New Post

Saturday, 11 February 2017

RUWA CIKIN COKALI.... PAGE 31

°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•°
    _(Ya ishi mai hankali wanka)_
*{BASED ON TRUE LIFE STORY}*
                *(AUGUST 2016)*

                          *NA*

*®Rashida .A. Kardam*
       
*N. W. A*
Page
*31*

BAYAN SHEKARA GOMA.....
_Wata Mata na hango tare da 'yan yaranta mata su biyu sun fito daga mota zasu shiga babban Asibiti Murtala dake garin Kano cikin tafiyan mace mai hankali suka shiga sun duba marasa lafiya tare da raba sadaka a Asibitin sun zo fita daga ward d'in kenan taji wata na kiran ta "Kdey! Kdeey!! Kdeey!!". Da sauri ta juya sam bata gane ta ba har ta juya zata tafi matan da ta kira ta tace"_
_Kdeey baki ganeni bane Samy ce fa". Cikin zare ido Kdeey ta nuna ta da yatsa ta ce"Aunty Samy kece haka?". Samy ta fashe da kuka ta ce”nice dan Allah ki yafe min nayi watsi da shawaranki kinga yanda Allah ya mai dani akan lesbian (mad'igo) kowa ya gujeni yanzu tsutsotsi ke fita daga gabana ga warin dana keyi a yanzu nayi nadama tabbas na yarda da kalman da hausasa ke cewa *RUWA CIKIN COKALI*_ ```ya ishi mai hankali wanka har ma ta sha yayi saura".``` _Ta had'iyi yawu ta ci gaba da cewa"Soby kam ma ta mutu Zeena ta kamu da k'anjamau ga ni ni kuma rayuwa ta ta kare a wulakance yanzu nayi nadama na tuba".  Ajiyan zuciya Kdeey tayi jikinta duk yayi sanyi tace"Allah ya yafe mu baki d'aya". Cutie ce tazo da gudu ta ce"mummy kinga Manshat na tsokanata". Samy ta kallesu ta ce"wa'yan fa yaranki ne?".  Kdeey ta ce" wannan Cutie sunanta d'ayar kuma Manshat". Samy ta jin-jina kai nan Kdeey ta bude jakanta ta d'ibi kudi masu yawa ta ba Samy suka mata sallama ta nufi mota gun Sojanta suka nufi gida._
         *TSOKACI*
```'Yan uwa ina fatan kun gane sak'on da ke cikin littafina mai``` *RUWA CIKIN COKALI* ```sannan ba wai akan masu lesbian darasi ya tsaya ba ya shafi Iyaye da yanda samu saka ma yaran mu ido a cikin littafin na  a gida hudu ku ga kowanne da yan yake tafiyar da tarbiyansa da kula da yara kusani yaran zan zu sai an had'a da samusu ido.  Yana da kyau iyaye asaka ido ma yara sosai asan dasuwa take kawance mai take shiga dashi mai take fita dashi bincika waya don waya yana d'aya daga cikin gin shikin lalacewan yara musamman masu hawa social media irinsu 2go, Whatsapp, Istagram, Facebook, zaka samu a kwai group na batsa da suke bud'ewa. Sai wasu amare su kan kalli blue fim da niyyar samun ilimin jima'i, tun tana ganin mace da namiji na yi sai kuma a nuna mata, daga nan kuma yarinya za ta fara tunanin yi. Maginin abu kar a fara, ke uwa ki lura da yarki sosai, kada ki sake yarki da kawa su kulle kansu a ɗaki har tsawon lokaci da sunan suna hira. Ke kuma wai wayayyiya ki ce kin ba su "privacy" ɗinsu, boko ko wayewa ba hauka ba ne, ba mu san ka ba ɗa yancin yin abinda ya ga dama ba. password gudun karta boye abu maras kyau bincika kayan yara duk yana tai makawa. Iyaye mata yawanci akinan akan mu yake don mu muka fi zama da yara iyaye maza masu fita ne daga lokacin da ka tsaya akan danka in ya taso cikin kamala da nutsuwa zakaji ana na ubane in ya baci kuma na uwane dan Allah mu dage mukula kusani yayan nan amana ne a gun mu kuma wallahi Allah sai ya tambaye mu akan su. Ya Allah ka kawo mana dauki kashiryar damu da yaran mu.```

         *ALHAMDULILAH*
Nan na kawo k'arshen wannan littafi mai suna *RIWA CIKIN COKALI* kuskuren danayi ya Allah ka yafe min.

      *SADAUKARWA*
Na sadaukar da wannan littafi ga sis *KDEEY 'N' MRS AL'AMEEN*

*WANNAN LITTAFIN TUKUICI NE GA*

DUKAN GROUP DINA NA *RASH KARDAM HAUSA NOVEL*.

Masoya da yan uwa ina kara godiya Allah ya bar k'auna taku a kullum *RASHIDA A KARDAM*

```Sai kun jini a sabon littafina mai suna``` *```GIMBIYAR KARDAM```* wanda na canza sunan i zuwa *```RASHEEDAH TA```*  yanan tafe ba da dad'ewa ba.
_Mashaa Allah Alhamdulilah!!!._

```Wa'a kulu k'auli haza astagafirullahaliy wa lakum.```

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts