BAZATA
By
©Rash Kardam
13
Kwanaki sun ja, Jidda ce zaune cikin dakinta kasancewar yau weekend, tana ta danne dane a system dinta, taji kara shigowar mai message ta gmail dinta, sai da ta gama abunda zatayi ta bude sakon, taga bata gane mai sakon ba, ta duba profile din ba wani abunda zata gamusu, sakon ta fara karan tawa kamar haka.
Assalamu’alaiki
Ya ma’abociyar sanyi da kamshi, farin wata mai haskaka sauran, kyakyawa acikin kyawawa, mutunci kamala fara’a suna dauke a fuskan ki, Hauwa’u tun randa na fara ganin zuciyata ta harbu, da tsananin kaunar ki, Jiddah ke mace daya ne tamkar da dubu, kallo ki na hadda samin farin, murmushin ki kan jefani kogin kauna, tafiyar na sanya ni cikin nishadi, bare ki bude dan karamin bakin har labbanki su motsa, zazzakan muryanki ta fito Ya Allah, kusan suma nakeyi, Jiddah ina matukar kaunanki ki taimaka ki son ko kwatan kwacin kwayan zarra ne, niko zan zameki Zuma mai tsanani zaki, zakuma kiyi Alfari dani nan gaba ina matukar kaunarki.
Mai Son ki
Tabbas kalamansa sun mata dadi amma sam ita ba soyayya bace a gabanta, wani tsaki taja kafin ta goge sakon. Ta kashe system din koda ta dawo kan gado taji massage ya shigo wayarta, tana budewa taga wani bakon number ya turo mata sako kamar haka.
My Jiddah
Every time i see a flower ……. I think about u and how much i want to be with u n how much i want to hear ur sweet voice, i luv u Jiddah pla luv me.
Urs
Lover Boy
Ta karanta sakon yafi akirga gaskiya guy din ya iya kalamai amma ba shi bane a gabanta, goge sakon tayi tacigaba da sabgarta, har dare tayi nan taji wayarta na ringing ko da ta dauka, new number tagani da sallamart tasa a kunne cikin wata sassayan murya mai daukan hankali, taji ana cewa Amincin Allah ya tabbata a gareki ma’abociya sanyi da kamshi ga kyan fuska, koda batayi niya ba sai da ta murmusa:) yaciga ba da cewa, My Hauwa ina matukar kaunanki sosai, Son ki yamin “BAZATA” amma nasan ke cikin tsiwa tace kai tsaya malam wai waye ne yake niman takura ma rayiwata, waye ne?? Cikin sanyin murya yace Mai Sonki ne. Wani tsaki tayi takashe wayar gaba daya ta kanta, sai me sam bacci yaki daukarta kaman mutumin sai yawo yake mata akanta rutse ido tayi har bacci ya dauketa, tunda ga ranan mutumin nan yasata gabada kamai tun bata so harta dawo jin dadi kalamansa wani sa in ta saurare sa, su dan gaisa haka rayuwa su tayita tafiya.
Cikin shirin aiki tanufi office don yau suna da meeting, Ko da ta isa mu marsal da sophia sun zo, jiran time kwai sukeyi su shiga metting, hira suke sosai, sai ga Dr Ghali da Samar su nufo su, Jiddah ta hade rai sai wani kun buri takeyi, ko da suka iso Dr Samar ne yace sanuku ya kk ya aiki suka amsa d lfy, ya kalli sophia yace Sophee pls ki dan kira mana Suhana a waya kice ita da Dr Saleem suyi sauri time din da za’a shiga fa yayi, mun kira wayar Saleem na kashe tace to, ta kirasu sikace gasu a hanya, dogiya sukayi suka wuce sai da sukayi nisa yace ya abokina kaga target yayi ka ganta cikin sauki, murmushi yayi, haka sukayi ta hira har aka shiga meeting duk wasu man yan Doctors din T.H sun hallara hall yacika, sosai kowa ya zauna, bayan wani Dr ne ya bude taro da Adu’a, bayan an shafa, professor Aminu Ilyasu ya mike cikin harshen turaci yake mafana, topic dinsu na yau akan Seminar da zasu je Kaduna 2 da kuma Doctor dinsu biyu da basa shiri, 3 zakuma a wakilci masu zuwa Seminar, sabida basa son in aje a samu matsala, hall din ne ya dan argitse da surutu, kafin ya ce ayishiru, saida gu ya lafa, yasoma bayani yanda seminar zai kasance bayan ya gama ya gan garo kan yan da zasu tafi, nan yasoma da kiran sunan doctors din 1 Aminu Ilyasu 2 Muhammad Ghali 3 Samar da Saleem. Female 1 muna da Hauwa’u Taneem 2 Maryam Sais( marsal)
Wednesday, 1 March 2017
Home »
» BAZATA PAGE 13
BAZATA PAGE 13
Popular Posts
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(AUGUST 2016)* ...
-
MOTAR KWADAYI RASH KARDAM Duk launin kalan idonta, sun canza izuwa ja. Hannu tasa a tsakanin cinyanta tana mammatsewa,Bad Boy yana ga...
-
AMANA TA CE By ©Rash Kardam 1 Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassa...
-
🐾🐾Raheenat🐾🐾 1 Yarinya ce yar kimanin shekara 12 ta yanko a guje ta fada jikin Dad...
-
MOTAR KWADAYI By Rash Kardam 21-25 Jan motar yayi, suka bar cikin Silver Sand Hotel, bai zarce da su ko ina ba, sai gid...
-
BAZATA By ©Rash Kardam 1 Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan l...
-
[6/5/6:30pm] 🌲RASH KARDAM🌲🌲 & 🎋SADEEY S ADAM🎋 ...
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(JULY 2016)* ...
0 comments:
Post a Comment