BAZATA
By
©Rash Kardam
18
Gidan Alhaji Taneem da gidan shirye2 na biki akeyi ba kadan ba, Abban su Jiddah kayan daki bana wasa ya sai mata ba ya hada kaya bakan2 ba, sai lailaya Feenat yakeyi, sabida irin biyyan da tamasa, komai sai feenat don tunda Jiddah taki umar ninsa ya dan janye mata, H Muslima ba karan gyara take ma feenat ba, haka duk wani abu mai kyau in tagani zata sai ma feenat, Jiddah ma kudi tacire sosai sukaje kasuwa da Jiddah suka zabi kaya kai gsky feenat ta ga gata bana wasa ba, ga wani kyau da takara don tana samun gyara na musan man fatarta tayi kyau luwai2 gwanin burgewa.
Gidan Alhaji Ahmad Muhammad suma shirye2 sukeyi bana kadan ba, don Dad yana ji da dansa, ga murnan dawowansa ga biki wanda hakan yake don haka Habeeba ya kira da Ruky yace baya son lbr ya isa kun Son dinsa, yace su shirya zasuje gd Auntyn sun suji mai zatayi sai su sanar masa da murna suka amsa, shirin zuwa gidansu feenat suka farayi duk jikinsu na rawa, zasuje suga Auntyn su, wanka sukayi sosai suka sa kaya iri daya bakara min kyau sukayi ba, yayan gd H Zaks kenan, driver ne ya dauke su ya kaisu, ko da suka je feenat kadai suka samu a gd, tamusu tarba mai kyau suka zauna suna hira ta kawo musu drinks ana cikin haka sai ga Jiddah ta shigo, ganin baki yasa ta zauna a falo aka shiga hira da ita, nan su Beeba da ke kusan sa’ar Jiddah tace Aunty Jiddah da man maganar Event muka zoyi tunda angon baya gari, haka kurum Jiddah taji faduwar gaba, cikin dauriya da tace ina ga zamuyi Dinner da walima kawai ya isa ko ya kk gani, sukace haka za’ayi, jiddah in sun hada ido da Ruky sa i taji gabanta yayi mumunan faduwa don tana kama sosai da ghalinta har yanayi murmushin su, da kasaitan maganar kaman na sarakai, san nan kuma bata da yawan surutu kaman na ghali, take taji yarinyan ta burgeta, su beeba sai dab magriba suka tafi gida suna jin dadin tarban da Feenat da Jiddah suka musu abun gwanin burgewa, ko da sukaje gida sun yaba ma feenat, Ruky tace ni Aunty jiddah ta fi burgeni inama da ita bros zai aura, beebah tace nikuma banga aibun aunty feenat ba haka sukayita hira har abba ya shigo suka masa bayani yaji dadi yace da kansa zaije yaga diyarsa, H Zakiyya ma taji dadi da yanda taji halin surkanta sai fatan Allah ya basu zaman lfy.
Su Jiddah nanya sai shirin biki, Dad da kanshi yazo ya kawo kudin su walima nan yace Abba ya kira masa yaransa su gaisa, hajiya muslima ya kira yasa ta kira masa Jiddah da feenatu, hijab suka saka suka fito, bayan sun gaisa ya ciro kudi ya mika ma musu dake Jiddah itace akusa ta mika hannu zata karba, rass kake ji yanda kirjin feenat ya buga, sai da ta razana, don wan nan mutumin sunyi tsananin kama da Dr ghali kamar an tsaga kara, har sai da Abba yace lfyrki kuwa, da sauri ta amsa tayi godiya ta suka tafi, bayan tafiyan Dad da kwana 5 ya aiko ma feenat da kati da zata raba na aure, katin yayi kyau sai a lokacin tasan sunan angonta Muhammad Ahmad Muhammad har cikin ranta taji tana son sunan ya burgeta, sai ta fara tunanin wani irin zama zasuyi shi bai taba ganinta ba itama bata taba ganinsa ba, gashi auren biyya zasuyi dukkansu, wata zuciyar tace to wani irin zama zakuyi kenan, nan taji tafara tausayin kanta, tun daga ranan aka fara shirye2 na biki gashi kwanaki sun ja yau saura sati biyu biki gashi Dr ghalin Jiddah ma saura sati biyu ya dawo, Jiddah sai murna takeyi gashi dai2 bikin feenat dinta duk wani abun da zasu bukata kama daga ashobe duk sun tana da jiddah kwanan nan sai yawan faduwar gaba takeyi don har yar rama sai da tayi, H muslima ta bayeta tace ba komai, dole ta kyaleta, suka ciba da shirin biki ga shi kwanaki ya karato yau saura kwana 4 ayi walima ran jumma’a a daura Aure kuma jumma’ah da daddare ayi dinner da kai amarya, duk su Jiddah sun dawo busy ga Dr ya kusa fawo wa abun ya mata kashi 2,
yan uwansu na kaduna duk sun zo yan uwan maman feenat sun zo suma sun taka nasu rawar g
Wednesday, 1 March 2017
Home »
» BAZATA PG 18
BAZATA PG 18
Popular Posts
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(AUGUST 2016)* ...
-
MOTAR KWADAYI RASH KARDAM Duk launin kalan idonta, sun canza izuwa ja. Hannu tasa a tsakanin cinyanta tana mammatsewa,Bad Boy yana ga...
-
AMANA TA CE By ©Rash Kardam 1 Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassa...
-
🐾🐾Raheenat🐾🐾 1 Yarinya ce yar kimanin shekara 12 ta yanko a guje ta fada jikin Dad...
-
MOTAR KWADAYI By Rash Kardam 21-25 Jan motar yayi, suka bar cikin Silver Sand Hotel, bai zarce da su ko ina ba, sai gid...
-
BAZATA By ©Rash Kardam 1 Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan l...
-
[6/5/6:30pm] 🌲RASH KARDAM🌲🌲 & 🎋SADEEY S ADAM🎋 ...
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(JULY 2016)* ...
0 comments:
Post a Comment