New Post

Saturday, 11 February 2017

ZAMAN MAKOKI PAGE 21-25

🍧🍹 *ZAMAN MAKOKI*🍹🍧

                  *Na*

*Rash Kardam*
          *Ummieluff*

  Page
*21~25*

Haushi ya yasa Anush ta wanka mata mari mai lafiya Candy ta ce “kutumelesi cabd'i yau ba zan yarda in kuma na yarda na dan k'are anan guri".

Kafin Aneesa tayi wani yunk'uri tuni Candy ta d'agata sama ta nuna kafin ta makata a k'asa ta d'ale ruwan cikinta Candy sai jibgar Aneesa ta ke kamar ta samu jaka. Ihun Aneesa ne yasaka Mamanta fotowa da sauri tana fad'in “lafiya Aneesa mai ya same....". Kasa karasawa tayi ganin Candy a kan Aneesa tana jibgarta da sauri Maman Aneesa ta nufo su Candy na nagin haka ta tashi da gudu tayi k'ofar gida ta rik'e k'uugu ta ce“Aneesa kalli nan wuuuu!". Ta mata gwalo ta ce“ehe naci shinka fa na more haushi ya kasheki.

Ran Maman Aneesa in yayi dubu ya b'aci ta kalli Candy ta ce“kanda kike ko wa naga fitsaranki ya soma yawa fa". Candy ta kyalkyale da dariya ta marairaice murya ta koyi yanda Maman Aneesa tayi magana ta ce“lah kuji bata iya fad'a ba wai Kanda hahaha!!!". Ta kece da dariya ran Maman Anee ya k'ara kufula ta juya zata duba bulala Candy ta lallab'o tazo ta zuba ma Aneesa dun-du tare da mari ta yanka aguje tayi k'ofar gida ta mata gwalo ta ce“na daki banza aha gobe ina zo cin shinkafa mutum ya hanani ya gani in masa wanda yafi na yau". Ta sake gwalo ta fita da gudu Maman Aneesa bak'in ciki y isheta tamkar ta kurma ihu ta ce“Aneesa d'auko gyaleki yau gidansu Kanda zamuje Aneesa ta ce“to Mama amma sunan ba Kanda ake cewa ba Candy ne kinga har tana kwaikwayan maganarki".

Wani tsawa Maman ta daka mata ta ce“rufe min baki sai yanzu kika iya maganan nan ina ta dakaki in banda ihu ba abun da kike mana kin kasa ramawa mtsss!!".

Fuuuuu Maman ta fita Aneesa ta rufa mata baya zasu kai k'aran Candy.

Candy tana fita bata zarce ko ina ba sai gun carafke da nan suka fara carafke yayi dad'i Candy ta nason cin gyad'a ta mik'e ta ce“tun d'azu sai cinyeki nake tunda 'yar bashi muke yi dan haka a gyad'anki zan fanshe bashi na". Kafin ya rinya ta mik'e Candy ta d'ibi gyad'a tasaka gudu tamkar k'afanta zai tab'a keyarta.

Sai da tayi nis sosai ta zauna akan wani hakali ta fara cin gyad'anta tana 'yar wak'a ta sai da ta cinye ta ce“yanzu ina zn a nufa? Gashi yau ba wani Gidan da ake ```ZAMAN MAKOKI``` bare naje". Wata zuciya ta ce“ki koma gida kiga halin da Ummaki ke ciki sai ki d'an taya ta aiki ma". Murmushi tayi ta ce“Allah sarki Umma na kina sona nima ina k'aunarki Allah ya bani kud'i in gina miki k'aton gida kaman Garin Bauchi.

       *```TAGWAUEN MARUBUTA```*

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts