🐾🐾 Raheenat🐾🐾
Rash Kardam💃🏻👈🏻
7⃣5⃣ -7⃣6⃣
Ba wanda zaiga h maryam yace, bata haihu ba, tayi kyau gashi ta cika, haka akayi suna, Abba ya yanka mata raguna biyu, suna dai sai son barka, tun daga ranan, H Maryam tacigaba da kula dake Raheenat, har kika kawo ga yanzu, wan nan shine lbr ki, in banda sheka2 kukan Heenat da h maryam ba kajin komai, sai da sukayi mai isarsu kafin Abba yace ya isa haka, Raheenat ya kira sunanta, cikin muryan kuka ta amsa, yace kamar yanda kike min biyayya ama tsayin uba ina son kikara min, cikin a sanyaye tace Abba komai kasa ni in maka zan bi umurnin ka banda kowa sai ku, dole in muku biyayya shine ka dai abunda zan saka muku dashi, Alhamdulilah yace akaro na biyu ya ce Heenat na Aurar dake ga wanda na san zai rike ki amana, da saurinta dago ta kalli Abba, cikin zuciyarta ko tace Abba dole in maka biyayya ko don rike ni da kayi, ko da ko wanda kau aura min bansonsa ko da mahaukaci ne, bare ma wa zai Aure ni Yar shege Yar tsintuwa”, maganar Abba ne ta dawo da ita daga tunanin da take, ina fatan ba zaki ki zabin mu ba a sanyaye tace na amince abba, yace Allah ya miki Albarka, tace amin ya ce sutashi su basu guri heenat, Aimana, Aisha duka suka wuce daki, ya kalli H Murja yace ke kuma shawaran da zan baki, yanzu in kin ga dama ki dauka ruwanki, don abun in ya baci wake zaiyi muni, yacigaba dacewa yanzu ba lokacin fushu bane, Adu’ah zakiyi ma danki din abun da na lura akwai asiri ajikinshi, tabbas matarsa bata kyaleshi haka ba, duk kan mu zamu dun kufa da Adu’ah, jikinta yayi sanyi bata ce komai ba haka suka watse kowa da abunda ke sakawa.
Ko da su baba larai suka je daki fada sukayi wa H Murja wanda yasa jikinta sanyi kuma ta gaskata abunda suka fada mata, ta kudiri aniyar yi ma danta Adu’ah, ta kuma rike surkarta da amana, tun daga wan nan rana gidan Alhaji Muhammad Dalhat ya dawo zaman lfy, tsakani h maryam d Murja mutunta juna da girmama juna, Aimana ta koma gombe haka Aysha ta na gidanta, Heenat kuwa kunyace tsakaninta da H Murja tun da taji MY ne Mijinta, haka zataje ta gyara mata daki ta mata yan wanki, wan nan duk aikin h maryam ke turata, ran girkinta ta taya ta aiki haka rayuwansu ya cigaba da gudana, h Murja na kuala da surkanta heenat sosai, Matsalarta daya ce bai wuce danta da aka rasa gane kansa ba wanda yanzu rabonsa da gidan ya kai wata daya da rabi bai zoba, dukkansu sun dun kufa Adu’ah.
Hausawa sunce duk abunda yayi farko, to tabbas yana da karshe, MY kullum ya zauna ya ringa tunanin iyayensa wai me ke hana sa zuwa gidansu bare har ya duba iyayensa ya gaida su ya samu lada, kamar an tsikaresa ya mike gida ya shiga, wanka yayi ya fito zai fita, Sadde taso cikin isa da gadara, tace ina zaka bai kulataba ya dau takalminsa zai fa tazo da sauri taja rigansa cikin bacin rai ya wanke ta da mari jikake tass, ya bata uku kyawawa, koka ta saki taci kwalar rigansa ta kamashi da kokuwa, duka ya mata sosai ya fita ransa abace, ko da ya isa gida haka kurum ya ji kirjinsa na dukan3 ya gaida mai gadi ya shiga ciki da Heenat ya fara karo tafito da ga side din h murja, sallamasa taji da sauri ta juya suna hada ido sai da gabanta ya bada damm… Ta amsa da sauri tayi side su, kansa ne ya daure, to mai ya kawo heenat gidan kuma yaushe akayi auren ta da har zata zo gida ga shikuma da alamar ta yini agidan ne, dakin mamansa yaje ko dayayi sallama ta amsa masa, sabida sanin muhimmanci amsa sallama, tun daga kan wan nan bata sake cewa komai ba, ta share shi ya gaidata yafi sau 3 amma taki amsawa a sanyaye yafito, yayi side H Maryam ya daidata ta amsa da fara’ata sannan yafito falo ya zauna, sai da ya dade ahaka kafin abba ya dawo yayi sallama, MY ya amsa masa abba bakaramin mamaki yayi ba, karasa shigowa cikin falon kiran murja ya
Friday, 3 March 2017
Home »
» RAHEENAT 75-76
RAHEENAT 75-76
Popular Posts
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(AUGUST 2016)* ...
-
MOTAR KWADAYI RASH KARDAM Duk launin kalan idonta, sun canza izuwa ja. Hannu tasa a tsakanin cinyanta tana mammatsewa,Bad Boy yana ga...
-
AMANA TA CE By ©Rash Kardam 1 Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassa...
-
🐾🐾Raheenat🐾🐾 1 Yarinya ce yar kimanin shekara 12 ta yanko a guje ta fada jikin Dad...
-
MOTAR KWADAYI By Rash Kardam 21-25 Jan motar yayi, suka bar cikin Silver Sand Hotel, bai zarce da su ko ina ba, sai gid...
-
BAZATA By ©Rash Kardam 1 Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan l...
-
[6/5/6:30pm] 🌲RASH KARDAM🌲🌲 & 🎋SADEEY S ADAM🎋 ...
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(JULY 2016)* ...
0 comments:
Post a Comment