New Post

Wednesday, 1 March 2017

BAZATA PG 15

BAZATA 
                By
©Rash Kardam 
  15                    
Jiddah ta daga idonta da ya canza kala zuwa ja, cikin sauri ta tashi jiki ba kwari ta nufi room dinta, kan gadon ta fada, kuka tasoma rusa why me yasa zaka bada jininka a jikina, ke nan yanzu jinina ya gauraya da naka, kuka tayi sosai, tana cewa i hate u Dr, why u do dis 4 me, dafata da taji anyi yasa ta dago marsal ta gani, jikinta ta fada tana kuka, marsal ta rarrasheta, tace kiyi hakuri Dr ba yayi da nufi bane yayi don Allah ne, kuma Jiddah ki kasance mai yafiya “Allah yana son masu yafiya da hakuri har albishir ya ce a musu, lalashinta tayitayi da kalamai masu dadi, harta hakura, amma sam batajin manta abunda Dr ya mata, sai da sukayi Sallah magriba kafin marsal ta fita, saida ta shiga dakin Sophia ta taras tana waya da yan gidansu bayan sungama suka dan taba hira ta mata sallama, ta tafi dakinta,
Bayan fitan marsal jiddah ta yi sallah isha’i ta roki Allah ya rage mata irin tsanar da takeyi ma Dr ghali, bayan ta shafa Adu’ah sai da tasha tea kafin ta kwanta tana tunani kala2 har bacci ya dauketa.
Dr ghali kuwa zazzabi ne ya rufesa sosai, sai rawan dari yakeyi, Dr Samar ne ya shigo ya gansa haka da sauri ya karasa gun sa ya yaye bargon, yaji jikinsa zafi, da sauri ya koma dakinsa ya debo kayan aiki ya auna sa, sannan ya masa alura , ba a dade ba bacci ya daukesa, ganin halin da ke ciki yasa samar rufe dakinsa ya dawo gunsa ya kwanta a resting chair dakin, bai farka sai kusan uku saura, nan yaji jikinsa ya masa sauki, bayi ya shiga yayi alwala ya biya sallah da ake binsa, tea samar ya hada masa ya sha, kafin ya bashi wasu magain  ya sha, ya sanan ya koma bacci da asuba suka yi sallah, bayan sun idar samar ya masa fada sosai, kan ya bar sanya damuwa a zuciyarsa gashi har jinimsa yaso ya hau, ko da sukayi breakfast suka nifi gun seminar, kallo daya zaka masa kaga irin ramar da yayi sosai, sai karan hancinsa da ya fito sosai, su jiddah ma haka suka fito sunsha kyau, suka nufin gun sau ran mota suka shiga suka nufi gun seminar. Jiddah ta kasa sakewa, sosai haka kurum taki son su hada hanya da Dr ghali, haka suka gama seminar suka soma shirin dawowa, sai da sukaje Abuja Road ta gaida yan uwan babanta ita da su Marsal kafin suka dawo hotel din washe gari suka dau hanyar bauchi, tun a hanya ta tura ma Lover Boy dinta sako kamar haka
        My Only
Gani a han yar dawowa, farin cikina, zan so ace kai zan fara tozali da kai don ina muradin ganinka burina mu kasance tare.

       Ur beloved Jiddah
Mesage ne ya shiga wayar sa bayan ya karanta yayi mata reply kamar haka,
           My Jiddah
Jiddah ina sonki ina tsananin kaunar ki but ina tsoron randa zamu hadu karkice baki sona kun fasa.
          Mai Son ki
Ko da takaranta mur mushi tayi ta mayar masa da amsa ka mar haka,
           My Hrt
Kasani Sonka da kaunar ka daga Allah ne ajina yake ina matukar sonka ina kaunarka, ban damu da ya kake ba kai nake so kai nake kauna, kudi ko kyau basa gabana kai ka dai ne a gabana, Sonka d Kaunar ka na tasa a gabana bana jin kira bana wai ge, na baka kaina  da zuciya ta .
           Ur Jiddah
Ko da ya ka ranta ya sake turo mata wani sakon
        My Jiddah
   Ki min alkawarin cewa in kin gani ko yaya nake bazaki kini ba zaki cigaba da sona a ko yaya nake, kuma duk rintsi duk wuya bazaki juya min baya ba.
            Mai Sonki
Ko da ta karanta murmushi tayi wanda yasa marsal da Sophia hada ido suka kalli juna, marsal kasa hakuri tayi tace wai nikam Jiddah murmushin mai kikeyi ne, tace kwaji da gulmanki, ina tare da Lover Boy ai dole kuka ina Smile:). shewa sukayi suka tafa ta ciga ba da rubu tunta,
        My Hrt
Na maka Alkawari bazan gujeka ba har karshen rayuwa ta ko da ta kasance kai gurgune ko makaho, ko mafi da gaka ni kai nake so kaunar ka ya kamani a cikin zuciyata bazan iya gudunka

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts