New Post

Wednesday, 1 March 2017

BAZATA PAGE 6

BAZATA 
               
By
©Rash Kardam 
  6
                   
Wacece Jiddah.
Alhaji Taneemu Musa hafafen dan garin Kaduna, nane a Abuja Road Magajin Gari, mutum ne mai kamata ga son mutane, ya kasance mutum mai saukin kai ga iya zama da jama’ah da wuya kaga fushin shi kulum yana cikin fara’ah, Yaya biyu Allah ya bashi su na farko Safeenat wanda suke kiranta da feenat mahaifiyar feenat Allah ya mata rasuwa tun suna Kaduna kafin su dawo bauchi, bayan rasuwar maman feenat ne Alhaji Taneemu ya samu transfer daga gun aiki zuwa bauchi, inda anan ya Hadu da hajiya Muslima ya Aureta itace uwar, Hauwa’u wanda suke kira da Jidda, H Muslima macece mai kirki da da’ah ta rike feenat riko mai kyau wanda ko uwarta ne ita yanda zata mata kenan ko kadan bata taba nuna musu ban banci ba, haka suka yi karatu yayinda feenat ta karanci business Administration, itakuma Jiddah tun tasowarta take son karatun Asibiti hakan ne yasa taje tayi karatun medicine dinta a Mai duguri, bayan ta dawo ne ta samu aiko a ATBU Bauchi, tana ban garen pharmacy, haka suke rayuwansu gwanin burgewa ko ina zaka gasu tare, feenat tana da saukin kai kuma bata da wani girman kai gata da sanyi sosai, sabanin Jiddah da take da zafin zuciya abu kadan ta hauro bata son raini kuma bata raina babba don bata son amata, kuma ita bata cika kula sabgar maza ba, ita bata kula kowa damuwar ta takeyi ita, wan nan shine ta kaitacen lbr Jidda.
Kwanaki sunja yau sati guda, yaune ranan daurin Auren Suhana da Angota Saleem kalo daya zakayi ma kawaye da angwaye kasan suana cikin farinciki suna taya yan’uwansu kuma abokan aikinsu murna, su jiddah, Marsal Sophia sam basu samu zama ba sune manyan kawaye, yanzu haka sun tafi Zungur, Villa Garden, yara gurin da za’ayi walima sun gayyato Malama Asmart Adam Dan Fulani, ita zata gabatar musu da wa’azi game da rayuwan Aure guri ya tsaru sosai, sun kuma ajiye komai a inda ya kamata, kafin suka dawo gida don yin wanka su shirya don lokaci yayai, haka suka dawo sukayi wanka tare da Sallah la’asar, kafin suka shirya zuwa gun walima gaskiya su jiddah sunyi kyau bakadan ba, ina ce zan tsaya tsara muku kyan da sukayi to zamu kwana mu yini ban gama ba   abokan ango ne suka turo motoci aka jidi yan’ walima aka kaisu, bayan sun gama isa, Malama Asmary ta soma yin nasiha gameda zaman Auren duk wanda ke gurin sai da yaji nasihar ta shigesa, a haka sukayi taro aka watse,koda suka maida Amarya gida, kafin azo a kaita gidanta, Jiddah tace zata tafi gida tayi shirin Dinner faga gida zata zo tunda Zindaba Hotel za’ayi haka ko akayi, nan tayi sallama wa Marsal da Sophia ta tafi.
Ko da ta isa gida lokacin ana kiran Isha sallah tayi kafin taci abunci, taje dakin Abba da sallamarta ya amsa tashigo, niman guri tayi ta tsuna ta gaida sa ya amsa cikin fara’a, tace Abba nazo rokon Alfarma ne, yace fadi Autar Abba nan tace masa tana son taje Dinner Suhana ne, sai da ya jin jina kai kafin yace Jiddah da bandun yanda kuke da Suhana ba, gaskiya da na hanaki fita banson kiyi nisa baran ma fitan dare banaso, yace amma kije Allah ya kare min ke, kuma kema ko kula da kanki tace in Allah ya yarda yace Allah ya miki Albarka tace Amin, dakim H Muslimah taje ta shaida mata tafiyarta kuma Abba ya barta, itama ba wani so takeyi ba ta amsa mta da sai ta dawo, dakinta takoma tayi wanka ta tsaya tsara kwaliya tayi kyau sosai kafin ta dauko kayan Dinner wani gown ne, Green da ratsin milk bakaramin kyau tayiba, ta dauko humranta ta feshe jikinta dashi, san nan ta sake dauko turarenta, Essences of love  ta fesa dan karamin bakinta yaji jan baki, ga man yan idanunta masu fisgan mutum, gaskiya ta zuba kyau sosai, tafito sannu a hankali take tafiya, H Muslima tsayawa tayi tana kallon diyarta gaskita Allah yayi halita agun ga kyau, ko da ta fita motarta tashiga ta tada, ta dau hanyar Zindaba Hotel, tafe take ahankali, lokacintar

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts