko wanne su da kalar nasa Adu’ah da sukeyi,daya da gacikin nurse din da suke kula da heenat ce tafito da gudu, tayi office din doctor Ikleema, tana zuwa ta sai damata Heenat ta farfado, da sauri docter Ikleema Umar ta bar aikin da take ta fito dakin suka nufa, nan su H Maryam suka mike sunyi cirko2 , docter ikleema ta dubata Alhamdulilah aiki yayi kyau don ta farfado, kuma abun ya zo da sauki, sai fatan Allah ya karamata lfy,sai da ta mata alura kafin ta fito da fara’arta ta nufo su tace Alhamdulilah maman ayi nasara, ta farfado, atare sukace Alhamdulilah, fisko kinsu dauke da farin ciki, H Maryam takira Abba ta sai da masa, yace Alhamdulilah gani a gate din asibitin yanzu na iso nima, ko da ya iso tare suka shiga daki, lokacin idonta na rufe amma tanajin duk abunda ke wakana, sai kuma jikinta ba karfi, jin an turo kofar yasa ta bude idonta, ganin Abba d su H Maryam, yasa ta tuno fa ba iyayenta bane, nan taji wani sabon kuka ya zomata, cikin sanyin jiki h maryam ta karasa gunta rike ta tayi, itama kukan tasoma, tace Heenat dan Allah kiyi shiru kiyi hakuri, kowani bawa da kaddaran da Allah ya daura masa, banson ki sake saka wani abu a ranki, kamar yanda tun farko kika rike mu iyaye, haryanzu ina son kirike mu, Heenat bakiyi maraici ba na iyaye tunda Nono na kika sha har na tsawon shekara daya da watanni, da sauri ta dago idon ta, da yayi ja tana kallonta alamar tambaya. tace kwarai kuwa, amma yanzu ba lokacin surutu bane ki bari sai kin samu sauki zakiji komai, gyaran muryan da Abba yayi ne yasa sukayi shiru Aunty Mardy taje toilet ta hada mata ruwan wanka ta kamata ta kaita bayi tayi wanka ta re da brush, kafin ta fito sallah tayi a zaune don jikinta ba kwari, ko da ta idar, har an hada mata tea da kyar ta sha don sai da Abba ya ta bata da kanshi kafin ta sha sosai, komaqa tayi ta kwanta. Tun daga wan nan rana likitoci sukaci gaba da kula da heenat sai da ta kara sati kafin yau doctor Ikleema Umar ta rubuta musu sallama tare da magun gunan da zata sha, kayan su ku tattara suka nufo mota don dawo gida.

Ina lbr Ango Sani, tun lokacin da ya iso gurin yaji ana hayaniya, nan ya tambayi maike faruwa, kansa ya dafe, tun a gurin yasoma kuka kamar karamin yaro, yaso ace ya Auri heenat dinsa amma ba yanda ya iya bai isa yayi musu ma Iyayensa ba don baida kamarsu, kuma yasan cire son heenat Abu ne mai wuya, bayan da suka dawo gida wani abokinsa ya shaida masa cewa An Aurar da Heenat ga MY, yashiga damuwa sai da ya rame sosai kallo daya zaka masa kasan yana damuwa, daga karshe dayaga bai da mafita ya hakura ya fauwala ma Allah komai, amma yace shida soyayya ba nan kusa ba, haka rayiwansa tacigaba da gudana, amma ya yi sanyi sosai.

MY kuwa tunda yaci sati bai futa aiki ba, ko da aka shiga wani sati ya fara fita aiki amma baya iya tsinana komai, damuwa ya masa yawa, yana son zuwa gida amma ya kasa, gashi in ya dawo daga aiki sadde ta rinka sahi aiki kenan yayi wannan, yayi wancan duk da cikin

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts