BAZATA
By
©Rash Kardam
9
Bata san lokacin da ta fadi kasa sumamiya ba, dariyan mugunta suka sheke da shi, wanda sai da yasa na razana, daukar ta sukayi, suka soma tafiya da ita, sanyin dake gurin shi ya dawo da ita daga sumar da tayi jinta hanun mutane yasa tasaki ihu ta rinkayi gwar gwadon karfinta, tasoma kiciniyar kwacewa amma ta kasa sun mata riko mai kyau, gani turjewa ba zai ficetaba yasa, suma kiciniyar tsugunawa kasa, laluben dutsi take, cikin sa’a ta samu mai girma lokacin sai janta sukeyi, fakan sa tayi ta kwada masa dutsi ta sa gudu, sosai take gudu hanyan titi, tabi sosai take gudun kamar kafar ta zai fita, suma suna binta, sai da sukayi gudu sosai kafin ta iso titi ai nan tasoma ihu ta na neman tai makon jama’ah, sam bata lura da motar police da tayo ta gun ba gudu take sosai, sai jin kiii nayi sunta ka burki cikin zafin nama, aeko nan ta kara sakin kara.
Dr Ghali ke kwance a daki da Jiddah ta fita sai faman lumshe ido yakeyi, kamar wanda aka mintsiresa ya mike yana tambayan kansa, anya nayi ma Jiddah adalci? In barta tana mace ta fita kuma ita daya a daren nan ti in wani abu ya sameta nice silla, sai ya tsinci kansa da jin haushin kansa, cikin han zari ya mike ya nufi motarsa, ya shiga sai alokacin ya kunna wayarsa,ya bude gate ya fita, ae ko bai yi nisa ba wayarsa ta soma ringing Dr Samar ya gani cikin hansari ya daga, Dr Samar cikin zafin rai ya soma maga Ghali ka kyauta kuwa ka dauki yar mutane mai zakayi mata a dare ka tafi da ita ka daga hankali iyayenta da mu, ko ka manta ita macece? Cikin sanyin jiki yace gaskita ban kyauta ba, Dr Samar yace tana ina, yace dazu ta tafi, cikin razana yace what? Kasan bata dauko motarta ba adaren nan ka barta tafita yanzu in aka saceta fa?,nan ya kara rikitar da Dr Ghali kashe wayan yayi ya soma gudu dai dai zai bar layin gidan yaga wasu mutane su biyu zasu shiga wani katon gida da alama masu gadi ne, horn yayi wanda ya sasu tsayawa, shima ya fito a motar sa yazo hunzu, ya rusuna ya gaidasu suka amsa yace baba dan Allah ko kunga wata bidur wan yariya ta wuce tanan, dayan yace bamu dade da jin wata yarinya ta fito tana gudu tana ihu da alaman wasu sun biyota, kuma ba mutum daya ba don muryoyisu da yawa, da gabaya kuma muka rinkaji ihu sosai, daga baya kuma muka daina jin ihun, dayan yace Allah yasa dai ba su keta mata haddi ba inji dayan,Dr Ghali ya dafe kansa, da sauri ya shiga mota gudu yakeyi sosai, ya karade duk inda ya duba a fadamar mada, ba alamar jiddah idonsa ya kawo kwalla, tabbas ni ghali na cika azzalumi maras kirki, na cuci Jiddah mai yasa naksa hakuri lokacin da ta juye min multina, wayan Dr Samar yasake kira yace kuna ina yace gamu a dai dai Rank Road zamuzo fadamar Mada, yace nima na fito ina kusa da inda kuke, Dr Samar yace kaga jiddah yace ko daya sai ya basu lbr da wayan nan mutane suka bashi, Samar yace Innalilahi wa inna ilaihi raji’un, wlh ka cuci Jiddah yanzu a wani hali take, Ghali yace gani isoa gunku.Ko da ya iso su Saleem da Samar sun masife shi sosai, kuma yayi dana sani abunda ya aikata ma jidda daga nan suka yanke shawara zuwa su sanar da iyayenta daganan su wuce police station, suyi report, hanyan Federal low cost, Zamani Area suka nufa ga dare yayi gashi suna cikin tashin hankali.
Jidda ko jin karar mota yasa ta kara rikicewa ta saki ihu da sauri wani matashin dan sanda ya fito da toci yana haska jidda da take ihu dai dai nan Wayanda suka biyota suka ga yansanda, nan suka juya zasu gudu sauran police dinsuka bisu, gudu sukayi sosai amma basuyi sa’ar kamasu ba, hakan yasa suka dawo, Sajan Nasir yace ke mai yafito dake cikin dare cikin muryan kuka tace Sir kamin afuwa ku kaini gida wlh zan fada muku ko miye don nasan babana yana cikin tashin hankali, yace bazan kaiki ba sai kin gaya min mai ya fito da ke, cikin muryan kuka ta bashi lbr, ya jin jina sannan yace zan kaiki gida, yanzu amma da ga yau
Wednesday, 1 March 2017
Home »
» BAZATA PAGE 9
BAZATA PAGE 9
Popular Posts
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(AUGUST 2016)* ...
-
MOTAR KWADAYI RASH KARDAM Duk launin kalan idonta, sun canza izuwa ja. Hannu tasa a tsakanin cinyanta tana mammatsewa,Bad Boy yana ga...
-
AMANA TA CE By ©Rash Kardam 1 Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassa...
-
🐾🐾Raheenat🐾🐾 1 Yarinya ce yar kimanin shekara 12 ta yanko a guje ta fada jikin Dad...
-
MOTAR KWADAYI By Rash Kardam 21-25 Jan motar yayi, suka bar cikin Silver Sand Hotel, bai zarce da su ko ina ba, sai gid...
-
BAZATA By ©Rash Kardam 1 Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan l...
-
[6/5/6:30pm] 🌲RASH KARDAM🌲🌲 & 🎋SADEEY S ADAM🎋 ...
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(JULY 2016)* ...
0 comments:
Post a Comment