BAZATA
By
©Rash Kardam
22
Ko da suka fita dad da Abba suka rakosu feenat sai kuka taketayi, motar su Samar dad yace tashiga Samar ya kaisu, gidan baya tashiga ghali da samar a gaba, samar yaja mota suka bar gidan Dad na bayansu, sai da Samar ya kaisu har cikin gd kafin ya musu sallama yaja motar ya koma gd da kyar don wani zazzabi ne yake neman rufeshi, ko da ya isa gida ruwa ya watsa ya yi alwala ya gatar da sallah nafila, adu’ah yayi sosai na Allah ya bashi hakuri da dangana bayan ya shafa ya kwanta.
Ghali ko gidan yashiga daki na farko yaga kaya sosai nan ya gane na feenat ne dayan daga gado sai sif, shi yashiga ya sa key, feenat na ganin yashiga daki daya itama tashiga wanda ya fara lekawa taga kayanta nan tagane dakinta ne, kulle kanta tayi itama kuka tayi sosai ganin kukan bashi bane mafita yasa ta dauro alwala ta fara sallah, ko da gari ya waye ghali bai bi ya kanta ba ya fita gidansu samar ya koma, samar na ganinsa yace mai yasa yagito yuwar haka, wani mugun kallo ya masa wanda yasa Samar jan bakinsa yayi shiru suka shiga ciki, sai da suka karya kafin suka fita zuwa cikin gari basu suka dawo ba sai dare bayan isha, ghali yace shifa ba zai koma gida ba, nan Samar yasa shigaba yayi ta masa nasiha wanda dole yasa ya mike ya karbi key din motar ya nufi gida.
Feenat bata fitoba sai kusan shabiyu rana idonta ya kumbura dosai, store tashiga ta dauko indomee ta dafa da ruwan tea tasha daki tasake komawa ta kulle kanta sai da yanma tafito ta sake dafa indomee taci takoma dakinta, ghali bai dawoba sai kusan 9:00 yana zuwa dakinsa ya wuce wanka yayi ya kwanta sam ya kasa bacci sai tunanin Jiddah sa yakeyi, tundaga wan nan rana haka rayuwansu feenat ya kasance sam bata bari su hadu da ghali shima bai damu da ya ganta ba duk wanda yasan ghali ada in ya ganshi yanzu sai yayi da gaske ya ganesa, yayi duhu duk gayunsa ya rage, yara ge yawan magana baya son shiga mutane.
Jiddah itama duk rayuwanta ya canxa ta dawo shiru2, bayan kwana biyu da faruwan abun, taje gun professor Aminu Ilyass ta masa bayani tana so ya tayata, niman Admission ita a kowani kasa ne tana so, nan yakarbi copies din ta kardunta, yace taje duk yanda tayuwu za tajishi, da murna ta dawo gd, yunda ga ranan tafara fita aiki sai dai ko kadan taki su hadu da ghali,
Yau tafito gun aiki bayan antashi tabi winti market ta karbi dinkinta, tafito kenan taga wani katuwar Jeep tatsaya a gabanta da sauri ta kauce tashiga motarta, ta tayar ta bar guri aeko sai taga mai motar yana binta, gudu tarinka yi shima ya kara ko da ta leka ta madubi sai taga motar har biyu suke binta dan haka taki bin hanyan gida ta nufi gidansu Sophia ko da ta iso kofar gidan ta ajiye motarta tafito kenan taga wani matashin saurayi fari sol kyakyawa da shi, ya nufota cikin fara a Sallama ya mata wanda yasa dole ta amsa masa, tazo zata wuce yace malama dan girman Allah ki saurare ni kiji mai zance maki, cikin sanyi jiki tatsaya yace Malama dan Allah meye sunan ki, kafin ta masa magana sai ganin ghali tayi yana huci yazo ya shake saurayinan yace kai baka da hankali ne matar nawa zaka tsaya da ita dan iska, ran jiddah ya baci tace kai ghali mai ya maka kasani, ni yanzu ba malakinka bane kayi hakuri ka fita a rayuwata, bana sonka bana soka, ghali kai mijin yata ne meye gamina da kai, ghali mtss tazo kusa da wan nan saurayi tace kayi hakuri kaji dan anjima kazo kasameni, shiko ya dauka gidansu ne cikin jin dadi ya tafi, ghali ya tsaya don tsananin mamaki, Jiddah ki ge fensa tabi ta wuce zuciyarta namata wani irin radadi tana shiga gidan su Sophia kuka tasaki a daki sophia don ta san bata kyauta ma ghali ba tayi hakan ne don ya rabu da ita ya zauna da feenat lfy, ko da sophia taga tana kuka rarrashinta tasjiga yi da kyar tayi shiru kafin sophia ta tan bayeta meye ta sanar mata, sai da ta dan huta kafin ta wuce gida, tana isa wanka tayi ta huta tukun tashiga kitchen ta taya Ummanta girki, bayan sungama ne tazo
Wednesday, 1 March 2017
Home »
» BAZATA PG 22
BAZATA PG 22
Popular Posts
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(AUGUST 2016)* ...
-
MOTAR KWADAYI RASH KARDAM Duk launin kalan idonta, sun canza izuwa ja. Hannu tasa a tsakanin cinyanta tana mammatsewa,Bad Boy yana ga...
-
AMANA TA CE By ©Rash Kardam 1 Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassa...
-
🐾🐾Raheenat🐾🐾 1 Yarinya ce yar kimanin shekara 12 ta yanko a guje ta fada jikin Dad...
-
MOTAR KWADAYI By Rash Kardam 21-25 Jan motar yayi, suka bar cikin Silver Sand Hotel, bai zarce da su ko ina ba, sai gid...
-
BAZATA By ©Rash Kardam 1 Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan l...
-
[6/5/6:30pm] 🌲RASH KARDAM🌲🌲 & 🎋SADEEY S ADAM🎋 ...
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(JULY 2016)* ...
0 comments:
Post a Comment