New Post

Friday, 3 March 2017

RAHEENAT 61-62

🐾🐾 Raheenat🐾🐾

Rash Kardam💃🏻👈🏻

            6⃣1⃣-6⃣2⃣

Sai dare ya isa kaduna, dakinsa ya shiga don ya gaji sosai, tea kawai yasha ya kwanta, bai dade da kwanciya ba bacci ya dauke sa, da asuba ya tashi ya shirya kafin yaje ya gaida Hajiyansa ya kuma saida masa yanda sukayi taji dadi, tace bari yayansa ya zo ran jumma’ah sai su je ayi maganar Aure,

Dakin sa ya kow ya sake kwanciya don ya gaji sosai, sai da ya kira heenat suka gaisa kafin y kwanta.

Sadde ce ke dukushe gaban MY tana bashi hakuri game da abunda tamasa, tunda taga ba sarki sai Allah tasoma basgi hakuri, kusan kulum sai ta bashi hakuri don ya fita a harkan ta kwata2, yau da kyar ta samu ya hakura, da kyar tun daga nan ta dan rage abunda take masa ba laifi ya saki jiki da ita, sai da suka samu sati da dai daituwarsu kafin tasoma masa zance zuwa gida, bai mata musu ba yace ta bari sai wani weekend sai ya kaita, batayi musu ba tayi godiya, haka ko akayi sati na zagowa yace suje suyi ma yan gidansu sallama, da farko taso taki da taga in bataje ba zai iya hana ta zuwa kafin ta mike sukaje, gaisuwar arziki batayi ma uwar saba sai kalon banza kafin sukayi ma Aunty M sallama, suka dawo fali suka zauna, saida Abba ya zo su ka gaisa shi suka masa Sallama kafin suka koma gidansu, ranan Sadde tai kwanan murna, ta kira karime ta shaida mata zuna zuwa gobe, don in tazo MY na dawo wa bauchi sai su wuce gurin boka, da misalin 10:00 suka dau hanyar kano, sai A da rana suka isa, anyi tarba ta mutuci ma MY, bayan suci sunsha ya gaida yan uwan sadde, sai da ya kwana washe gari ya kama hanyar Bauchi.

Sadde ko yana tafiya taje gun dadyn ta tace kudi take so ya bata akwai abunda take sin saya ba musu yabata 100k tayi murna ta hada da na gunta su, ran lahadi da safe tayi gidansu Karima, tana zuwa daman tana shieye, mota suka shiga sai meyere, ko da sukaje gun boka ta ce boka ni sonake ya zamana nice a gabansa, kuma yan’uwansa suna son su takura min, inason ya daina jin maganarsu kwata2 sai nawa, yace wan nan karamin aiki ne in ta kula, tace boka boka in dai bukata zai biya zan kula, yayi wata muguwar dariya kafin ya dauko wata kwarya ya bata da ruwa aciki da dan karanin ka dan gare na yawo aciki, yace wan nan kwaryan kar ki bari ya fadi a kasa ko ruwan ciki ya zube, zaki boyeshi ga wan nan fai fayin kurufe da shi san nan duk bayan sati zaki fito da kwaryan ki bude tasha iska tace to, ga wan nan garin maganin ki tabbatar kin samasa a abincinsa, in yaci shikenan, godiya sukayi kafin ta bashi kudu masu yawa suka dau hanyar kano ko da suka iso gidansu karima sukaje su ja ajiye akan in ana gobe zata koma sai ta kawo mata, tun daga ranan tashiga yawon gaida yan uwa har tayi kwana ki 6 tafara shirye shiryen dawowa Bauchi.

MY kuwa ko da ya bar Kano, ya dawo bauchi da dadare gidansu yazo, nan ya tarar da Heenat sun dawo yayi murna sosai amma bai gwada ba ya dan fiske, ko da ya shigo dakin H Maryam suka gaisa han kalinsa na kan Heenat gudun kar su gane shiyasa ya fita, tun daga wan nan ranan ya dawo yini agida shine zaman falo ko don ya ga heenat.

Kamar yan da sani yayi Alkawari ma Abba kuwa sati na cikawa magabatansa suka zo, sun bada sadaki 70k sun kuma tsayar da ranan Aure nan da wata daya, hakan ba karamin dadi yayi ma heenat da sani ba, bayan sun tafi da daddare MY yazo gida ya samu Abba a falo sai da suka danyi hira kafin ya ke sai da mishi maganan Auren Heenat ya gir giza sisa gumi sai karyo masa yakeyi duk da sanyin AC da ke falon, tai makonsa daya dare ne kuma Abba bai gane yanayin da yake ciki ba, da kyar ya iya cewa Allah ya sanya Alkairi, “azuciyarsa yace ba Ameen ba’ sallama yayi ma Abba ya tashi ya fita ko ta kan Abinci bai bi ba, don yaji yunwan ma baya ji, gidansa ya nufa, ya kwanta ya rasa me ke masa dadi abun duniya ya ishesh

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts