🐾🐾 Raheenat🐾🐾
Rash Kardam💃🏻👈🏻
7⃣9⃣ -8⃣0⃣
Ki yi hakuri nima da kika gani Jameela daurewa ka wai nakeyi ace yata daya tilo wacce nake ji da ita, Adu’ah kawai zamu kara tsatantawa, Allah ya bayyanata, amma duk wanda nasan da sa hannunsa abatar, bazan yafe masa ba don ya ruguza mana farin cikin mu na shekara da dama, amma ba komai Allah na tare da mu, Allah ya bayya nata Ameen ta amsa cikin muryan rashin lfy, tashi yayi yafita ya nufi dakin Hajiya Suwaiba da sallama ya shiga ta na ganinsa, ta mike daga kwanciyar da take, sannu da zuwa, cikin kulawa tace Alhaji ya na ganka haka, karasa zama yayi yace ae dole, batar yarin yar nan yana so ya dawo min sabo don na daure amma haka kurum jikina ke ban zamiyi nasara za a sameta, gashi ciwon Jameela sai gaba yakeyi, lamarin sai dai Allah ya kyauta, cikin zuciyar suwaiba tace ba Ameen ba, afili kuma tace Alhaji ni dai da zakubi nawa da an hakura kawai yau shekara sha takwas fa, wani khafa yayi tare da mata wani mugun kalo, yace ko kin manta cewa ita kadai Allah ya ban duk abun da na tara ace banda magaji, kuma ko yanzu a wani hali take oho ban saniba cikin jin dado ko wahala, wasu hawaye ne suka zubo masa.
Waye Alhaji Ahmad Aliyu Yola
Alhaji AA Yola sha hararen dan kasuwa ne mai ji da nera a 9ja ciki da waje ba wanda bai sanshi ba, shine na daya acikin Masu kudin 9ja, daga shi sai Aliko Dan Gwate, wa yanda ake ji dasu ta fanni business, AA Yola, Allah ya azurta shi da kudi sosai, yana tare da Matarsa Kwaya daya Hajiya Suwaiba Wasiri, yar asalin yola ce itama, sun debi sheka bakwai da Aurw amma shiru ba lbr haihuwa, nan hankalinsu ya tashi, amma AA Yola duk da haka yana kwantar mata da hankali, kulum sai ta dameshi suje asibiti, Visa ya shiry ya suka fati Egypt don duba lfyta ko dasu ka je likitoci sunyi binci kensu sun tabbatar matsalar daga gareta ne bazata samu haihuwa ba, sabida zuciyarta ba zai dauki nauyi yaro ba, hajiya suwaiba ba karamin kuka tayi sosaiba, duk da haka bata daddara ba tace ma Alhaji suje Saudiya akara duba ta, bai mata musu ba, da ga Egypt suka wuce saudi, d same abudaya aka fada musu abban asibitin saudia, tun daga wan nan rana tashiga tashin hankali sosai amma AA Yola yace ta kwantar da hankalinta, ba zai kara aure ba, haka yayi ta lalabata har suka dawo 9ja.
Haka sukayi ta rayuwa cikin soyayya da kauna har suka samu 2 years bai taba nuna mata damuwarsa, suna cikin shekara na uku bayan dawowansu, Maman AA Yola, ta daga masa hankali sai daifa ya kara Aure don ita bazata ita zama bata jikanta ba, kulum sai ta masa magana amma sai dai yayi ta bata hakuri, data ga abun ba yibane, takirashi ko ya kara Aure ko kuma ta tsine masa, nan yashiga tashin hankali ba kadan ba, ko da yasamu suwaiba da magana, bata bashi wata matsalaba ta goya bayan yayi Aure ya bi “UMURNIN UWARSA”.
a san yaye yace mata shi ba zai iya zuwa nimar mace ba amma zai samu hajiyarsa duk yansa tace haka za ayi.
Ko da ya sanar da hajiarsa tace abu mai Saul ne a kwai kawarta, yar Niger ce Maradi sunyi zamar mutunci, kafin su koma Nijar amma suna waya da ita akai akai don haka ina ga yarta jamila zaka nima gata da kyau ga ilimi ga hankali, yace ma hajiya Jameela gidan Malam Ja’afar kike nufi tace ita fa, sau da ya danyi jim kafin yace shikenan, tace to kashirya sai kuje Kuma bana son abata lokaci zan yi waya da ita Maman Jameela.
haka ko akayi ko da sukayi waya, sun amince, ba bata lokaci sukaje Niger, basu samu matsala da Malam Ja’afar ya basa jamila akan sati mai zuwa za’a daura aure, kuma ya hutar dasu yin komai zaiyi sun yi godia, ko da sati yazo bata lokaci aka yi aure ya taho da amaryansa.
Hajiyansa da kanta ta hadasu dukansu, jameela da Suwaiba ta musu nasiha sosai, game d suyi zaman
Friday, 3 March 2017
Home »
» RAHEENAT 79-80
RAHEENAT 79-80
Popular Posts
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(AUGUST 2016)* ...
-
MOTAR KWADAYI RASH KARDAM Duk launin kalan idonta, sun canza izuwa ja. Hannu tasa a tsakanin cinyanta tana mammatsewa,Bad Boy yana ga...
-
AMANA TA CE By ©Rash Kardam 1 Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassa...
-
🐾🐾Raheenat🐾🐾 1 Yarinya ce yar kimanin shekara 12 ta yanko a guje ta fada jikin Dad...
-
MOTAR KWADAYI By Rash Kardam 21-25 Jan motar yayi, suka bar cikin Silver Sand Hotel, bai zarce da su ko ina ba, sai gid...
-
BAZATA By ©Rash Kardam 1 Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan l...
-
[6/5/6:30pm] 🌲RASH KARDAM🌲🌲 & 🎋SADEEY S ADAM🎋 ...
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(JULY 2016)* ...
0 comments:
Post a Comment