🐾🐾 Raheenat🐾🐾
Rash Kardam💃🏻👈🏻
5⃣9⃣-6⃣0⃣
Ban garen Heenat kuwa kullum soyayya kara habaka yake tsakaninta Sani, yan uwanta sun sanshi, shima nasa sun santa don haka Aunty mardy ta yanke shawaran ranan Sati zasu gombe daga gombe kuma sai su wuce bauchi, din gabatar da Sani ma iyayen Heenat daga nan sai ayi maganan Aure, wan abu ba karamin dadi yayi ma Heenat da Sani ba nan suka fara murna sosai shirye shirye sujeyi sosai na zuwa gombe, Sani ya sanar da iyayens hajiyarsa tayi murna soi sai, ranan Alhamis sai da sukaye sukayi shoping sosai suka sayi tsaraba ma yan uwa, ranan Alhamis din da yamma sosai sani yazo sukayi sallama da Heenat don ran lahadi zai je gombe ya same su daga nan sai su wuce bauchi, sun danyi soyayyarsu kafin sukayi sallama, kamar kar su rabu da juna,
Ranan jumma’ah da safe sophia taje school an musu hutu zango karatu nabiyu, tana dawowa suka yi wanka, suka dau hanyar gobe, heenat murna ba 2 sabida zataje taga Aimana ta sun kwana biyu basu ga juna ba, gudu sukayi sosai, sai bayan isha suka isa gombe, sallolin su suka gabatar, kafin suka ci Abinci Hajiya kakan Heenat tayi murna da ganin jikarta, hajiya tasa heenat d sophia suje su gaida ya kumbo ki shiyar hajiya suka shiga, sai wani harare takeyi Heenat ta gaidata ko amsawar arziki bata mata ba, sophia ta gaida ta ba laifi ta dan sake ta amsa, kafin ta juya tayi uwar daki, Alhaji S Belo ya murna da ganin jikar sa, nan yayi ta tsokanarta kafin sukayi sallama ya musu saida safe, heenat abu daya ke damunta wanda tun tana yarinya duk lokacin da tazo yakumbo in banda zagi da hantara ba abunda ke rabasu, abun na damunta, da wan nan tunanin bacci ya dauke ta, ko da gari ya waye bayan sunyi sallah taje ta gaida Hajiya da Aunty Mardy, kafin taje ta gaida Alhaji da yakumbo, ta da dawo ta gyara daki aka kawo musu abun karyawa suka karya, wanka tayi wuraren karfe goma, tashirya ita da sophia zasu je gidan Aiman da ke federal lawcost, kwaliya ta yi na burgewa, a napep suka shiga basu sha wahala ba suka isa gidan Aiman tayi murna da gudu ta rungume heenat, kafin suka zauna ruwa ta kawo musu suka sha, daki suka koma nan aka fara hiran yaushe rabo, bayan sun sha hiransu, kafin ta kai musu abinci dinin suka ci sannan, ta ja Heenat suka zaga gidan ba laifi ko ina yayi kyau su Abba sunyi kokari don ba kara min kudi suka kashe mata ba,sallah azahar sukayi suka sake zama hira suka cigaba dayi nan Heenat ta ba ma Aimana lbr rabuwarta da Mukhtar da haduwar ta da Sani, da kuma gobe zai zo su wuce bauchi a gobe, Aiman tayi murna sosai jin sis dinta zatayi Aure,amma bataso ta tafi gobeba, Heenat tace zan dawo don sai mun dawo gombe, kafin mu koma kaduna, haka sukayi ni cikin farin ciki sai yamma Jabeer ya dawo daga office yayi murna da ganin su bayan ya huta suka gaisa, sukayi ta hira sai magriba ya suka maidasu gida harda Aimana ta shiga suka gaisa da mutanen gida, kafin suka tafi, haka suka kwana washe gari suka tashi da shirye shir tarban Sani, girki a kamasa sosai, kafin tayi wanka ta shirya cikin lafiyayen less dinta Brown da ratsin milk tayi kyau sosai, ko da ya iso bai samu matsala ba, ya xo unguwar dakin Uncle KB kanin su Aunty mardy aka masa masauki, sai da yayi sallah kafi a ka kawo masa, abinci, san nan Heenat tasgigo kallon ta ya tsayi baki sake, don tayi kyau sosai, tana isowa daf dashi tayi farrr da ido sannan tace, Ur wlc Dear, murmushi yayi kafin yace, My Heenat kiyi kyau fiye da kullum, murmushi tayi tace kafini, yace aa, kafin tace ya hanya? Yace lfylau, sun danyi hira kafin ta masa rakiya, zuwa cikin gida dakin hajiya ya gaidata, sai da ta tsokanesu kafin tace ta kaishi ya gaida Alhaji, ya gaida alhaji suka danyi hira ya masa Alkairi kafin ta kaishi dakin yakumbo, sai wani kallon baza take musu a wulakance ta amsa sama2 kafin ya ajiye mata 5k
Friday, 3 March 2017
Home »
» RAHEENAT 59-60
RAHEENAT 59-60
Popular Posts
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(AUGUST 2016)* ...
-
MOTAR KWADAYI RASH KARDAM Duk launin kalan idonta, sun canza izuwa ja. Hannu tasa a tsakanin cinyanta tana mammatsewa,Bad Boy yana ga...
-
AMANA TA CE By ©Rash Kardam 1 Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassa...
-
🐾🐾Raheenat🐾🐾 1 Yarinya ce yar kimanin shekara 12 ta yanko a guje ta fada jikin Dad...
-
MOTAR KWADAYI By Rash Kardam 21-25 Jan motar yayi, suka bar cikin Silver Sand Hotel, bai zarce da su ko ina ba, sai gid...
-
BAZATA By ©Rash Kardam 1 Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan l...
-
[6/5/6:30pm] 🌲RASH KARDAM🌲🌲 & 🎋SADEEY S ADAM🎋 ...
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(JULY 2016)* ...
0 comments:
Post a Comment