: AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
6
Motar suka shiga nan mutum min yace subada 1500 kudin mota sai a lokacin ya tuna basu da kokisi, innalinahi wa inna ilaihi raji’un abunda ya furta gashi sunyi nisa sosai, sun shiga jeji don sun bar cikin garin kaduna sosai, jiki ba kwari yace wa driver dan Allah ka tai make mu wlh fitowar gaggawa ne ya kama mu bakosisi ajikin mu, driver ya narko ashar yayi, aefa baka isaba zan dauko ku a bati ne ba ko sisi mai na tsada kuma niman kudi na fito, waya sani ko dan iska ne ma kai kasato musu yarinya inazaka da wannan yar gashi jikinta duk jini, kalala ta mata rayuwa, ko sayarta zakayi, nan take ran Ammar ya baci don tunda yake ba abundaya tsana kaman zargi ko kazafi, shi da ya tsani zina a rayuwansa mezaisa ya aikata cikin bacin rai yace kaii Malam ya isheka in har bazaka taimaka min ba karka min wan nan zaton, nan mutumin yace anyimaka kuma zata fita anan ba wlh sai kabani kudina, nan ran Ammar yakara baci wai shi dayake nima da guminsa ga kuma Zainab yar gata gabada baya wai yau sune a wulakance ga shi an kashe su Alhaji shikenan Zee sa ta dawo “MARAINIYA”nan take yaji hawaye:'(:'(:'( wasu na bin wasu, sai a lokacin ya kalli agogon hannusa mai kyau yace ma
driver bani da kudi amma ga agogona in zaka karba yafi karfin kudinka, driver yace nagani ko da ya karba yagani yasan zaiyi tsada dayawa nan yace to shikenan yanzu in kaiku saminaka ne ko zaku sauka anan tsabage bacin rai yace barin musauka anan, ya dauki Auta suka fita, gefen hanya ya kwantar da ita lokacin gari ya waye sosai, sai alokacin yaga kafarta ya kumbura sosai fa bakinta ma ya kumbura sosai, gashi yayi ja abunka da farar mace, gindin wata katuwar bishiya yaje ya shinfida fallen zani ya kwantar ta, ga yunwa yasoma damunsa ga hannusa yana masa zafi sosai, bayan ya kantarta, yasoma dube2 ko zaiga ruwa don yasha yakuma ji alwala.
Acikin garin kaduna kuma Alhaji Abubakar ko ince Inspector Abukar shiyatsa akan gawan su dad har akayi zana idarsu aka kaisu makwancinsu na gsky, kafin kace me lbr ya baza gari, yan uwan dad sun taru a gidan ko da Sadiya yar Baba sani taji lbr ba karamin girgita yayi ba baran da taji ance ba a ga Zee ba tashiga tashin hankali don suna shishiri sosai,
Inspector Abubakar daya koma gd ya tausaya ma yarsa bulkisu don kawar Autace sosai tayi kuka kuma nan ta dauki aniyar saita dau fansa akan duk wanda ya aikata abun, bayan kwana uku da rasuwan su Dad yan uwansa sukace su duk wanda yayi abun nam sun barshi da Allah, sirutu kala2 su ka rinkayi har saida Inspector Abubakar yaso ya ganesu, bilkisu kuwa ranan kwana na uku, tasami Abbanta akan ita ta canza ra’ayi daga kan Science courses, yanzu Law zata karanta don tazama barrister don ta nimo ma Kawarta Ameeniyar ta, hakkunta da cutar da ita da akayi, kuma tace Abba ni ajikina inajin Zee bata mutu ba ko ga yanayin statement din da aka samu kuma kaga ba aga Ammar ba nisan yana tare da ita kuma bazai cutarta ba da yardan Allah don yana da hali mai kyau, Inspector Abubakar yaji dadin maganar yarsa Bilisu wanda ake kita da futuhatul-khai, yamata Adu’an Alkairi da fatan nasara.
Su baba sani nan suka fara kiciniyan raba dukiyar dad har yaso su samu sabani da baba isiya akan wanda zai zauna a gidan dad da kyar Baba isiya ya hakura akan shi za a bashi motar dad babban ya rike.
Rayuwa kenan wai naka najikinka shiyake son ganin bayanka basa tunanin suma zasu mutu ba tsoron Allah wan nan wani irin zamani ne burin wasu mutanen su ci “Amana” yan uwa muji tsoron Allah musani Amana tana gefen siradi da Zumunci duk wanda ya karya daya aciki to yasan makomarsa, don ranan kiyama akwai wasu kugiyoyi a kasan gadan siradi duk wanda yaci amana ko ya bata zumunci ko da ya kusa karshen haye gadanne haka kugiyar zata finciko shi wasu kafin su isa duk sun yaga naman jik
Friday, 17 March 2017
Home »
» AMANA TA CE 6
AMANA TA CE 6
Popular Posts
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(AUGUST 2016)* ...
-
MOTAR KWADAYI RASH KARDAM Duk launin kalan idonta, sun canza izuwa ja. Hannu tasa a tsakanin cinyanta tana mammatsewa,Bad Boy yana ga...
-
AMANA TA CE By ©Rash Kardam 1 Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassa...
-
🐾🐾Raheenat🐾🐾 1 Yarinya ce yar kimanin shekara 12 ta yanko a guje ta fada jikin Dad...
-
MOTAR KWADAYI By Rash Kardam 21-25 Jan motar yayi, suka bar cikin Silver Sand Hotel, bai zarce da su ko ina ba, sai gid...
-
BAZATA By ©Rash Kardam 1 Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan l...
-
[6/5/6:30pm] 🌲RASH KARDAM🌲🌲 & 🎋SADEEY S ADAM🎋 ...
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(JULY 2016)* ...
0 comments:
Post a Comment