🐾🐾 Raheenat🐾🐾
Rash Kardam💃🏻👈🏻
5⃣1⃣-5⃣2⃣
Da sauri ta sha gabansa, ya kauce jakarsa ta rike, wani mungun kallo ya mata, bashiri ta saki, cikin murya kuka, tace haba MY ko ba komai ae ya kamata ka fada min ko ka manta ni matar kace, yana da kyau insan inda zaka baran ma barin gari zakayi, nan da nan tausayin ta ya diran mishi, amma sai ya dake yace kauce min a hanya, kuka ta kara sauti, ganin bada niyar dainawa kuma zata bata mata lokaci yasa, yace ya isa haka, shiru tayi, a sanyaye yace mata Kaduna zani, zaro ido:oops: mai zakaje yi Acan? Kallon ta yayi yaga tsan tsan kishi a idonta, aiki zanje yi kwana2 zanyi in dawo, to shine bazaka ce in shirya mutafi ba, ya ce hakan ne bai taso ba don ba daddewa zanyi ba, san nan banyarda ki fita ko gate ba harsai na dawo, to tace ya wuce ta gefenta yafita ko yar adawo lfu, bata iya fada ba tana komawa cikin falo kan kujura ta hau tacigaba d chart dinta,
📢📢📢📢
Kira garemu yan’uwa mata kulura da wani abu Namiji tamkar rakumi🐪 ke ce a kalan da zaki ja shi matsawan kin san me kike, namiji yana son tarairaya da nuna kulawa, a koda yaushe zai fita ki rako shi har kofa ki masa Adu’o’in Alkairi da na kariya, kin ga anan riba biyu Allah ya kare shi, san nan ya kumaji karin sonki❤ a zuciyarsa don namiji yana son mace da zata na yawan ta masa fatan Alkairi, san nan tsafta babban a bune, ki yawaita tsabtace jikin ki da muhalli, iya girki namiji nason kina jiyar da shi dadi kalolin abinci🍝🍛🍲 ya na daya da ga cikin abunda ke kara dan kon So da Kauna❤,Yan uwa mata🙍🏻👰🏻💁🏻 kurike wan nan.
MY na fita motarsa ya shiga hanyar Kano ya dauka don ta kano yake sin shiga hanyar tafi kyau gudu yakeyi sosai, ya sanya Kira’an Ahmad Sulaiman, yana bi, sai misalin 3:24pm ya iso kano Sallah yayi kafin ya shiga kasuwa tsara ba yasaya sosai kafin ya dau Hanyan KD, tafe yake yau wani irin farin ciki yakeyi wanda shi kanshi ba zai iya misaltawa ba, yau zaiga Heenat kanwarsa wanda yake jin wani irin so yake mata na daban wanda in ka dauke Allah da manzon sa, sai iyayensa, to sai Heenat ya ke, jin irin wan’nan Son❤ fuskanta ke masa yawo a kawayar idosa, sannu a hankali yake tafiya harya iso garin Kaduna lokacin ana kiran Magriba don yayi gudu sosai, wani Masallaci ya samu a bakin titi ya parking yai alwala kafin ya ga batar da sallah sa bai bar gurin ba sai da a kayi isha’i, kafin ya bar masallacin, Restaurant ya nima ya cika cikin shi da abunci🍛 kafin ya soma tunani yanda zai nufi gidan Aunty Mardiya.
Sai da yaga gari ya soma duhu kafin ya mike jiki ba kwari ya nufi hanyan Unguwan Sarki, da tambaya Har ya iske gidan ko da ya iso gate din gidan ko Dad din su sophia shima ke shirin shiga gidan, Horn ya masa, dad din sophia na gani an masa horn ya tsaya, sai da MY ya fito har yazo dad da motarsa kafin shima ya fito hannu ya mika masa suka gaisa, da alamun Dad di sophia bai gane shiba, cikin sanyi nurya yace baka gane ni ba ko, eh ya amsa masa kafin Yace Muhammad Yasir ne daga bauchi yana fadan haka murmushin ah! ah! Mutane India yaushe kashigo garin, kai ya dan sosa kafin yace ban dade ba da zuwa munzo wani aiki ne na kwana 2 shine nace barin sauka a nan, madallah yayi kyau ka kyauta Allah ya bada sa’a Ameen, sa mai gadi yayi ya wan gale musu gate suka shiga da mutarsu🚘🚙 duka cikin gidan, dakin baki maza ya kaishi wanda sai ka shig falo tage fen side din Dad din sophia, aka masa masauki, yana shiga gida ya tarar da su Heenat sun kwanta, Aunty Mardy ya sanar mata da zuwansa, bakara min mamaki tayi ba kasancewa H Maryam bata fada mata ba don wayarta na
Friday, 3 March 2017
Home »
» RAHEENAT 51-52
RAHEENAT 51-52
Popular Posts
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(AUGUST 2016)* ...
-
MOTAR KWADAYI RASH KARDAM Duk launin kalan idonta, sun canza izuwa ja. Hannu tasa a tsakanin cinyanta tana mammatsewa,Bad Boy yana ga...
-
AMANA TA CE By ©Rash Kardam 1 Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassa...
-
🐾🐾Raheenat🐾🐾 1 Yarinya ce yar kimanin shekara 12 ta yanko a guje ta fada jikin Dad...
-
MOTAR KWADAYI By Rash Kardam 21-25 Jan motar yayi, suka bar cikin Silver Sand Hotel, bai zarce da su ko ina ba, sai gid...
-
BAZATA By ©Rash Kardam 1 Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan l...
-
[6/5/6:30pm] 🌲RASH KARDAM🌲🌲 & 🎋SADEEY S ADAM🎋 ...
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(JULY 2016)* ...
0 comments:
Post a Comment