BAZATA
By
©Rash Kardam
21
Sai da sukayi kuka mai isar su, ghali ne yace Samar feenat ta kace dole in bar maka feenat, Samar yace no ka bi umarni iyayenka cikin muryan kuka ghali yace bana ki musu ba amma su tausaya mana Jiddah itace zabina itace rayuwata, sam ba zan iya zama da feenat a matsayin mata ba, bazan iya mata adalci ba, ina tsoron kar Allah ya kamani da laifin ban yima iyalina adalci, haka sukayi ta jimami, sai kusan 1:00 suka kwanta duk sun kasa bacci ko wanne da abunda yake sakawa a zuciyarsa.
Su Abba ko da su ka isa gd dakinsa yayi, feenat ma dakinta tayi, tana shiga sallah tayi ta fara kai kukan ta ma Ubangiji, tana rokon Allah ya kawo mata mafita, don ita ko kadan bata son gani Jiddah cikin tashin hankali,haka shafa ta kwanta bacci.
Su Jiddah haka ta kwanta, ko da gari ya waye misalin karfe goma aka sallame su, don jikinta da sauki daman firgicin da tashiga ne, haka suka dawo gd, ko da ta koma dakinta tayi ga gidan da yan biki, wanka tayi ta sha tea, ta zabga uban tagumi, feenat ne ta turo kofa ta shigo kallo daya tayi ma Jiddah idinta ya ciko da kwala:'(, sam jiddah bata san an shigo dakin ba, sai da feenat ta dafata san nan ta dawo hayyacinta, ganin feenat ne yasa tayi yaken da yafi kuka ciwo, feenat jiddah ki kwantar da hankalinki ghali na kine bazan iya zama da wanda kukeso ba, Jiddah ta girgiza mata kai alamar aa, jiddah tace sis ki bi Mijinki kiyi masa biyya kisani Allah ne ya jarabce ni sanadin kin bin umarnin mahaifina, nayi nadama kuma na gane kure na, nan kuka ya kwace mata, tace sis na hakura da ghalu, feenat tace aa ina sis ba zaiyuwa ba, ganin sunki sasanta kansu yasa feenat na kuka ta bar mata dakin, tana zuwa dakinta kuka tayi sosai, Jiddah kam duk ta rame yini daya, ta kuma fauwala ma Allah komai.
Dr ghali ko da gari ya waye sukayi sallah, kalo daya zaka musu kaga irin raman da sukayi, sai karfe 10:30 suka fito asibiti suka nufa, nan suka tara da an salami Jiddah, Dr ghali yace su je gidan Dr Samar yace baa’ayi haka ba, kana da Auren yarta kaje duba kanwa Abba da Dad baza suji dadi ba, yanzu muje gidanku muji mai ke tafiya, ko da sukaje suka tarar da sauran yan biki nan abokan wasa suka fara tsoka narsa angon feenat ransa ya kara bacci, da zai juwa Dr Samar ya rikesa, falon Mum dinsa sukaje, koda suka isa, habeeba suka gani tafito daga dakinsu, ganin yanda wanta ya dawo idonta ya ciko da kwala, ta juya da sauri tayi dakin mum dinsu, sai da ta share hawayenta kafin tashiga dakin tace wa Mum ga su bros sun zo, jiki ba kwari H Zaks ta fito, fiskanta dauke da fara’a suka gaisa da Dr Samar ghali ya gaidata ta amsa, nan ta musu nasiha sosai, ghali yace ina dad tace dad baya nan ya fita, Ruky ta kira, ki kawo musu abinci sai da ta kawo mum ta tasa su gaba sai da sukaci, ganin mutane yasa suka mata sallama gidan su Samar suka koma, ghali kwanciyayi yana tunane2 dinsa, ghalu ko ya zabga uban tagumi abun duniya ya ishesa, haka sukayi har dare duk sun dawi so silent, bayan magriba Dad ya kira Samar yace su zo da ghali su sameshi a gidansu feenat, sai da sukayi isha’i wajan karfe takwas kafin suka isa gidan ai ko su dad ma lokacin su ka shigo da Abba a kasan carpet suka zauna cikin biyayya suka gaida su Abba suka amsa H Muslima ne ta fito suka gaisa da dad, Abba yace takira masa feenat da jiddah, bata dade ba, suka zo tare suma guri suka zauna a kasa kusa da H muslima, cikin ladabi suka daida dad, Abba ne ya fara da Adu’ah kafin suka sha, san nan ya kira sunan ghali da feenat ya musu nasiha sosai ya kuma ce ma ghali ya rike matarsa da amana, cikin muryan kuka ghali yace Abba banaki umurnin ku ba, feenat sam bata dace daniba Dr Samar shi ya dade yana sonta, tun randa ya fara ganinta dad yace kaji min yaran “ZAMANI” book by Sheedat Y Abbas, waza ku mayar yaro zaman Aure ba fashi, Dad yace ghali ban yarda ba inji kasaki feenat
Wednesday, 1 March 2017
Home »
» BAZATA PG 21
BAZATA PG 21
Popular Posts
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(AUGUST 2016)* ...
-
MOTAR KWADAYI RASH KARDAM Duk launin kalan idonta, sun canza izuwa ja. Hannu tasa a tsakanin cinyanta tana mammatsewa,Bad Boy yana ga...
-
AMANA TA CE By ©Rash Kardam 1 Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassa...
-
🐾🐾Raheenat🐾🐾 1 Yarinya ce yar kimanin shekara 12 ta yanko a guje ta fada jikin Dad...
-
MOTAR KWADAYI By Rash Kardam 21-25 Jan motar yayi, suka bar cikin Silver Sand Hotel, bai zarce da su ko ina ba, sai gid...
-
BAZATA By ©Rash Kardam 1 Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan l...
-
[6/5/6:30pm] 🌲RASH KARDAM🌲🌲 & 🎋SADEEY S ADAM🎋 ...
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(JULY 2016)* ...
0 comments:
Post a Comment