New Post

Friday, 17 March 2017

AMANA TA CE 5

:   AMANA TA CE 
                        By
©Rasheedah .A. Kardam
  
                  ®WWA®
          5                      
Ko da sukaje gidan kawu isiya wanda tutun nufawa, ba kowa aciki kuma ba nisa sosai da gidan Alhaji marigayi, nan suka shiga ko da suka zauna nan baba sani yace yau burin mu yacika na gama wa da Al-hasan da iyalansa, kamar yanda mukayi Alkawari zamu ba ku 400k kowa zai dau 200k kenan gumus ne yace oga mungo amma munaso aba mota koda kwaya daya ne ehhh musamu na yawo a gari, ko wani aiki kuke so zamu muku cikin sauki kawu isiya yace aaa bazai yuba abun yaso ya dawo musu rikici baba sani yace ba matsala za a duba in komai ya lafa abaku, nan ya ciro 300k ya basu yace kurike wan nan kafin komai in ya lafa zamu sallame ku, gaba daya nan sukayi sallama kowa ya kama gabansa.

Da safe yan unguwa suka fito don wasu sunji karar tsayuwar  don haka suka yi cirko2 gashi jiya anyi ruwa sosa, mukwabcin dad wani mai suna Alhaji Abubakar yace yan uwa yau ban ga Al-hassan a masallaci ba kuma duk rintsi in ba jinya yayi tsanani yana zuwa sallah amma yau shiru, ko lfy wani mai suna Alhj kabir yace ni jiya fa kamar an shigo unguwan nan don duk da karan ruwan sama   dake zuba naji ihu san nan naji harbin bindiga  sun dade suna jimami kafin wani acikinsu yace kamata yayi mu shiga gidan mugani, nan suka dun guma suka shiga tun a kofa sukaga masu gadi an daure su, da sauri suka isa wajansu, bakinsu an toshe da tsumma, kunce su sukayi nan Alhaji Abubakar ya fara tambayan lfy, sun wahala yasa ba wani amsa don dauri da aka musu mai kyau ne hakan shi ya gala baitar dasu, da sauri suka nufi cikin gidan bayan sunshiga a falo suka tarar da gawan Alhaji da hajiya nan suka soma jimami masu kuka   suka fara, alhaji abubakar makocin dad police ne nan take ya kira ja mi’an tsaro suka fara binjike nan sukaje dakin Auta inda suka ga yanda aka baza kaya da alamar kare kansu da sukayi da kuma fasa window da akayi gashi ba auta ko da suka zaga nan sukaga jini da kuma alaman harbin da akayi ta waje, Alhj Abubakar yace cikin daya biyu ko sun kashe Zainab ko sun dauketa ko da suka dawo gd sai alokacin ya tuna da ammar nan ya nufi dakin da ke tsammanin nasa ne sallaya tagani a shin fide da alamar anyi sallah akai ki da suka fito suka nufi kofar baya nan sukaga an tura kofar anshiga duk binciken da sukayi ba wani amsa nan suka kira Alhaji sani da baba isiya suka sai da musu, ko da suka iso gidan kuka sukeyi sosai kai ka rantse basu da hannu aciki har sani na ikirarin imyasan wanda yayi kisan nan sai ya dau fansa, kawu isiya kam ko mace iyakaci yanda yake kuka. haka police suka tafi da gawarwakin don kara bincike.
Ammar da auta kuwa tafiya yayi sosai, sun shigo cikin gari kuma dare yayi sosai don asuba ya kusa, nan yasamu inda ba ayi ruwa ba ya kwantar da Auta ya yagi zanin dake daure a saman kayan baccinta ya kulle hannusa sai runtse ido yakeyi alamar zafi, ya daure hannuta ya dauketa suka cigaba da tafiya sunyi nisa sosai, sai ga wani mai mota yazo wucewa nan ya tsare shi sam yaki tsaya haka ya cigaba da tafiya sai ga wani da alamar wan nan irin yan taxi masu zuwa gari zuwa gari har yaki tsayawa komai ya tuna ya dawo daukarsu, nan Ammar nace ina zan kaiku Ammar yace ban sani ba mutumin yace to ni saminaka zanje yanzu, yace muje ka ajiye mu a hanya.
               ®WHW®
    
Rash Kardam 

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts