New Post

Wednesday, 1 March 2017

BAZATA PG 16

BAZATA 
                By
©Rash Kardam 
16                      
Duk jikinta rawa yakeyi, bakinta  na rawa, idonta ya fara fida hawaye:'(da sauri ta koma motarta  tana kuka, da hanzari ya biyota gun motarta, kafin ya karaso tayi ribas sai kura ta tayar ta bar gun da gudu kamar zata tashi sama, ganin irin gudun da takeyi ya razana don gabada ba gudun hankali takeba motarsa ya shiga ya bita hanyar auguwansu, ina tayi nisa sosai ko da ya iso bai ga alamarta ba, tsayawa yayi a kofar gidan, ya tamabayi mai gadi, ko Jiddah ta dawo? Yace tun dazu ta fita kuma bata dawo ba, hankalinsa yakara tashi, gidan su Dr Samar ya nufa cikin tashin han kali, ko da ya isa ya tar yana shi shin fita, ganin Dr ghali yasa ya tsaya kalonsa don baya hayyacinsa gaba daya, da sauri ya rike shi yace Dr lfy mai ya faru? Hannunsa ya kama ya shigar dashi dakinsa, ya zaunar da shi, ruwa ya miko masa maisanyi ya sha, ya ce ya kara masa, sai da ya dan nutsu kadan kafin Dr Samar ya ce mai ya faru na ganka haka? Idon Dr yayi ja yace Samar abunda nake gudu kenan gashi ya faru, Dr Samar yace mai ya faru? Nan ta kwashe lbr komai ya fada masa, Dr samar yace haba Ghali, pls be a man, abu kadan sai ka daga hankalin ka, ka yawaita adu’ah Allah yana tare da mu, in Allah ya yarda Jiddah malakin ka ce, cikin sanyin murya yace Ameen, haka sukayita hira Samar yana lallashinsa har dare yayi kafin suka rabu.
Jiddah na jan motar ta, gudu tarinka yi tana kuka, ta nufi gidansu Marsal ko da ta iso horn tarinkayi, harda na hauka, duk mai gadi ya rikice, cikin hanzari ya bude gate ta shiga gidan ajiye motar tayi ta fito da gudu tayi cikin gidan tana kuka, tayi sa’ar ba kowa, a falo, dakin Marsal tayi, tana shiga ta gansu da Sophia sun gama shiri zasu je gidansu Jiddan, jikinsu ta fada ta saki kuka, sosai take kuka duk ta ruda su, sai tambayar ta sukeyi lfy, cikin kuka Jiddah tace Lover asai Dr Ghali ne, ya cucen sai da ya samin sonsa na kamu zai min haka mai na masa da yake shiga rayuwata haka, ajiyar zuciya Sophia ta sauke tace Alhamdulilah na jima ina fatan haka, Allah ya amshi fatana, jiddah cikin kuka ta dago tace Sophia asai ba kya sona ke ma, tayi murmushi tace ko daya naga kun matukar dacewa ne shiyasa, marsal da sophia sukayi ta rarrashinta kuma suka gwada nata tayita adu’ah may be a kwai alkairin da Allah ya boye, sai magriba ta bar gidan ko da ta isa gida sallah tayi ta kwanta, nan feenat ta shigo, tazo kan gado tace sis kin dawo ko ki laiko ni, ko dai lover boy bai miki bane, nan idon jiddah ya kawo kwalla, ta fada jikin feenat ta saki kuka, feenat ta rarrashe ta kafin tace sis mai ya faru? Jiddah tace asai lover boy Dr Ghali ne, feenat tace ghali wanda kukayi ta case kwanaki tace yes, feenat tace wooow amma salon soyayyar ku ta burgeni, munsha rigima Allah ya sanya alkairi, jiddah ta zame jikinta, feenat ta mata nasiha kafin ta mata sallama ta koma dakinta, ta kwace taji karar shigowan sako tasan ghali ne da farko taso ta share amma zuciyarta ta kasa hakan, mika hannu tayi ta dauko wayan ga sakon kamar haka,
    My Jiddah
Ki yarda dani ina tsananin kaunarki, Allah ne ta jarabeni, ki sani in ba ke ba zan iya rayuwa ba, ki tausaya min dan Allah
  
       Urs 
           Dr Ghali
Har cikin zuciyanta taji tausayinsa amma gan gan jikinta ya kasa yafe masa, haka yayi ta turo mata sako kala2 da ta gaji kashe wayar tayi washe gari kin fita aiki tayi.
Dr Ghali kuwa tun da yaga Jiddah bata fito ba han kalinsa ya tashi, ya nufi pharmacy ya samu su marsal bayan sun gaisa yake tambayarta, ya jiddah lfy bata fito sukace suma basu sani ba don sun kira wayarta akashe amma suna ganin lfy ne, hakan nan suka dan yi hira da su marsal har suna tsokanan sa haka abun ya kasance, gaskiya sunji dadi wan nan hadi na Haughal, har cikin ran doctor yaji dadin sunan ya musu salama ya nufi office dinsa,
Jiddah ko sai da ta kwana biyu bata fi

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts