New Post

Wednesday, 1 March 2017

RAHEENAT PAGE 3

🐾🐾Raheenat🐾🐾


3⃣ Haka H Maryam take hakuri bata nuna damuwanta kasancewan wanda take zama dominshi bai daga hankaliba yai lallashinta da yakeyi takara hakuri kuma rabobta na nan zuwa ba dadewa haka zai ta kwantar mata da hankali ya na nuna mata haihuwa daga Allah ne fatansa shima bai wuce ya ganta da danta ba hakan rayuwansu ya cigaba komai na tafiya har lokacin Aymana tayi wayo sosai tana son H maryam itama tana ji da ita hakan ba karamin dadi yakeyi wa Alhaji ba yanda take nuna kulaarta ga diyarsa. A haka har Allah yabata diyarta Raheenat wanda suke nuna mata tsan tsan so da kulawa ga yarinyan da basira gata da shiga rai duk wanda ya ganta sai ya ji ta burgeshi gata da wayo sosai sai
Kwanaki su ja lokacin Heenat ta girma sosai lokacin shekaranta 12 amma in ka ganta ka dauka ta kai shekara 15 don lokacin tana Jss2 yayin da Ayman take da shekara 15 tana jss3 a makarantan su wato dolphin Maria makaranta da yamsa sunansa Aysha ma anan take karatu tana SSS2 yayin da M Y kuma yana India inda yake Karantan Medicine a can ban garen islamiya kuma su Heenat suna Abu Huraira da ke cikin G R A ya ran gasu da kokari Musamman Heenat ita take daukar musu 1st position a boko da islamiya Aymana ma da tata kokarin Aysha ce dai bata mai da hankalinta ga karatu
Ta bangare hajiya marya komai na tafiya mata dai dai matsalan H maryam bai wuce yanda H Murja ke nuna tsana ma Heenat va karara ko side dinta tayi guri Aymana sai kinga tafito tana kuka ta korota ko ta rankwasheta Aysha ma ba tayar baya ba don ta tsaneta ita kullum da kalar tata mugunta ahaka H maryam taki fada ma Alhaji abunda suke ma heenat wanda ko in a gabansa ne h murja bata nunawa karara sai a bayan idonshi don haka yasa maryam take jan Heenat su zauna a daki tana koya mata karatun da a ka musu a makaranta

👇🏻👇🏻👇🏻

🐾Rash Kardam💃🏻👈🏻

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts