🐾🐾 Raheenat🐾🐾
🐾🐾08069420822🐾🐾
Rash Kardam💃🏻👈🏻
3⃣9⃣-4⃣0⃣
Abba ya kira sunanta, a sanyaye ta dago tana kallonsa, “Raheenatu, na yanke hukuncin, da ga yau zan karbe, duk SIM din wa yarki banson, wata alaka ta kara shiga tsakanin ki da SK ban yarda ki kara kiranshi ko daga wayansa kinji, kanta a kasa ta daga masa alamar eh idonta ya cika da kwalla a hankali ta sa hannu ta goge, Allah ya muku Albarka Allah ya sauya miki da wani wanda ya fishi Alkairi Ameen H Maryam ta amsa, yace kutashi kuje, da gudu, ta isa daki, kan gado ta fada kuka ta saki mai tsuma zuciya, Aimana ta zo ta rungumeta tana rarrashinta, itama kukan take ni kaina Rash, saida na zubda kwallah tsaban tausayi don rabuwa da masoyi ba dadi, cikin she shekan kuka, Aimana shikenan na rasa SK zuciyata shita ke so bazan samu kamarsa ba, Aimana tace in Allah ya yarda sai kinsamu wanda ya fishi, sai da sukayi kuka, mai isarsu kafin sukayi shiru, Heenat ta tuna da kala man Abba don haka ta kudiri a niyar cire SK daga zuciyarta, ko don tayi biyayya ma Abbanta, ta hakan ne zai san ya haifi yar da zaiyi Alfahari da ita.
A ban garen Abba kuwa ko da su Heenat suka tafi, abba ya kalli h maryam yace ina ga ta wanan hanyan ne ka dai zai ni santa Heenat da Sk kuma bana son tasan dalilin, H maryam tace kamin dai dai, Allah ya mata zabin Alkairi ya amsa da ameen. tun daga wan nan lokacin a ka ci gaba da shirye2 biki , Aiman tace ita baza tayi komai sai Walima, don bikin ma kamar a fasa takeji bata son ta tafi ta bar Heenat dinta, gashi har yanzu bata gama dawowa dai dai ba, ba wani taron da zatayi, yau ya rage kwana hudu biki, duk wanda ka ganshi murna ya keyi, H Maryam ma ba a bart a baya ba, don ta gyara Aimana, tsuminta ta hada mata bana wasa ba, su da kunta da kayan fruit ta shasu harta gaji, san nan ta sata a daki ta koya mata tunda ga yanda zata tashi mijinta a bacci salon shagwaba, gyaran gado, abinci na musam man, style din kwanciya, abun ba a cewa komai sai wanda yaji ya gani, Aimana ko har mamaki takeyi, lalle ba a banza ba Abba yake ji da Aunty maryam don ta hadu cikakiyar mace wacce ta amsa sunanta mace. Heenat ko tana kwace don jikinta na dan taba ta, haka akayi ta shirye shirye,
A bangare Sadde kuwa sun tsara event din da zasu dinner, launching, kamu lollipop day abun ba a cewa komai, “Sakina lokacin da ta samu Card Auren Sadde ba karamin mamaki tayi ba wai MY shi zai auri saddi hmm tace to Allah ya sanya Alkairi” na amsa da ameen,
Haka akayi ta sha galin biki, ranan jumma bayar an idar da sallah jumma’a aka daira auren Muhammad Yasir Muhammad da Amaryarsa Saddiqa Muhammad Ilelah Auren da ya tara jama’a da man yan manyan masu kudi, da yan siyasa da yan kasuwa, bayan nasu kuma Aka Daura Auren Aimana Muhammad da Angonta Jabir Abubakar, kowa ka gani sai farin ciki akeyi daga nan a ka dauko a marya sai Bauchin Yakubu, Yan bauchi kuma ana ta shirin zuwa wajen walimar Aimana kowa ya shirya har an fara tafiya da wasu, Aimana ne tashigo dakin ta hau kan gado ta yaye bargon da Heenat ta lulubu da shi, jikinta yayi zafi sosai sis ya jinki, cikin muryan jin jiki ta amsa da sauki, sannu kai ta daga mata alamar eh, suna haka h maryam ta shigo tace ma Aimana kiyi ki tafi kinga kar aje ayita jiranki, autny ni ba zani ba, sis ba lfy mai zanje nayi? aa bazai yiwuba an tara mutane sun zo dominki bai kamata kiyi haka ba baza su ji dadi ba, kuma zaki jamin magana, yanzu ma ya na kare, kunnuwata👂🏻na toshe, ganin ran Aunty Amarya ya baci yasa, ta tashi jiki ba kwari ta fita haka suka tafi gun walima.
Su Alhaji suna dawowa, side din da bakowa kowa yasa aka kai amare da man an gyarashi, su zauna kafin a yi ma amarya shere a gidanta da ke bayan
Friday, 3 March 2017
Home »
» RAHEENAT 39-40
RAHEENAT 39-40
Popular Posts
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(AUGUST 2016)* ...
-
MOTAR KWADAYI RASH KARDAM Duk launin kalan idonta, sun canza izuwa ja. Hannu tasa a tsakanin cinyanta tana mammatsewa,Bad Boy yana ga...
-
AMANA TA CE By ©Rash Kardam 1 Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassa...
-
🐾🐾Raheenat🐾🐾 1 Yarinya ce yar kimanin shekara 12 ta yanko a guje ta fada jikin Dad...
-
MOTAR KWADAYI By Rash Kardam 21-25 Jan motar yayi, suka bar cikin Silver Sand Hotel, bai zarce da su ko ina ba, sai gid...
-
BAZATA By ©Rash Kardam 1 Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan l...
-
π»π»π»π»π»π»π»π» ππ»BABBAN KUSKERENππ» ππ»DANA TAFKA ππ» π»π»π» ππ»ππ» ...
-
[6/5/6:30pm] 🌲RASH KARDAM🌲🌲 & 🎋SADEEY S ADAM🎋 ...
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(JULY 2016)* ...
-
π»π»π»π»π»π»π»π» ππ»BABBAN KUSKERENππ» ππ»DANA TAFKA ππ» π»π»π» ππ»ππ» ...
0 comments:
Post a Comment