🐾🐾 Raheenat🐾🐾k
©Rash Kardam💃🏻👈🏻
9⃣5⃣-9⃣6⃣
Ko da su ka fito godiya ga Allah sukayi suka gabatar da kansu tabbas duk wanda yaga jameela to yaga heenat ko da suka gama su Abba suka fito suka mika godiyarsu ga Allah da ya hada heenat da iyayenta daga nan aka soma dibar abinci bayan aci ansha aka watse ciki da farin ciki, haka su heenat suka dawo gida ko da suka koma side dinsu wanka tayi tayi sallah, sanna sukaje babban falo inda kowa yake aka soma cin abinci cokali daya heenat ta kai bakinta nan taji zuciyarta ya suma tashi dan haka ruwan zafi kawai ta sha ko da dad dinta da su Abba suka tambayeta tace bakomai, haka sukayi hira adaddafe takoma dakinsu nan zazzabi ya rufe ta hankalin MY ya tashi matuka kasa mata wani abu yayi arude ya kira wayar cikin gida aiko A A ne ya dauka nan ya sanar amasa heenat bata jin dadi a rude suda su abba suka shigo likita ya kira bai dade ba ya zo ya dan dubata da tambayoyi, nan ya dauki fitsarin ta yace bari yaje lab komaiye zai dawo ya sanar musu allura ya mata tasamu bacci kafin ya tafi MY tagumi ya zuba ya sata agaba yana kallonta, ko da likita ya auna gwajin farko sakamako ya gwada ta na dauke da ciki wata biyu da kwanaki cikin murna ya kira A A yasanar masa duka sunyi murna, haka suka kwana washe gari likita yazo ya bata yan shawar wari, haka rayuwa mai dadi sukayi a yola ga soyayyan da suke ba da MY abun ba acewa komai saida sukayi sati uku kafin A A ya daukar musu jirgin da zai kawo su Bauchi ko da suka iso Bauchi daman yana da gida akarin dan haka gidanshi ya sauka, haka ya bar duk abunda zaiyi ya yi sati guda ko da ya tashi tafiya, Ya dauki takardun alkawarin da yayi ya mika ma Abba, shi kuma yace ba zai karba don allah yayi sai da AA yayi ta rokonsa kafin ya karba ya kuma rokeshi da ya ya rubuta takardan barin aiki sai ya dawo sucigaba da kasuwanci, ya debi kudi masu yawa ya ba ma H Maryam da Murja ya dauki duk dukiyarsa yayi signed kancewa ya mallaka ma heenat ya debi wasu masu yawa ya ba ma Suwaiba da company biyu, haka suka rabu cikin farinciki, akan duk karshen wata su heenat zasu na zua gaida su, haka gidan Alhaji Muhammad Dalhat ya kasance cikin farin ciki.
Ina lbr Sadde tun bayan barinta bauchi duka shirya suka je gun boka ko da sukaje suka tarar da boka bayida lfy inta kaice muku kafin su bar gun ya mutu gashi mutuwar wulakanci da kaskanci haka suka baro kauye batare da tayi nadama ba, bayan sun dawo suka sake daukar hanyan katsina gun wani boka a hanya sukayi hatsari yanzu haka kafar Sadde an yake ta hannunta kuma ya bar amfani sai a keken gura gu ake turata Karema kuwa an sheka lahira, sai dai fatan Allah ya yafe mana kura kuren mu na amsa da Ameen
Kwanaki sunja yau cikin H Maryam ya cika wata tara gashi ta tashi da wani matsana cin ciwon baya gani halin da take ciki yasa su heenat suka kaita asibiti cikin ikon Allah suna zuwa basu dade ba ta zan kado kyawawan yaranta biyu mace da na miji masu kama da Abba gasu kyawawa, bayan an gyarata suka dawo gida,
Haka gidan ya cika makil da yan gaisuwa lokacin cikin heenat ma ya fito su Aysha ma kulum sai ta zo, haka sukayi ta shirin suna, sai da ana gobe suna Aimana ta zo gida ya hadu gasu cikin farin ciki, ranan da Aimana tazo Ranan su H Jameela da Suwaiba suka zo AA Yola ba karamin barin kudi yayi ba baran ma da yaji marikiyar yarsa, haka sukayita aiki har washegari inda yaran suna, namiji aka samasa Muhammadul Akbar, macen kuwa aka samata AmatulRasheed, haka akayini gashi duk dan gin da suka zo sai an gwada musu iyayen heenat yakumbo mata zo ganin iyayen heenat bakaramin girgizatayi ba don tayi na damar abunda tamata daman duk lokacin da heenat ta samu manemi ita take turawa a fada musu yar tsuntuwane, kafin su ya kumbo su bar bauchi saida tanimi yafiyar heenat da maryam, haka aka watse a taro cikin farin ciki, rayuwa mai dadi sukeyi in kaje gidan Abba sai abun ya burgek
Friday, 3 March 2017
Home »
» RAHEENAT 95-96
RAHEENAT 95-96
Popular Posts
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(AUGUST 2016)* ...
-
MOTAR KWADAYI RASH KARDAM Duk launin kalan idonta, sun canza izuwa ja. Hannu tasa a tsakanin cinyanta tana mammatsewa,Bad Boy yana ga...
-
AMANA TA CE By ©Rash Kardam 1 Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassa...
-
🐾🐾Raheenat🐾🐾 1 Yarinya ce yar kimanin shekara 12 ta yanko a guje ta fada jikin Dad...
-
MOTAR KWADAYI By Rash Kardam 21-25 Jan motar yayi, suka bar cikin Silver Sand Hotel, bai zarce da su ko ina ba, sai gid...
-
BAZATA By ©Rash Kardam 1 Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan l...
-
[6/5/6:30pm] 🌲RASH KARDAM🌲🌲 & 🎋SADEEY S ADAM🎋 ...
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(JULY 2016)* ...
0 comments:
Post a Comment