🐓🎄🎄🎄🐓🎄🎄🎄🐓
DAI-DAI RUWA
DAI-DAI GARI
(DON'T EXPECT TOO MUCH
IN
LIFE)
🐓🎄🎄🎄🐓🎄🎄🎄🐓
NA
©RASHIDA .A. KARDAM
Bismillahi rahmanu rahim,tsarki ya tabbata ga Allah ubangiji talikai, mai jinkan bayinsa idan yaso.
Ya Allah ina rokonka yanda na fara rubuta wannan gajeren labari kabani ikon isar da sak'o acikinsa Ameen.
SHARHI
Wannan labarin k'agaggene, nayi shine bisa yanda rayuwa ke tafiya, da abubuwan da suke gudana a cikinta.
Ma'anar Littafin shine, karka dau buri ma kanka, ko ka kai kanka inda Allah bai kaika ba. Da yawa su a wannan rayuwan, suna kalon abunda yan'uwansu ke dashi, ko suka mallaka, suma su saka ma ransu dole sai sun samu. Irin haka sai kaga mutum ya fada halaka ko yana danasanin aikata wasu abubuwan da yayi. Allah yasa mu dace Ameen.
Pg-1~5.
Sauri-sauri ta kai ruwa bayi dontayi wanka, kar ta makara zata fita zuwa gun tafsir, din da Malam Isa Ali Pantami ke gabatar wa, a masallacinsa dake Federal low cost. Bata dad'e sosai ba tafito d'aure da zani a k'irjinta. Wani k'aramin zani ta d'auko, wanda ta barshi na tsane jikinta, in tayi wanka.
Ta gyara jikinta, tare da shafa mai mai laushi. Dogon riga ta d'auko ta saka, bata tsaya yin make-up ba, kasancewan Rahmadan ne. Hijab ta d'auka ta saka, tare da d'aura nikaf akan fuskanta. Ko da na kalleta ta fito ustaziya sak, cikin nutsuwa ta tako zuwa d'akin Ummi, tace"Ummi na tafin gun tafsir d'in. Ummi cikin muryan mace mai kamala da mutunci tace"Allah ya kare ya bada sa'a.
"Allah yasa ku amfana da abinda zakuji.
"Sai kin dawo d'iyata.
Cikin ladabi Hameeda ta amsa da "Ameen Ummana".
Ko da ta fito gidan su Khairat ta shiga da sallamanta, Maman Khairat ta amsa mata tare da cewa"a'a Hameedah ce?.
"Ki shiga k'awarkin na ciki, yanzu nake mata fad'an ta shirya zaku makara.
Da fara'arta tashiga d'akin su Khairat, tare da Sallama.
Khairat tace"shigo k'awas, Hameedah ta harareta tace"ni kiyi sauri kar mu makara banson a wuce wallahi.
Khairat tace"kafin mu tafi ga kayanda Anas ya kawomin na Azumi ki bud'e ki gani.
Wasu manyan laidoji Khairat ta tara ma Hameeda a gaba, take ta fara bud'e kayan wasu manyan madara ne guda 2 da gwan-gwanin Ovaltine guda 2, sugar yar kwali guda 5, ga catoon d'in indomee kitchen guda 2 manya. 'Daya laidan kuwa kayan chocolate ne iri da kala ga cake masu jida kyau aciki. Sai crete d'in k'wai guda biyar, ga sabin kud'in wanda inaga zai kai 5k. Nikaina Rash sai da na yaba kayan.
Hameedah ta mata murna da yaba kayan, cikin zuciyarta ko cewa take"gaskiya Khairat tayi dacen saurayi mai k'ok'ari.
Wata b'an garen zuciyarta ko cewa take"hmm yanzu halane Haisam ya miki kamar wannan.
Wata zuciyar tace"bakiga shi baida k'arfi sosai, baikai Anas ba.
Muryan Khairat ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta lula.
Suka fita suka nufin gun tafsir, suna yan hiransu. Awansu d'aya aka tashi a tafsir suka nufo gida, Hameedah ta na shiga gida, Hijab ta cire ta fara gyara musu shinkasa tare da had'a wutan abinci.
*DEDICATED TO*
*MY FANS*
*AS HAPPY SALLAH*
0 comments:
Post a Comment