New Post

Wednesday, 1 March 2017

BAZATA PAGE 12

BAZATA 
                By
©Rash Kardam 
   12                   
Dan iska ma cuci, ka kawo ni nan ka cuce nine, kansa ya dafe nan take ya fara jin haushin kansa,Jiddah ganin bai fita ba yasa tayi kokarin mikewa wani zafi taji kirjinta da kanta na mata, ko da ta duba gefenta, sai a lokacin taga ruwanda aka sa mata, ko da ta kalli kafarta bendeji ta ga ansamata, nan take ta saki kuka, jin kukanta na tsuma zucoyar sa ba zai iya sauraron kukan ya mike zai fita sai da ya kai kofa ya jiyo ya kalleta idonshi ya kawo kwalla ga wani Sonta da ya ke ji, kirjinsa sai harbawa yakeyi da sauri2 bude kofar yayi dai2 nan ya ga Marsal Sophia da Amarya Suhana sun nufo dakin, kallo daya suka masa, suka gane yana cikin damuwa, gai sawa sukayi suka tambayesa ya me jiki,? Yace da sauki don anbasu lbr irin taimakon da ya mata harda jininasa da ya bayar, dakin suma shig.
Dr Ghali yafita harabà asibitin, ya nufi gun ajiye motoci, ya shiga motarsa ya bar Asibitin, don zuciyarsa na masa wani irin suya, gudu yayi sosai kafin ya isa gida dakinsa ya shiga ya kulle kansa, kan gado ya fada yana juyi ga zuciyarsa da ke masa wani irin suya, yace ni Ghali na cuci kaina, yarinyar da na tsana ita nake matukar kauna gashi kuma dai2 itakuma take tsananin tsanata, ya zanyi da zuciyata kwalla ne  ya cika idonsa, ya kudiri aniyar sai ya wanke kansa, Hauwa’u na ina matukar Kaunan ki My Jiddah, pla kisoni koda rabin cokali, i’m deeply in love with you My Jiddah, you hrt, my Only, kukane ya kwace masa, tabbas yayi nadama sosai, wanda ni “Rash na saida Ghali yana matukar son Jiddah’ yace Jiddah sai na koyar dake yanda zaki So  ni haka yayi ta sanbatu shi kadai har magriba tayi yaje yayi Sallah, sai Isha’i ya dawo shirin kwanciya yayi, yana Adu’ar Allah bama jiddah lfy.
Marsal da Sophia suka tura kofar dakin suka shiga, ganin tana kuka yasa suka karasa da gudu, sannu jiddah, ya jikin kuka ta kara saki ta fada jikinsu tana cewa, Ya tafi bana son ganinsa na tsane sa dan iskane, mai satan yan mata, kuka take sosai, Suhana tace waye haka, Jiddah tace Dr Ghali, Marsal tace ai bayanan ya fita, sai lokacin ta bude idonta taga baya nan wani Ajiyan hrt ta sauke, Sophia tace yanzu ki bar zance nan ya jiki tace da sauki, nan suka kira su Abba suka sanar musu Abba yace gashi zuwa yanzu, wayar Feenat ya kira tana gun aiki itama yace taje T.H Emergency ta same su, tace lfy yace Jiddah ce tayi Accident, cikin rudewa tace Yasalam!!! Ajiye file din da take cikawa tayi, kafin ta je ta nimi permission ta fita, gudu tayi kafin ta isa asibiti, ko da ta isa wayar Sophia ta kira ta zo ta kaita room din, rungume sis dinta tayi, ido ya ciko da kwalla, tace sannu sis Allah ya kare na gaba, su Marsal suka amsa da Ameen, Abba sun zo haka suka zauna suna kula da ita, sai magriba su marsal suka tafi tun daga wan nan rana, Jiddah take samun kulawa mai kyau, kullum sai Dr Ghali ya zo dubata batare da saninta ba, kuma ya sai kaya ya bama su marsal da Sophia sukawo, amma vasu taba cewa shi bane, don sanin halinta, satin jiddah daya a asibiti aka sallameta, tayi kyau ta murmuri, sabida samun hutu ba fita rana bare zurga zurga2 sai yan tabon da suka rage mata, haka suka dawo gida kulum feenat ke da wainiya da yar’uwa ta, haka harta warke sosai, ta fara fita aiki, sai yan tabon da basu gama baceawa ba, shima tana shafa musu zuma, tayi kyau sosai fiye da da. Yanzu komai han kali kwance takeyi don harta manta da wani wai shi Ghali, a sabgarta.
Ghali in banda wutar son Jiddah ba abunda ya dame shi, kulum ka ganshi yana zaune shi ka dai, sai dai yayita smile, yana tuna jidda, a rin wanan tunanin ranan Samar yazo ya samesa, ya jima a zaune cikin office bai san ya isoba sai murmushi yakeyi sai da Dr Samar ya bugi table kafin ya dawo hayya cinsa, yace ghali wlh kabi a hankali, don sam yarinyan nan bata san kana yi ba, hasali haushinka take ji g

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts