New Post

Wednesday, 1 March 2017

BAZATA PAGE 10

BAZATA 
                By
©Rash Kardam 
  10                   
Dr Saleema ne ya daure ya bashi lbr abunda ya faru, san nan Sajan Nasir ya daura daga inda suka gamu Abbanta shiru yayi kafin yace ya gode ma Allah da ba abunda ya sameta, kuma daga yau ta bar zuwa biki, san nan yace Jiddah waya gaya miki a na wa namiji irin yanda kk masa shifa tai makon ki yayi duk da bai kyauta ba kema baki kyauta, Allah ya kare naga ba, suka amsa da ameen, sallama suka masa shida iya lansa sukayi cikin gida, Su Samar suka koma mota Dr ghali ya kalle samar yace naga jiddah ta dawo ina fatan ba abinda ya sameta, ko kallonsa baiyiba sukayi motarsu suka tafi don ya bata musu rai, gashi ko bacci basuyi ba har 3:20am tabbas ya san bai kyauta ba har su samar sukayi fushi ga baccin dayake ji haka ya tada motarsa ta bar unguwan jiki ba kwari.
Jiddah ko tunda suka shiga gida abba yace suje su kwanta, daki tashiga ta watsa ruwa ga kafarta sai zafi yake mata, rabonta da tayi gudu irin wan nan har ya manta,ko da tafito doguwar riga tasa da hijab ta biya salolin da ke kanta kafin ta kwanta bacci tayi sosai, ko da gari ta waye bata tashiba sai kusan 6:40 tayi sallah asuba kafin takoma ta kwanta dake weekend ne ranan sai goma da mintoci ta farka, toilet taje ta wanke bakinta kafin tayi wanka ta sa kaya marasa nauyi tafito falo, ta tarar da Abba da H Musleemah sun fito feenah tana kan dining ta gaida iyayenta kafin taje ta gaida Aunty ta, suka yi breakfast a tare, kafin suka dawo gun su Abba suka zauna Abba ya musu fada sosai, yace ma Jiddah ta kiyaye yin gatsali ma na miji, don tayi sa’an mai kirki da wani sai ya mata rashin mutunci, kuma yace daga ranan ya soke zuwa bikin dare, in ba da wani dan uwanta na kusa ba, san nan yace sa iya tafiya, tun daga wan nan ranan Jiddah take jin wani tsanar Dr Ghali ko kallonsa bata sonyi bare taji sunan sa haka ta karashi weekend din duk jikinta ciwo yakeyi.
Dr Ghali kuwa tunda tunda ya koma gidansa, kasa bacci yayi, don in ya rufe idonsa Jiddah yake gani tana masa murmushi, gashi ta tafi ta barmasa kamshinta, sai lumshe ido yakeyi, take ya fara jin wani irin feelings gameda Jiddah, sannu a hankali yake karanto surarta sai wani murmushi yakeyi haka kuru yaji zuciyarsa na tsanani son ganinta, nan take ya tambayi me take nufi kardai na kamu da son  Jiddah yace anya yarinyar da bama shiri, can yaga tunani ba zai ficcesa ba ga dare yayi, alwala ya yi ya shimfida salaya ya fara kiyamul lail, haka har aka yi kiran sallaha kafin yaje masalacin da ke unguwar yayi sallah ya dawo, Azkar yayi har zuwa 7:00am kafin ya kwanta bacci, nan ya fara mafarki mai dadi, Jiddah ce tazomasa da wani fulawa  mai kyau ga kamshi ta mika masa
tana murmushi, cikin fa’a yakarba ya zo dafda ita zai mata rada a kunne ta ju tasoma wani tafiya mai daukan hankali tana karairaya, dai dai nan yaji wayansa na ringing, ya ki bude idonsa amma sam ya bar ganin Jiddah, wani uban tsaki ya daka kafin yadaga, yaji Company MTN ke masa talle Caller Tone, nan yaji wani bakin ciki ya tokaresa, wayar ya kashe ya koma ya sake lumshe idonsa kozaiga Jiddah amma shiru, haka yayita juyi karshe wanka yayi ya saka kanana kaya ya nufi restaurant ya sai abinci bai wani ci na kirkiba don yanzu zuciyarsa ta addabesa da tunanin jiddah har Allah, Allah yakeyi monday su hadu agun aiki yaga kyakyawan fuskarta mai burgewa.
Su samar ko da suka isa gida Wayar Sophia Samar ya kira ya saida mata ansamu Jiddah ta fada masu Marsal tace to sukayi sallama suka kwanta suma da gajiya suka tashi, haka akayi yinin biki ba wani amarshi sosai, sabida jiga jigan bikin basu samu hallara ba, sai dai muce SUHANA DA SALEEM, ALLAH YA BADA ZAMAN LFY.asha amarci lfy   .
Yau take Monday da wuri jiddah ta fita don taso makara, gudu tayi sosai bata dau mintuna masu yawa ba ta isa ATBU, parking motar ta tayi ta fito tana dan sauri, wanda saurin da takeyi yasa duk ilahirin jikinta motsawa, ga can nesa na hangi Dr Ghali ya ha

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts