: AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
11
Suna hira da Malam har suka dawo gida,….
da daddare basu wani hiraba sanadin hadarin da ya hadu, daki suka shiga suka kwanta ba a dade ba ruwa ya sauko sosai, haka aka kwana ana ruwa, da asuba malam sukaje sukayi sallah, inna da zainab sukayi acikin gd, haka suka yi koko da kosai shuka karya, bayan sun karya sukayi wanka,..
Bayan sun kan mala komai lokacin gari ya dan sha, kafin suka fito gidin biyar kofar gdn kasancewar garin ba mutane da yawa, don gida daya na da rata tsakaninsa da wani gd,..
bayan sun zauna malam ya bukaci ammar da ya cigaba da lbr sa…
Ammar ya cigaba da cewa bayan na mai dugri mun dau hanyar kaduna, sai dare muka iso kaduna don driver ma na gudu sosai, ko da muka isa garin kaduna, mun sauka a kawo, nan kowa ya fita don ya tafi girin da yazo, ina ina tsaye ni da wani a gefena sai ga mai taxi yazo, yana fadin Abuja Road Magajin, nan mutumin yace nan zaije, take nima na shiga taxi din munyi tafiya mai nisa ina kale2 don yanayin garin yayi kyau sosai, ahaka dai muka iso magajin gari nan mutum ya sauka nima na sauka, ko da na fito na rasa inda zani, hakan yasa nazo masallaci nayi sallah kafin na bar masallaci don na fara jin bacci, kofar wani shago na samu na kwanta don na gaji sosai, kwanana 3 a gurin ganin kar mutanen gurin su zargeni yasa na dau ledata na fara tafiya, nayi nisa sosai kafin naga wani guri mai gine2 na sama ga jama a sosai, daga nesa naga an rubuta “CHE CHENIA MARKET” da manyan harufa, nan nasamu na kutsa, kusa da shagon mai takalma na zauna.
na kwana biyu ina zama a gun har na dawo dan aika a gun, abinda na lura a kwai wani shagon takalma da less da material, saman shagon an rubuta “ZAINAB FASHION DESIGN” a bunda na lura akwai wani alhajin da ke yawan zuwa da yarsa wata kyakyawa na karshe, suna sayan kaya ne ko mai sukeyi ban sani ba, tun da na kalli yarinya naji ta kwanta min a rai ina sonta da kanwa, hakan yasa duk randa zasu zo in sun sai kaya zanje in dauka musu in gaida alhajin ko da babanta zai bani kudi bana karba, sai yayi da gske nake karba, hakan ya mana masa dadi, har yasoma tambayata inane unguwan mu, nan nasoma hawaye ganin haka Alhaji ya kama hannuna muka nufi motarsa, munyi tafiya mai nisan gske, har na fara tsoro ko dan yankan kaine, nan nakama adu’ah neman tsari, mun isa wani unguwan da ba mutane sosai, sai da mukazo kofar wani katon gd mai kyau horn yayi aka bude kofar, gate din, gd ba laifi kam yayi kyau sosai.
Munshiga cikin gd mata kyakyawan mace ta fito da murnanta, tana sannu da zuwa Alhaji, nan ta kalleni, tace Abban Auta ina kasamo wan nan yaro mai kyau haka, Alhaji yace bari mu zauna tukun.
®WHW®
Rash Kardam
Friday, 17 March 2017
Home »
» AMANA TA CE 11
AMANA TA CE 11
Popular Posts
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(AUGUST 2016)* ...
-
MOTAR KWADAYI RASH KARDAM Duk launin kalan idonta, sun canza izuwa ja. Hannu tasa a tsakanin cinyanta tana mammatsewa,Bad Boy yana ga...
-
AMANA TA CE By ©Rash Kardam 1 Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassa...
-
🐾🐾Raheenat🐾🐾 1 Yarinya ce yar kimanin shekara 12 ta yanko a guje ta fada jikin Dad...
-
MOTAR KWADAYI By Rash Kardam 21-25 Jan motar yayi, suka bar cikin Silver Sand Hotel, bai zarce da su ko ina ba, sai gid...
-
BAZATA By ©Rash Kardam 1 Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan l...
-
[6/5/6:30pm] 🌲RASH KARDAM🌲🌲 & 🎋SADEEY S ADAM🎋 ...
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(JULY 2016)* ...
?
ReplyDelete