BAZATA
By
©Rash Kardam
5
Waye Dr Muhammad Ghali.
Muhammad Ghali asalin haifen bauchi ne, iyayensa fulali ne gaba da baya, Alhaji Muhammad shin mahaifin Ghali da Mahaifiyarsa hajiya Zakiyyatu dukkansu fulanine, Ghali shine babban dan Alhaji sai kanensa biyu mata Habiba d Ruky, sun taso cikin tarbiya mai kyau, tare da kulawar junansu da kaunar junasu, family ne mai dauke da farinciki sosai d sosai, ko ni kaina saida familyn suka burgeni, haka rayuwansu ke gudana cikin aminci, wan na shine asalin Dr Ghali.
Jidda ko bayan da tafito da ga wanka ta shafe jikinta da mayuka masu kamshi ta gyara jikinta, kananun kaya ta sa ta kwanta, ko da ta kanta taso ta dan samu bacci amma abu ya fassakar don bakin cikin abunda ya mata shi ya tsaya mata a rai, ta dau aniyar saita rama, da haka har sallan la’asar tayi tayi sallah, bayan ta idar ne ta fito falo gani Abbanta ya dawo yasa taje gunsa tasoma zuba masa shagwaba, suna cikin haka Hajiya Muslimah ta fito hannunta rike da kofi ruwan lemune aciki ta miko ma Abba ya sha, suka zauna falo, feenat ma ta fito cikin wankata na riga da skirt sun mata kyau sosai zuwa tayi ta zauna aka soma hira da ita, gaka sukayita hira har mangariba, kafin suka mike kowa yaje yayi sallah, haka rayuwansu ya cigaba da guda na cikin aminci duk wanda ka gani agidan na cikin farin ciki barin Abba da kulum ya kalli yan yaransa Mata da Allah ta basa sai ya gode ma Allah, sai fatan Allah ya kawo musu miji na gari, na amsa da Ameen.
Jidda ce sanye cikin shaddarta, purple colour ya matukar yi mata kyau sosai, tafe take ciki takunta mai daukan hankali ga duk wanda ya ganta, zua gun H Muslimag tayi ta rungumeta ta baya tace maa, tace ya aki autar Abba, tace ina son zan dan fita ne, zanje kasuwa inyi sayya tace to kar ki dade tace to nagode, ko da ta fita motarta tashiga tafiya tace cikin hankali tana jin wakar Aashiqui Hum Mar Jayenge. Tana matukar son wakokin Aashiqui sosai kalo daya zaka mata kasan tana cikin ni shadi, wayarta ne ya soma kara, ta daga taga Dr Suhana cikin murna ta dauka ta ce Amaryan next week ba kya laifi cikin murmushi Suhana tace, Sis an fitar da Ashoben fa kina gida ne in kawo miki tace,,,.. Ummmm bana nan na dan fita kasuwa amma ba dade wa zanyi ba tace right, sai kin dawo zanzo. Na sukayi sallama, ta shiga kasuwa sayyaya tayi sosai duk wani abunda ta san tana da bukata, wani abun burgewa komai ta sai ma kanta sai ta sai ma Sis feenat dinta don tana matukar ji da ita sosai, haka ta gama ta dawo gida, bata dade ba Suhana ta zo ta kawo mata anko din bikin gaskiya sunyi yau sosai, hira sukayi sosai kafin sukayi salama ta tafi, tun daga wan nan rana shirin bikin Dr Suhana sukeyi basa zama sosai sune can sune nan don sune kirjin biki. Sun tsara events din biki bazata yi wani bidi’ah ba, just Walima zatayi ran Friday bayan daurin Aure Sai Dinner da angwaye suka shirya da daddare bayan an dauko Amarya zasu wuce. Dinner komai ya tsaru yanda ya kamata sai jiran satin bikin da fatan kuma Allah ya kaimu na amsa da Ameen.
Wednesday, 1 March 2017
Home »
» BAZATA PAGE 5
BAZATA PAGE 5
Popular Posts
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(AUGUST 2016)* ...
-
MOTAR KWADAYI RASH KARDAM Duk launin kalan idonta, sun canza izuwa ja. Hannu tasa a tsakanin cinyanta tana mammatsewa,Bad Boy yana ga...
-
AMANA TA CE By ©Rash Kardam 1 Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassa...
-
🐾🐾Raheenat🐾🐾 1 Yarinya ce yar kimanin shekara 12 ta yanko a guje ta fada jikin Dad...
-
MOTAR KWADAYI By Rash Kardam 21-25 Jan motar yayi, suka bar cikin Silver Sand Hotel, bai zarce da su ko ina ba, sai gid...
-
BAZATA By ©Rash Kardam 1 Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan l...
-
[6/5/6:30pm] 🌲RASH KARDAM🌲🌲 & 🎋SADEEY S ADAM🎋 ...
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(JULY 2016)* ...
0 comments:
Post a Comment