: AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
4
Ammar ya ma rasa ya zaiyi ga Auta numfashin ta na kokarin daukewa da sauri ya suguna akasa ya ajiyeta acikin tabo ga jini yana ta zuba daga hannunsa,
Gumus suka nufo su da sauri nan ya harba bindigan ya sake harba wa yaji bullet ya kare cikin jin haushi yace oh ya wurgar da bindigan akasa ya nufosu ko da yazo daman Ammar na ankare yana isowa suka fara kokuwa cikin ukon Allah karfin yazo ma Ammar ya wurga shi a wan nan ruwan, aiko dan uwan gumus na ganin haka dake yana haskasu da touch light, ga shi gumus nata fanjam aruwa dake shi bai iya ruwa ba, kuma ruwan da dan yawa, da sauri yayi gun ruwan ko ta kan su Ammar baibiba ya je gun dan uwansa don ceto rayuwansa,
Ammar na ganin haka ya dauki Auta yasa gudu sai da yayi nisa ga ruwa ya soma tsagaitawa, ya samu wani rumfa ya ajiyeta ya huta, basu dade sosaiba ya auta sai hawaye:'(:'(take tayi ko da ya laluba kafarta yaji ta kubura suntum, taba kafar dayayi har sai da tayi ihu haka ya dauketa suka cigaba da tafiya.
Su gumus ansha wuya da kyar aka ciro shi don har yasoma shan ruwa, yana dawo wa hayyacinsa yake tambayar mugum ina suke yace sungudu, mtssss bahaka nasoba nan yace naga abunda ya faru kar ka sheke zuwa lahira da wuri shiyasa na ciroka kai kajimin wayan nan sai kace mutuwar nima izini takeyi, mikewa sukayi gumus ya karbi wayar mugum don nasa ruwa ya bata, baba sani ya kira ya tambayesu suna ina yace yanzu zasu bar gidan Alhaji kenan sukace gasu zuwa.
ko da suka isa nan suka samu baba isiya da sani sun daure sale mai gadi da musa, don daman sunyi akan zasu daure su sabida ace barayi ne suka zo, hakan sukayi, ko da su gumus suka iso nan sukaga abunda ke faruwa dariya sukayi sosai sukace Alhaji baku da dama,
Baba sani yace ya ina fatan kun sheke su cikin sauri gumus yace ai har gawan ma sai da muka yardasu inda ba mai gani, nan kawu isiya yace aikin ku na kyau, gumus yayi murmushi yace oga sai kudin fa baba sani yace ina zuwa cikin gidan suka shiga dakin dad suka duba drawer nan suka ci karo da damin kudi sai dasukayi dariya sosai kafin suka diba nan suka fito falo, baba sani yazo cikin izgilaci yace su Al-hassan yau an sheka kiyama to ina naira kai dan taurin kai yau zamu facaka da dukiyar da kake ta kama dashi, yana zuwa kan hajiya sai da ya shureta da kafa, ke kuma yar iyeye yau munyi maganinki da yar da kuke so, harda dauko bare wanda bakusan daga ina yake ba ku fifita shi akan mu gashi yau duka bakwa nan mun kuma samu dukiyar cikin ruwan sanyi sai ya kece da dariya sosai, nan suka fita suka shiga mota suka tafi don suke su sallami su gumus.
®WHW®
Rash Kardam
Friday, 17 March 2017
Home »
» AMANA TA CE 4
AMANA TA CE 4
Popular Posts
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(AUGUST 2016)* ...
-
MOTAR KWADAYI RASH KARDAM Duk launin kalan idonta, sun canza izuwa ja. Hannu tasa a tsakanin cinyanta tana mammatsewa,Bad Boy yana ga...
-
AMANA TA CE By ©Rash Kardam 1 Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassa...
-
🐾🐾Raheenat🐾🐾 1 Yarinya ce yar kimanin shekara 12 ta yanko a guje ta fada jikin Dad...
-
MOTAR KWADAYI By Rash Kardam 21-25 Jan motar yayi, suka bar cikin Silver Sand Hotel, bai zarce da su ko ina ba, sai gid...
-
BAZATA By ©Rash Kardam 1 Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan l...
-
[6/5/6:30pm] 🌲RASH KARDAM🌲🌲 & 🎋SADEEY S ADAM🎋 ...
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(JULY 2016)* ...
0 comments:
Post a Comment