New Post

Friday, 17 March 2017

AMANA TA CE 8

:   AMANA TA CE 
                        By
©Rasheedah .A. Kardam
  
                ®WWA®
          8                   
Bayan Auta tasha maganin, sai aka dawo kan Ammar nan shima ya kunce daurin da yayi ma ciwonsa, tsohon nan da naji inna laure nakira da malam, ya dauko wasu magun guna, ya wanke masa ciwon da wani farin ruwa, nan ya haungo karamin glass ya shiga hannun, sai da ya dauko aska ya ciro glass din, duk da Ammar na miji ne sai da na ga indonsa yayi jajazur da alamar yana jin zafi sosai, baran ciwon ya kwana shiyasa, Auta kam kasa jure gani tayi sai kifa kanta tayi tana kuka maras sauti…,
wai yau itace a kungurmin kauyen da ko wuta babu bare ruwan fanfo, kafin asauko gun kwanciya mai kyau, nan take kalaman Dad dinta ya fado mata, inda yake mata nasihan sa na karshe akan ta yi hakuri a duk inda tasamu kanta, sabida yanayin rayuwa.
Allah sarki duniya kenan wai ace su baba sani su zasu kashe iyayenta akan dukiya da son duniya, mai suka maida zumunci ne ga cin “Amana” wan nan wani irin rayuwa ne sam tausayi ya kaurace a idon jama’a basa tunawa zasu mutu su koma ga Allah, in har kayi mai kyau zaka taras, kwanciyan kabari ma akabar mutum dashi babban aiki ne bare ace ka aikata mumunan abu har akaika wutar yasalam!!… Innalilahi wa inna ilaihi raji’un duniya tazo karshe wayan nan abun duk alamun karshen duniya ne Allah ya kyauta yasa mudace da karshe mai kyau ameen.
Hawaye ke gan garimata daga idonta, tayi nisa cikin tunani, sai ji tayi ana share mata hawaye, tana daga ido taga Ammar ne, shima hawayen yakeyi sai alokacin tasamu tasaki kuka mai ban tausayi, shima kukan yasaki, an rasa mai rarrashin wani.
Malam da inna laure sun zuba musu ido sai kallonsu sukeyi, tabbas ko basu fada musuba suna cikin tsananin tashin hankali, nan take ina kaure ta fara hawayen tausayi, malam idonsa yayi ja sosai, malam kenan akwai tausayi ga taimako.
malam yace bawan Allah kai na mijine ka kasance mai juriya a kowani hali duk da bansan mai yasame ku ba aman da alama kuna cikin tashin hankali, kuyi hakuri, kusani duk tsanani yana tare da sauki, kuyi hakuri ku bar ma Allah komai, zai yi muku saukin Al’amarin, haka rayuwa take kowa da irin jaraban da ubangiji ke masa kuyi fatan Allah ya baku ikon ci, Ammar ya amsa da ameen.
Inna ta mike ta debu ruwan wanka a yar bahonta da tsage aka nane shi ta surka kafin ta kaima auta bayi, sai da ta taimaka mata kafin ta kaita bayi tafito ta barta nan ta dauraye jikinta, don ruwan da dumi sosai ya gasa mata jiki kuma ta samu dan karfi, bayan ya fito inna tasake sama Ammar ruwan ta kaimishi shima wankan yayi, bayan yafitoa wanka suka shafa mai dake lokacin da mina ne, a kwai dan sanyi kadan.
Malam ne ya hau kekensa yaje can kauyen da gabansu anan ake samu shago, yasayo musu suga, yadawo inna laure ta musu surki mai dumi sosai, don ya ware musu hanji, abinci ta dauko musu dambu tayi daman, kuma ta danyi da yawa, san nan Malam ya karamusu da nashi, aiko sunci danbun sosai don yunwa sukeji, sai da suka gama cin abincin, san nan sukayi godiya ga Allah da ya kubutar dasu, san nan Ammar ya juyo ya gode ma Malam, cikin kulawa malam yace karkada mu ni domin Allah na muku, ita rayuwa bakan wa zai tai make ka nan gaba, kuma dukiya da dan mitum, da dabba ba a musu keta, ku kara gode ma Allah ammar sai da yaji kwalla, asai ana samun irin wayan nan mutane a zamanin yanzu, Hamdalah yasakeyi ga Allah da ya ciyar dasu.
Inna laure ta gyara daya dakin nan dama da kyausa, in sunyi baki anan suke kwana, ta kwantar da yar katifar bonun da ke dakun tayi shinfidi akan gado, inna laure kenan duk da acikin kauye suke tsohuwar akwai tsabta, komai nata tsab2 gwanin burgewa, ga kamala da kyautawa.
Malam yace ga daki an gyara zamu kwana da kai inna laure kuma sai su kwana da kan warka, kafin in Allah ya kaimu waye wan gari, sai kubamu tarihin ku da abunda ya

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts