🐾🐾 Raheenat🐾🐾
Rash Kardam💃🏻👈🏻
6⃣3⃣-6⃣4⃣
Ya ce tsaya, sai da ta dan razana, gira ya daga mata, washin kice koko? Yau naga kin caza, murmushi tayi kafin ta sa abinci a plate da kanta tayi ta basa har ya koshi, duk tana halkance da shi, tun daga ran da MY yaci abunci, ko mai ya canza don yanzu ko gidan su ya daina zuwa sai yanda Sadde tayi dashi, aiki ma sai ta bashi izinin fita.
Aban garen Amarya yau sun iso bauchi duk wani shirin da ya kamata ayi ayi sai tsumata suke bana wasa ba, yau aure saura kwana 7 aka kawo lefe yawanci a dinke suke gaskiya Sani ya zuba kudi ba kadan ba, don sate biyu ya mata amma duk suncika saida suka hada da wani hadadun jakukuna masu kyau, aka sa sauran kayan aciki, Aiman tazo lokacin tana da shigan karamin ciki, Aysha gida ta dawi sai angama hidimar biki kafin ta koma duk inda ka zaga Amare suke ta hidima, abun gwanin burgewa, h maryam tayi murna sosai yanda Sani ya fidata kunya, tayi fatan Alkairi, ko ina ka zaga a yan uwa zancen kayan Heenat akeyi.
Aban garen h Murja ko tunda taga kwana biyu danta bai zo ba ta shirya har gidan sukaje, ko da tashigo gidan, karo tayi da danta yana ta wankin kayan Sadde harda su under wears dinta da su pant, ido ta zaro mai zan gani, Yasir kai kake wanke kayar matar ka, tafa hannu ta fara tana salati, daga bangare daya taji ance sai me in ya wanke kayan na, ku tsofin nan kun faye sa ido wlh mai ma ya kawo ki gidan mu tdohuwar bansa Sadde ta inda take shiga batanan take fita ba, ran H Murja in yayi dubu ya baci daga hannun tayi zata wanke ta da mari, kafin ta iso taji saukar ruwa ajikinta, ko da taduba taga ruwan dati yayi baki Sadde ta sheka mata, shiko mu MY yana tsaye ya kasa komai ko dayake zuciyarsa na kuna amma ya kasa aikata komai, haka H Murja ta bar gidan tana kuka sosai. Ko da ta isa gida dakinta tashiga tasamu su Aisha da Aimana kuka take sosai sai da kuka ta sosai kafin ta basu lbr ran Aysha in yayi dubu ya baci suka mike sai gidan ko da suka shiga lokacin sadde na kan white chairs shi kuma na wanki, mikewa tayi tace kunzo ra ma matane, na su ka fara zaginta aiko san da ta dauko tabisu da gudu suka fita, ko da suka koma gida sun jin jina abun, sunyi mamakin yanda bros ko ya dau mataki, h Murja ta sanar da Abba komai ransa ya baci, ya kira MY amma bai daga ba. Tun daga lokacin bai sake kiransa ba.
Murna gun yan uwa da abokan aziki ba a magana gobe take Auren Heenat da Sabi bayan an idar da Sallah la”asar, Abba ya kira MY yayi sa’a ko likacin na office, ya daga sai da ya masa fada sosai kafin yace yazo gida ya samesa, ko dayam ma da yaraso daga aiki ya shigi gida nan ya ga jama’ah acike duk ya manta ma me ke.faruwa ko da ya ajiye motarsa ya nufo shiga falo ya na sauri don ya samu karin baya ni, ” heenat ke ta sauri zata kai ma Aysha phone dinta suna zaune a garden, bata ankara ba taji tayi karo da mutum, tayi taga taga zata fadi ya tarota, fiskanta ya zuba ma ido tayi kyau sosai ga, ya kai kallonsa ga hannunta tasha lalle baki da adon ja tayi matukar kyau gashi ta kara kiba, ga wani kamshin da ke fita daga jikinta, baisan lokacin da ya rungumeta ba, jikinta ya dau bari tayi tayi ta kace kanta ta kasa, can dabara ta fado mata, cizo ta gantsara masa a fuska wanda yasa yayi saurin sakinta da gudu ta wuce shi tayi garden tana haki, har sai da Aysha ta tambayeta lfy tace bakomai gudu tayi, gefe ta koma tasoma tunani kala2 wai me bros ke nufi da zai run gumeta, kuma ta lura tun bayau ba yake nuna mata wasu abubuwa daban daban, rasa amsa tayi kawai sai ta share.
Shiko ko da ya shiga gun Abba su ka gaisa kansa akasa Abba ya masa fada sosai, ya kuma gane asiri akayi masa nan yace, Muhammadu kana yawan Adu’ah kuwa? Kana Azkar din tsarin jiki kuwa? Shiru yayi kafin ya tuna rabonsa da yayi azkar din tsari
Friday, 3 March 2017
Home »
» RAHEENAT 63-64
RAHEENAT 63-64
Popular Posts
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(AUGUST 2016)* ...
-
MOTAR KWADAYI RASH KARDAM Duk launin kalan idonta, sun canza izuwa ja. Hannu tasa a tsakanin cinyanta tana mammatsewa,Bad Boy yana ga...
-
AMANA TA CE By ©Rash Kardam 1 Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassa...
-
🐾🐾Raheenat🐾🐾 1 Yarinya ce yar kimanin shekara 12 ta yanko a guje ta fada jikin Dad...
-
MOTAR KWADAYI By Rash Kardam 21-25 Jan motar yayi, suka bar cikin Silver Sand Hotel, bai zarce da su ko ina ba, sai gid...
-
BAZATA By ©Rash Kardam 1 Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan l...
-
[6/5/6:30pm] 🌲RASH KARDAM🌲🌲 & 🎋SADEEY S ADAM🎋 ...
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(JULY 2016)* ...
0 comments:
Post a Comment