🐾🐾 Raheenat🐾🐾
Rash Kardam💃🏻👈🏻
8⃣1⃣-8⃣2⃣
Cikin baka ramin daga ma suwaiba hankali yayi ba, tunda ga wan nan rana ta kudiri aniyar zubar da cikin ko ta wani hali,.
Hajiya ko kamar ta san mai suwaib take shiryawa, tattari kayanta ta dawo gidan A A Yola, kula na musamma take ba ma Jameela, abinci ma ba kowane take ci ba ko da zata ce ta ga abu tana so to bara ta bari taci wanda ta ganinba don sai dai ta mata wani, hakan ya dami suwaiba har take zargin ko hajia ta gane tane, ka warta, Asmart Adam takira ta sanar mata mai ke faruwa, Asmart tace kar ki zubar da cikin nan yanzu za’a gane abu tasha kuma za’a iya tuhumanki, ki bari ta haihu ko a asibiti ko a gida ni zan san yanda za’ayi a dauke jaririn zai a yar dashi, tace haka za’ayi.
Kwana ki sun ja watani sun tafi yau cikin jamila, ya kai wata tara, in kaga cikin ka dauka twins zata haifa yayi girma sosai, kulawa kuwa guri Hajia da Suwaiba ba a magana kai ka rantse da zuciya daya takeyi, in tana kula da Jameela sai ka rasa tsakanin ita da hajiya da Alhaji wa yafi wani son cikin, duk wanda yaga yanda takeyi ba zai kawo da mungun nufi a zuciuarta ba, yau take jumma’ah tun da da rana Jameela take jin ciwon mara, haka tayita daurewa har zuwa dare, can tsakar dare ciwon ya tsananta, nan ta sanar da hajiya, hajiya ta kira suwaiba, ko da ta sai da mata haibuwane, nan tace bari ta dau ko key din motarta su tafi asibiti hajia tace driver fa tace yana bacci kyaleshi kawai, hajia tace ko za a fada ma Ahmad ne suwaiba tace yanzu in mun fada masa hankalinsa zai tashi muje kawai, ko da suwaiba ta shiga daki sai da takira Asmart Adam ta fada mata tace karki damu yanzu kuje asibitin, tace to, tace kar ki bari kuje asalin asibitin ku kuje wani tace ti ko da ta fito suka saka jameela a mota sukayi asibiti ana zuwa basu dade ba ta haihu, koda nurse suka gyarata, suka gyara baby, sauran suka fita nan akace suje su kawo kaya asa ma baby din, suwaiba tace yana mota, Suwaiba tace bara dauko ba, ko da suka kawo kaya aka sa ma baby take aka sallame su, duk yanda suka so su saci yarinya basu samu da ma ba haka suka hakura.
Ko da suka dawo gida tasa aka kira mata AA Yola nan ta saida masa Jameela ta haihu kar kuso kuga murna a gunsa, washe kari ya dawo, haka a kasoma shir shiryen suna, gashi kulum gidan da baki da ma yau ba jama’a sosai, subaiba ne sukayi waya da Asmart mai suka kitsa ni dai shewarsu naji, nan Suwaiba ta tafi dakin hajia hira sukeyi sosai, a gate kuwa masu gadin AA Yola, ne zaine bakin gate, sai wata mata da nikaf da doguwar riga, da goyo a bayanta tashigo, masu gadi suka tambayeta da ga ina tace ita yar uwar Jameela ce ta yola da zama, ganin matar oga basu kawo komaiba, suka barta ta shiga, ko da tasiga gidan side jamila tawuce bata ga kowa a falo ba, uwar daki ta nufa nan ta ciro abunda ke bayanta, asau tedy ta goya, ta wurgar, ko da ta leka, ta hango Jameela da alaman wanka zata shiga, amma digital camera ce a hanun ta yar karama, zuwa tayi ta ta daukar baby a photo, yarinya mai kyau mai kama uwart, kana ganinsu ka ga fulani asali, ko da ta gama daukata, tasa camera a sif, tashiga wanka, matar nan na ganin haka da sanda tazo ta dauki yar ta goyata, tafito ko da ta fito masu hadi basu zargeta ba tafita abunta, ko da tafita motar bauchi tashiga irin kananu motar nan take suka dau hanya, sai da sukayi tafiya mai nisa kafin har kusan takwas na dare kafin suka iso Bauchi, ko da ta iso bauchi hitel taje ta kama, yarinya yunwa ya soma damunta, don dai ma tana da hakuri ne, mafaran yara tasoyo a wasu shop da ke hotel din na cikin gari,nan ta ba ma yar yasha sosai, ksfin suka kwanta, ko da gari ya waye, bayan ta karya, fitowa tayi, ta tsari mai tazi yakaita tashar gombe, anan ta shiga mota, ko da su
Friday, 3 March 2017
Home »
» RAHEENAT 81-82
RAHEENAT 81-82
Popular Posts
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(AUGUST 2016)* ...
-
MOTAR KWADAYI RASH KARDAM Duk launin kalan idonta, sun canza izuwa ja. Hannu tasa a tsakanin cinyanta tana mammatsewa,Bad Boy yana ga...
-
AMANA TA CE By ©Rash Kardam 1 Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassa...
-
🐾🐾Raheenat🐾🐾 1 Yarinya ce yar kimanin shekara 12 ta yanko a guje ta fada jikin Dad...
-
MOTAR KWADAYI By Rash Kardam 21-25 Jan motar yayi, suka bar cikin Silver Sand Hotel, bai zarce da su ko ina ba, sai gid...
-
BAZATA By ©Rash Kardam 1 Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan l...
-
[6/5/6:30pm] 🌲RASH KARDAM🌲🌲 & 🎋SADEEY S ADAM🎋 ...
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(JULY 2016)* ...
0 comments:
Post a Comment