New Post

Friday, 17 March 2017

AMANA TA CE 2

:   AMANA TA CE 
                 By
©Rash Kardam
  2
                  
Tass kake ji karan harbin bindiga   nan take Auta tasaki razananen kara, da sauri suka juyo girin da sukaji karan suna fadin suwaye, suka nufo gun, Ammar yana ganin haka yaja Auta tana turjewa ita sai taje gun su Dad da Hajiyarta, dakyar ya shigarda ita dakinta yasaka key ya kullesu, ga ruwa sai sauka  yakeyi ana tsawa, nan yarasa yanda zaiyi Adu’ah ya tuno na ne man tsari daga abokan gaba ya fara karantawa, autakan sai kuka take, ana cikin haka su Kawu Sani suka iso kofar nan suka fara jijjiga kofar, Auta ko kara sautin kuka takeyi Ammar bai san lokacin daya daka mata tsawa tayi shiru don kukanta har cikin zuciyar  shi yake tabasa, nan ta damke bakinta , duk ya rue yarasa ya zaiyi gashi ba hanya, kasu Baba Isiya da sani su jijjiga kofa ga harbin    suketayi, kiris yarage su balla kofar nan take dabara ta fado masa da sauri yayi gun Waldrop, ya zazzagar da kayan ciki kasa da kyar ya turo ya jawo ya kawo zuwa bakin kofar ya tokare, nan ya janyo dress miro shima ya tokare nan ya dafe kansa sai ga wasu zafafan hawaye:'(:'( ke zuba yana kiran sunan Allah ya kawo musu mafita.
A bakin gate kuwa mai gadi da sale suka leko ganin su Alhaji an sheka kiyama suka sheke da dariya sukace yau ina kudin ka ya dawo namu, gumus ne ya fito yace kuba mu karfe ina tunanin akwai wasu agidan nan zamu balle ko fa, don yar Alhaji na tare da wani Sai a lokaci idi yace kai:oops::oops:munyi kuskure daya da muka bar dakin Ammar bamu fara ta kanshi ba barinje na dubo shi, ko da yaje dakin ba ammar nan yace duk yanda akayi Auta tana tare da Ammar amma bazasu gudu ba, don gidan nan na rufe ba gurin tsira dariyan    mugunta suka farayi, wani katon karfe suka samo wanda duka daya zasuyi wa kofar su balle, nan suka nufo cikin dakin da karfen.
Ammar kuwa adu’o’i yakeyi can ya tuna windo dakin na glass da sauri ya mike nan ya fara dube2 ba wani karfe a dakin wanda zai fasa ga shi sukuma sun kusa balle kofa duk ya kalli ko ina na dakin ba wani abu, sai can ya kalli Bedside drawer, da sauri ya dauko ya zubar da kayan ciki, ya nufi windon da karfin ya buga tare da bissmila bugu biyu yayi mai kyau wundon ya balle sosai yanda zasu wuce sai da ya leka ta baya yaga ba kowa kafin ya dauko Auta ya sanyota ta waje tasauka kenan yana shirin fita wani kwanban da bai gama balle ba ya yankeshi nan sai ga jini sosai gashi kwalbar ya shiga sosai har sai da yace washhhhh, lokacin su baba Sani suka balle kofar suka nufoshi.

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts