New Post

Wednesday, 1 March 2017

BAZATA PAGE 11

BAZATA 
                By
©Rash Kardam 
11                     
A hankali ya tura kofar sai da ya tsaya kusan na minti biyar, ya zuba ma jiddah ido ko kyaftawa ba yayi, sophia ce ta fito da ga cikin toilet din pharmacy din, karaf suka hada ido da Ghali da sauri ya shigo da Sallamarsa, tana jin kamshin turarensa, ranta ya baci wani tsanarsa takeji yana ziyaran zuciyarta, bata dago tanajin suna gaisawa da sophia, can yacemata Dr Samar yazo nan kuwa tace aa ae yana office, ka duba office dinsa kuwa, cikin inda inda yasoma…..dama….uhumm….ae na dauka yazonan ne, sophia ta gama dagoshi, murmushi tayi, yace barinje na dubashi tace to, yana fita sukayi gamu da Marsal zata shigo pharmacy din, gaisawa sukayi sosai, ya wuce ta shigo, Sophia tace sis Marsal ya kk? Ya aiki tace lau, Marsal tace mai Dr Ghali yazo yi pharmacy? Sophia tace ban sani ba nima,na dai fito daga toilet na ganshi tsaye a kofa  tace nikam ina zargin wani abu, sai a lokacin Jiddah ta dago man yan ifanunta ta harari Matsal, Sophia tace, anya Dr ba son Jiddah yake ba, marsal tace na dade da tunanin haka, don ina hango tsananin kaunarta a idonsa, wani tsaki Jiddah tace dan Allah ku bar hadani da wannan dan iskan, Marsal tace ba zaki gane bane guy din ya hadu, ya na da qualities din da za ace kin so shi, sis hararanta tayi tafita ta bar musu pharmacy din, Sophia tace kyaleta zasu dai daita mu na mu ido dariya sukayi, haka sukayita aiki har aka tashi kowa ya nufi gida.
Kwanaki sun ja watanni sun tafi sofiya in banda tsana da kiyayyan Dr ghali ba abunda zaka gani a idonta, hakane ma yasa ta daina kula kowa, haka rayuwa tayi ta tafiya duk yanda Dr Ghali yaso suyi mutunci abun ya faskara, kulum Adu’ar shi ta yafe masa.
Yanzu duk wanda suke tare ko ba a fada ba sun san yana son Jidda sosai,amma yana wayancea sabida rashin hadin kanta da bai samu ba shine kulum zaman jikin window ko zai ga wucewar ya samu relief a zuciyarsa . Haka suka kasance cikin wan nan hali.
Jiddah ce tafito cikin shirin aiki sauri take ta makara sosai, ko da tashiga motarta  tayi2 motar taki tashi sam, ga feenat ta fita gun aiki a motarta Abba kuma baya nan shima, gida ta koma ta ajiye key din tafito tashiga a Keke Napep, tashiga tace masa Malam dan Allah kayi sauri na danyi late yace to gudu sukeyi sosai, sun iso dai dai kwanar da zai shigar da kai hanyan T.H sai jin kau…… Kau…. Keke Napep dinsu ya hadu da wani mota wanda sai da yayi sanadin fifowar jidda waje, kalo kayi ma napep din da kyar tayi aiki nan gaba, In banda salati ba abunda ke tashi agun ga jini sai kwarara yakeyi, dai2 nan Dr Ghali ya zo wuce ganin abunda ya faru yasa ya tsaya, yana dubawa yaga Jiddah ce nan take ya rikice, yana kiransunan ta yana hawaye pls Jiddah kar ki tafi ki barni ina tsanani bukatar ki, pls Jiddah dau karta yayi wasu suka taimaka masa da mai napep din su ka dauko shi, suka sasu a motarsa, gudu yayi sosai suka isa Emergency nan take Doctors sukayi caaa kansu sai kusan awa daya kafin wani likita ya fito, yace Dr muna son jini, za amata kari don ta zubar da jini sosai, Dr Ghali yace muje a duba nawa in yayi a dauka, cikin ikon Allah jinin su yazo daya. batare da bata lokaciba aka dau jininsa, aka samata, bayan angama treatment dinta aka kaita single room aka samata ruwa, Dr ta ghali ya zauna ya sata agaba ya zabga uban tagumi, sai da ta samu kusan awa daya kafin ta soma bude idon ta a hankali tana salati, taras ta sauke su kan Dr ta ghali, nan take tasaki wani kuka tacwa, dan isaka ka tafi bana son ganinka so kake ka cuceni ka kawo nan kansa ya dafe kansa.

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts