AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
®WWA®
9
Bacci tayi sosai akan yar katifan inna, sai magriba ta farka tayi sallah, bayan ta idar inna ta kawo musu tuwon dawa mai laushi miyar danyan kubiya yaji man shanu, sai kamshi takeyi,nan suka ci suka koshi, sai da sukayi isha’i kafin Auta ta dingisa kafarta tashiga daki ta kwanta, bata dade ba bacci ya dauketa, Ammar ma dakin suka shiga shida malam suka kwana,
Auta bata farka ba dai asuba da inna ta daga ta tayi sallah bayan sunyi sallah,
ta gaida inna ta din gisa zuwa dakinsu malam ta gaidasu ta dawo ta zauna, don ba halin taya inna girki,… Bata da lfy,
inna ta musu dumame da kunun tsamiya, nan sukaci duk da damuwan da suke sai da sukayi santi don inna gwanar iya girki ce,…
sai bayan da suka karya kafin malam ya umurci Ammar da ya basu tarihinsa dana Auta, ammar ya gyara zama nan take idonsa ya kawo hawaye, da bai zubo ba ya fara dacewa,
Sunana Ammar Saad Saraki, ni haifafen dan maiduguri ne iyayena yan mai duguri ne, kenan su Barebari ne gaba da baya, baba na ya kasance dan gidan sarkin Gwaza ne, su biyar mahaifinsu ya haife su, Uku mata biyu masa matan akwai Ya fanna, da da hajja gana da Yakura, sai wan babana sunasa hashim sai babana mai suna Sa’ad, mahaifina ya taso cikin kulawa da kaunar mahaifinsa kasan cewar yana da nutsuwa sabani yaya shi da suke uba daya wato hashim,
hakan yasa suka tsani baba na da mahaifiyarsa don shikadai ta haifa sauran hudun duk yayan kishiyarta ce Hajiya faima,…
duk tsanar da suka masa bai damesa ba ya nimi ilimin boko da na addini bayan ya kammala karatun degree dinsa ya dawo gd,
sai mahaifin sa ya masa Auren gata da mahaifiya ta, Hakimin liman kara, hajja faty mahaifiya kenan ta kasance mace ce mai kamala da kyautatawa ga hakuri da juriya ga sanin darajan dan adam, lokacin auren kudin da sarki Abdallah Saraki ya kashe ba karamin tada hankalin hajiya fatima yayi ba, nan tace ita mai yasa baza ayi auren danta ba, sarki yace a yanda bai nitsu ba shine shaye2 yar wa za a hada shi da ita,
tun daga wan nan lokacin suka dau tsan gwama suka daura ma kakata da da mahaifiya ta, duk da hakan bai damesu ba,
kwanaki sun ja yau wata 5 da auren mahaifina da umma na nan ta fara laulayin ciki, gashi yazo mata da laulayi, bata son shan ruwan fanfo sai na rija tunda suka lura da hakan, sukayi makircinsu aka bata ruwan gdn gaba daya don karta samu na sha, haka kullum sai anje nimota ta a gari don in bata sha ba tashin hankali ne, haka rayuwa tayita tafiya.
Sarki Abdallah Saraki, ya yanke shawaran sauka a mulki sai daura dana Sa’ad Saraki akan mulkin gwaza, tun daga randa sarki ya yanke hukunci, hankali hajiya fatima ya tashi, nan suka soma shiga bokaye, sai da suka san makircin da sukayi mahaifina ya dau mahaifiya suka bar garin bashi tun daga lokacin ba asan inda mahaifina yake ba, bayan tafiyan mahaifina bakin cikin yasa yagamu da ciwon hawan jini, harya makance da ganan kuma Allah ya karbi abunsa,……
Mahaifina na barin gari bai zarce ko ina ba sai kanon dabo tunbin giwa ko da mai kazo anfika,….lol…. Amma basufi yan Bauchi ba fa,
nan ya samu wani mutumin kirki ya rikesa a unguwar Dakata, haka yayi ta rayuwansa da umma na harta cikinta ya kai na haihuwa, nan laraba ta tashi da matsanacin ciwon mara nan sukayi asibiti, ana kaita ta haifi danta, tubarkala ko kalon dan batayi ba Allah ya karbi abunsa, asai masalan da aka samu lokacin tana mai duguri, maganin da aka a rijiya ta sha don karta haihu dake Allah yayi zanzo duniya sai da ta haifen lokacin ya mata illa sosai, shine sanadin mutuwarta.
®WHW®
Rash Kardam
Friday, 17 March 2017
Home »
» AMANA TA CE 9
AMANA TA CE 9
Popular Posts
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(AUGUST 2016)* ...
-
MOTAR KWADAYI RASH KARDAM Duk launin kalan idonta, sun canza izuwa ja. Hannu tasa a tsakanin cinyanta tana mammatsewa,Bad Boy yana ga...
-
AMANA TA CE By ©Rash Kardam 1 Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassa...
-
🐾🐾Raheenat🐾🐾 1 Yarinya ce yar kimanin shekara 12 ta yanko a guje ta fada jikin Dad...
-
MOTAR KWADAYI By Rash Kardam 21-25 Jan motar yayi, suka bar cikin Silver Sand Hotel, bai zarce da su ko ina ba, sai gid...
-
BAZATA By ©Rash Kardam 1 Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan l...
-
[6/5/6:30pm] 🌲RASH KARDAM🌲🌲 & 🎋SADEEY S ADAM🎋 ...
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(JULY 2016)* ...
0 comments:
Post a Comment