New Post

Friday, 3 March 2017

RAHEENAT 47-48

🐾🐾 Raheenat🐾🐾


Rash Kardam💃🏻👈🏻

            4⃣7⃣-4⃣8⃣
Woow tace a cikin zuciyar ta furta a zuciyarta, gaskiya guy din ya hadu, a hankali ta janye hannunta, daga nasa ta sun kuyar da kanta, shiko kasa dauke idon sa yayi daga kanta gaskiya ta hadu iya haduwa, kasa motsi yayi ila binta da yayi da ido, gani da yayi taje zata biya kudin kuma alamar ta fiya zatayi da sauri ya bita gurin biyan kudin suna gama lissafi, accountant din yace 30k tana kokarin cirowa, ya sauri ya zaro kudin da shi kanshi baisan nawa bane, ya basu, ko kalloshi batayi ba cikin zazxakar muryamta mai dadin sauraro,lfy malam? muna da kudin biya ba sai ka biya mana ba, shiko kasa magana yayi ya tsaya yana kallon dan karamin bakin👄ta yanda take budesu tana magana kamar bataso, gani ya tsaya mazuba mata ido yasa, ta ajiye kunta, tajuya ta bargurin sophia na ganin haka ta juma zata bita da sauri ya sha gabanta sis dan Allah ki karbi kudin, banson muyi musu, da farko taki amma kwarjinin sa, yasa ta amsa, har tajuya zata tafi, yace sis ta juyo, ya sunan ki da murmushi a fuskanta, tace sophia, nice name yace, aunty, fa tace, Heenat woow yace suna masu dadi tajuya zata tafi ya daga mata hannu alamun byee ita ta mishi, ko da ta iso muta🚘 heenat fada ta mata sosai, sophia tun da taga ran aunty heenat ya baci, shiga bata hakuri, wlh ba da gan gan ta tsayaba, ko ta kanta bata bi ba tace ma driver su tafi,

Shi ko suna fita, shima motar sa ya shiga, a hankali ya rinka binsu har suka iso Unguwan Sarki, nan ya ga sun shiga katun gida mai dauke da bakin gate a kofarsa, sai da ya dade ya ga basu fito ba nan ya tabbar gidansu ne, jiyawa yayi ya dau hanyar unguwamsu wato Malali, ko ta kan shopping bai biba yana zuwa gida daki ya fada, ya kwanta a kan gado tunanin Heenat ya hanashi sakat, irin haduwar da sukayi ya ke tunawa da irin laushin hannunta, da yanda take magana, wani mayen murmushi ya saki, a fili ya furta, I love you❤Heenat, haka ranan ya wuni cikin tunaninta ya kasa sakat in ya runce ido photo heenat ya ke gani da yanda take sarrafa jikinta, a zuciyar shi kuwa cewa yakeyi ya samu matar Aure don heenat ta hada duk wani abunda yake son mace ta hada.

Ban garen Heenat kuwa bayan sun shiga gida, da fushi tayi dakinsu, ko da sophia ta shigo, Aunty mardiya ta ke tambayanta mai ya mu Heenat don taga kamar, ranta a bace, sophia ta gaya mata yanda sukayi da wanda suka hadu dashi a Super Market, murmushi tayi ta gane dalilin, tace kyale Auntyn ku zata sauko, ko da heenat ta koma daki ta kwanta da niyar tayi bacci, itama tunanin guy din nan ya hana ta sakat haka tayi ta juyi da sake2 har lokacin sallah yayi haka ta tashi tayi sallah sannan ta nimi tsari da fadawa tarkon so irin yanda tasha wahala a baya, haka tayi ni sukuku, har dare yayi suna falo suna kallo a zahiri ita bakallon take ba tunanin ya rinjayi kallon har lokacin kwanciya yayi sukaje suka kwanta, da asuba ta tashi tayi sallah san nan tayi yan aikace akaicen da zatayi tayi wanka ta kuma ta kwanta, kasancewan asabar, idonta a lumshe photon wan nan saurayin take gani, harzuwa yamma tayi sallah la’asar kafin tayi wankanta atanfa tasa brown colour da surkin baki tayi kyau sosai, gashi dinki yayi dai dai da jikinta, falo ta fito, lokacin yan gidan suna kallon Sunnah TV itama guri ta samu ta zauna aka ci gaba da sauraron wa’azin Malam Tijjani Ahmad Guruntum Bauchi, yana nasiha akan alamomin Karshen duniya, wa’azin ya shigeta.

A ban garen Sani kuwa gari na wayewa ya tashi cikin farin ciki nan ya fara shirin, yamma nayi zashi gidan su Heenat don ya ganta, ko da yamma tayi ya shirya cikin galila shaddar sa yayi matukar kyau in ka ganshi kace wani sabon angone, ko da yashigo gida saida hajiyarsa tambayesa Auta irin wan nan wanka haka sai ina naga

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts