🐾Rash Kardam💃🏻👈🏻
🐾🐾 Raheenat🐾🐾
Rash Kardam💃🏻👈🏻
4⃣3⃣-4⃣4⃣
Sai kusan asuba ya kyaleta, tabbas ya ji dadi don Sadde ta rike mutuncin ta, duk iya duniyancin ta, bata sake ta zubar da mutuncinta ba, bayi ya shiga yayi wanka kafin ya hada ma sadde ruwan zafi,taje tayi wanka ta gasa jikinta, kafin ta fito har ya gyara gadon,su ka kwanta da gari ya waye Aunty Maryam ta musu kayan breakfast mai kyau ta ba ma driver ya kawo musu, MY yaji dadi, haka suka gudanar da Amarcin su, MY ya na tarairaya Sadde amma.sam.sadde bata iya yar shagwa ba da kisisi nan nan ba, shiko ya na son mace mai shagwaba.
📢📢 kira gare ku Yan’uwa Mata yi wa mazaje shagwaba, ba karamin tai makawa ya ke gurin kara soyayya maza suna son mace mai iya shagwaba mu kulla kar ki ga ko kin gir ma ki tarairayasa, ki masa kalaman da zai sanyaya ziciyarsa, ya wan yi masa Adu’ah da fatan Alkairi, ya na kara soyayya.
Haka sukaci gaba da rayuwan Aurensu tun a sati na biyu ya fara fuskanta matsala da sadde don ko kadan bata iya girko ba, bare a kai ga ta sa hannu ta gyara daki, nan ta fara ko rafi a kan sai dai su dauko yar aiki, da farko ya ki amma da yaga ta dage sai ya amince ba dan yaso ba, don shi bai cika cin girkin kowaba, ya na son yawan tsafta don zaka ga komai nashi tsab tsab, yau ta kama asabar yan’uwan hajiya murja ne suka zo gidana, sun dade a falo kafin ta fito a wulakance ta kalle su, ta na wani yatsina tana cika ta na basewa, zuwa tayi ta zauna ta daura daya akan daya, ta na kada kafa, baki suka sake suna kallon ikon, Allah, a wula kance ta kalle su tace daga ina, wan ta juya ta kalli wan nan ina Kulu ne ta yi karfin halin cewa Yayen Maman Muhammadu ne Maifiyar Mijinki, oh tace san nun ku, su ka amsa da yauwa, tace da kun dan zauna a kasa kar, kusa min dati a kujera na don sabi ne, kuma naga kamar jikin ku bai samu wanka sosai ba, Baba Jimmai t mike, ke kinsan masu wa kike fadan maga nan nan? Ai ko ba iyayen Muhammadu ba, bai kamata ki mana haka ba, a mulakance ta kallesu mai na muku Mtsss ta ja tsaki halina da gidadawan kauyawa ke ban, Inna Jimmai tace hmm lalle kan zata gwada ma na ita yar ” ZAMANI” ne, baba asabe tace ku tashi muta fi, suna futa ta sake tsaki, abinda ba zai yuba ke nan don banson in ga wani ya rabi MY dole in dau mataki a kansu.
Ko da suka isa gida su ka samu H Murja a daki su ka gaya mata komai, bata dau maganan su da muhimman ciba sai take ga kamar yan’uwanta suna son su hadata da “SURKARTA” ne ko hassada suke so su mata gashi ance ubanta hamshakin mai kudi ne, nan ta sha shantar da magana ta nuna musu halin ko in kula, abun ya kona musu rai ba shiri suka tattara yana su ya nasu suka koma kauye,
Heenat ko haka ta yi ta jinya daga karshe ta fauwala ma Allah komai, tacigaba da zuwa Islamiyarta, h maryam ko taci gaba da kula da yarta,
Ban garen Aimana tun da aka kaita kusan kullum sai sunyi waya da Heenat, haka rayuwa taci gaba da gudana, dadi da ba dadi san’nan duk wata mu’amala da ta san da ta hada ta da MY kauce shi takeyi, bata shiga saggar kowa da muwarta rakeyi, Yanzu H Murja ce ta matsa mata kullum cikin ha baici ita H Maryam, ko kadan bai da munta abunda tasa a gabar ta shi takeyi, kamar kullum ita taso da ga islamiya gida take dawow, tun a hanya ta lura da wani mai jan motar d ke bin ta, sauri ta kara harta iso gida ko da tashiga bata sake bi ta kanta ba, shiko yana ganin gidan da tashiga, ya fito a mota ya samu mai gadi, ya tambaye sa yarinyar da tashiga, Mai gadi yace Raheenatu ce yar Albarka nan, yaji dadin ya bata da yayi nan ya dan masa tambayoyi game da ita bai samu wata aibunta ba nan yayi godiya, yace masa sunansa Mukh
Friday, 3 March 2017
Home »
» RAHEENAT 43-44
RAHEENAT 43-44
Popular Posts
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(AUGUST 2016)* ...
-
MOTAR KWADAYI RASH KARDAM Duk launin kalan idonta, sun canza izuwa ja. Hannu tasa a tsakanin cinyanta tana mammatsewa,Bad Boy yana ga...
-
AMANA TA CE By ©Rash Kardam 1 Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassa...
-
🐾🐾Raheenat🐾🐾 1 Yarinya ce yar kimanin shekara 12 ta yanko a guje ta fada jikin Dad...
-
MOTAR KWADAYI By Rash Kardam 21-25 Jan motar yayi, suka bar cikin Silver Sand Hotel, bai zarce da su ko ina ba, sai gid...
-
BAZATA By ©Rash Kardam 1 Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan l...
-
π»π»π»π»π»π»π»π» ππ»BABBAN KUSKERENππ» ππ»DANA TAFKA ππ» π»π»π» ππ»ππ» ...
-
[6/5/6:30pm] 🌲RASH KARDAM🌲🌲 & 🎋SADEEY S ADAM🎋 ...
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(JULY 2016)* ...
-
π»π»π»π»π»π»π»π» ππ»BABBAN KUSKERENππ» ππ»DANA TAFKA ππ» π»π»π» ππ»ππ» ...
0 comments:
Post a Comment