New Post

Wednesday, 1 March 2017

BAZATA PG 25

BAZATA 
                By
©Rash Kardam 
    25                  
Abba ya ce ba damuwa, kuma na jidadin hakan Allah ya sanya Alkairi, Anwar ya amsa da Ameen,
Anwar ya samu Maryam Salis(Marsal) da farko ta ki sai da Sophia tayi ta lalashinta kafin ta amince, iyayen Anwar da Abba sun zo sun samu magabatan Marsal ansayar da rana daya za’ayi da na Jiddah, haka suka rabu cikin farin ciki, su Marsal Amare  an soma gyaran jiki shirin biki sukeyi sosai don ko ba komai suna masu farin cikin Jiddah zata Auri gowaninta,
Anwar da Marsal soyayya sukeyi mai burgewa kai kace sun saba tun tuni, marsal har mamakin kanta takeyi irin yanda take nuna ma Anwar tsan2 kulawa da soyayya, su marsal sabon shiga, a soma luv   .
A ban garen ghali kuwa gyaran gidansa ya shiga yi don yana son su zauna da Jiddah sa a gidansa na fadaman mada, in da ya fara kaita lokacin da suke rikicinsu, gyara sosai ya sa ayi don har tsarin gidan ya dan canza zuwa wani salo, ghali yanzu hankali ya soma kwanciya har ya soma murmurewa, burin shi kawai ace yau an daura, don shi yana ga binta can zai bazai iya jiran sai ta dawo ba,  wooo nikuma nace su ghali dan dauki, yanzu an samu Jiddah mun huta da rigima,   wani lokacin in yana zaune shi kadai sai dai kaga yana murmushi, karasa na meye shidai ya san mai yake tunawa.
Jiddah da Nuceey zau ne suke a kofan hall sun fito daga lectures, Nuceey ta kalli Jiddah tace wai ni kwana biyu mai ya faru na ganki cikin farin ciki, Jiddah tace Nuceey wlh na rasa mai yasa, haka kurum nake jina cikin nisha di kuma walwla na ya karu, Nuceey cikin sigar tsokana tace kodai mun samu ango ne, Jiddah ta harereta tace agogo ne ba Angoba, dariya sukayi gaba daya kafin suka shiga motar Nuceeyluff suka nufi gida suna yar hiransu abun birgewa, komai nasu tare sukeyi sun hada kansu kai kace yan’uwa ne na asali, ko da suka koma abinci suka girka kafin suka watsa ruwa suka ci, wayar Nuceey ce yai ringing tana daukowa taga an rubuta dan uwa, da murna ta daga bayansun gaisa sunyi hira, yace ta ba ma Jiddah nan ta mika mata sun gaisa ya tambayeta karatu tace Alhamdulilah, sun danyi hira sukayi sallama, haka rayuwan su Jiddah da Nuceey a skul ya kasance cikin farin ciki ga kokari ba sa wasa da karatu.
Dr Samar ya samu feenat suma sun dai2 kansu,kasancewar feenat bata da iddah tun da ghali ko dakinta bai taba shiga ba, bare ya kusance ta, shima ya turo magaba tansa, sannu a hankali Samar ya ko yarda feenat sinshi  wanda ya kasance kulum suna tare a waya, ko tana gun aiki suna tare wata shakuwa sukayi na musamman, hakan suka shiga shiri ba wasa, kwanaki sunja tau biki saura wata daya, iyayen Dr Samar sun kawo kayan Aure gsky yayi kokari sosai don ya zage damtse ya mata kayan kece raini, sai fatan Allah yasa ayi damu.
Amarya marsal da Ango Anwar suma an kai kaya komai sai son barka abun gwanin burgewa, Amare sai shiri sukeyi.
Abba yasa an kwaso kayan feenat ya sa ma H Muslima ita kuma ya sai mata sabi wanda suka fi na da kyau, ko kadan ba wanda ya fada ma Jiddah maganar Autenta, haka sukayita shi, gali ko dubai taje ya hado lefen Jiddah H Zakiyya ma tayi kikari don da ya dawo ta karamasa kayan sai na saura 3 day biki aka kai lefen Jiddah yan uwa sun yaba ko ni kaina sai da na sara ma ghali don ya kashe kudi kamar bai san zafinsu ba, feenat da taga kayyan sai da ta tsorota dob kayan sai ka sha mamaki, haka sukayita shiri Amare sun sha gyara Musan man H Muslima ta sa aka dauko sis Mamu ta gyara amare, don sis Mamu ba wasa wajen gyara     tun daga nesa in ka hango su har wani kyali sukeyi.
Rana bata karya, yau jumma’a da yazo dai2 da
    26/ feb/ 2016
Duban jama’a suka halarci daurun Auren
Muhammad Ghali Ahmad da Amaryarsa Hauwa’u(Jiddah) Taneemu,
Samar Abdallah da Amaryansa Safeenat Taneemu
Anwar Kabir da Amaryansa Maryam Salis(Marsal)
Bayan daurin Aure angwaye suka wuce hotel don gabatar da liyafa, tun gada nes

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts