New Post

Tuesday, 7 February 2017

MAYAUDARA PAGE 60-65

[6/8/2:00pm]

💖BEEBAHLUV 💖
              &
🌲RASH KARDAM 🌲
           WITH
🎋SADEEY S ADAM 🎋

🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
      MA'YAUDARAH
    🌺🌺🌺🌺🌺🌺
            60~65

        Dinner tayi dinner anci, ansha, kuma anci uban nera don kuwa tayi kuka sosai,, ba a tashi ba sai karfe sha biyu na dare, amarya kam tayi farin jini kuma tayi bala'in kyau, kowa yabon ta yake kamar wata Queen,, abokan shi kuwa sai yabon ta suke suna cewa  yayi dacen mata, yakan ji dadi a lokacin da aka yaben ta, shima tana birge shi kuma yakan ji wani abu a zuciyar shi sai dai kuma kome yake tunawa sai yaji yatsane ta.

       Angwaye sun maida amare gida akan zuwa gobe za a zo daukan amarya, a mota ango yakan dan janta da hira kadan badan yana so ba.
        Washe gari ankai amarya gidanta, kawayen da abokai sunyi chilling masu yin yan mata nayi ansha Cece kuce shidai ango ba ehm ba ehm ehm, yana ta imagining dama teemah shi ce abar kaunar shi da yafi kowa jin dadi, haka dai suka watse aka bar amarya da ango, bayan rakiyar abokan shi ya dawo ya wuce dakin shi ya shiga wanka bai kuma waiwayen ta ba ya kwanta baccin ma dai sai barawo ne ya dauke shi.

       Itama bayan fitar su bata wani damu da dawowar shi ba tayi wanka tayi Sallah tayi addu a ta kwanta daman akwai gajia a tare da ita bata farka ba sai 6 har sai da tayi lattin sallar asuba.
     Da safe ta cancada kwalliyarta, tace bari ta zagaya gidan ta gani tayi deciding abinda zata nemar masu su ci, ta fita tayi zagayen gidan yayi kyau sosai ta gode ma Allah ta daya kaita wannan matsayin,, taji ana knocking tana budewa taga yan aike daga gidan su an kawo abinci,, ta jere su bisa dining table ta dauko duk abinda za a bukata ta zauna jiran megidan bai tashi fitowa ba sai kusan 12 saura yayi wanka sai kanshi yake, yana fitowa taje ta tare shi ya Areef ina kwana ya amsa a takaice, da fatan an tashi lfy tace lfy kalau, ga abinci umma ta aiko mana, ok na koshi yayi hanyar waje nizan fita bai jira amsar taba yayi waje,.
      
        Umman teemah ta dade bata farka ba, wannan ta farfado har a lokacin kuka take tana Allah wadai da halin da teemah ta tsinci kanta. Nan dai likita ya bata baki akan tayi hakuri jarabawa ce ta ubangiji haka Allah ya kaddaro, ta kwantar da hankalinta zai dora teemah akan maganin dazai  bata, zata dade sosai a dunia akwai masu cutar in ta gansu ma baza tace suna da cutar ba, sai sanda kwanan su ya kare, yanzu ma dasun zo da wuri asibitin ya daura ta akan maganin tun wuri da bai nuna a jikin ta ba haka, sai dai addua Allah ya kara kare wa, nan dai yayi   tayi wa teemah fada tana ta zubar da kwalla tana dana sanin rayuwar datai a baya, Allah ya yafe mata tana ta kuka. Nan dai doctor ya bata gado don samun karfin jikin ta da  kuma lfyr ta.

         Su Futha amare ana can ana tashan luv, don kuwa komai bata nema ta rasa ba haka duk wani motsi nata sai ya tambaya any problem? An sai mata wata arniyar mota "BENZ" sannan sunje honeymoon kusan 4 months sukai acan kasa she 4 suka je DUBAI, LONDON, INDIA, sai kuma suka wuce umara wato SAUDIA,, kai!!! A gaskia Futha tayi dace Allah yaba yan baya ma haka,, sun dawo 9ja a lokacin da karamin cikin ta wata 4 cip cip,, tayi zagayen dangi daga nan ta kira teemah tace zata zo ta kawo mata tsaraba tace sai tazo bata da lfy ma.

         Ta wuce daga gidan su, ta shiga da sallamar ta,, ta tarar da umman su a tsakar gida tana zaune ta gaishe a a Futha yaushe kuka dawo ne? Tace yau kwana 5 umma Allah sarki an dawo lfy, tace lfy kalau umma ya mai jiki ? Hmmm umma tace da sauki ta nuna alamar damuwa ai sai dai addua Futha Allah dai ya shirya mana zuri a tace Amin,, Futha dai bata gane me umma ke nufi ba don bata san meke faruwa ba, Ta mika mata tsarabar data kawo mata sannan ta shige dakin, Allah sarki umma harda kwallar ta dama tata yar itama bata jefa kanta cikin ukuba ba gashi nan yanzu tana dana sanin rayuwar ta.

      Futha na shiga da gudu ta taso ta rungume  ta tana murna,, Futha tace teemah wannan wane irin ciwo ne lokaci kankani kika koma haka kinyi baki,, kin kwanjame, kin rame, kamar bake ba,, hmmm nan fa suka zauna teemah ta fara kuka me tsuma rai hmm kedai bari yar uwa, kiga dai yanda na koma naki jin shawarar da kike ban da umma take ban da sauran mutane keban, yanzu ga halin dana saka kaina a ciki nan dai ta bama Futha labarin komai game da ciwon ta har yanda DR ya bata magani shine fa dalilin samun lafiyar ta har ta fara murmure wa,, yanzu dan kudin data tara dasu take siyan magani,, amman da kam whl da ta ganta baza ta gane taba,,, gashi yan unguwa da yan gari duk sunsan halin da nike ciki duk inda nayi sai  daria ake min nikam na shiga uku na lalace,, kuma kinsan waya saka mun wannan cutar Khalid ne,, sai gashi mun hadu dashi a wurin blood test,,, yace zaizo gida muyi magana har yau bai zoba.. Futha tayi kuka tayi kuka sosai ta kuma tausaya wa kawarta,, nan dai tayi mata nasiha me shiga jiki,  ("Toh yan uwa maza da mata kundai ga halin da kawata kuma aminiya ta futha yau yanda Allah ya maida ita kundai ji yanda take ada tana ganin rayuwar banza ita ce rayuwa har gani take ni ban waye ba, rayuwar banza lyk tara samari wannan yazo wancan yazo, aje ayi masha 'a a dawo ba a tsoron Allah ba a tunanin gaba,, kece wancan hotel wancan gida duk kina tunanin birgewa ne, whl ba birgewa bane karshe dai sai mutum yayi dana sanin rayuwa ko baka dauki cuta ba sai kayi dana sani,, don haka ina me bamu shawara yan uwa akan mubi dunia a sannu ba madauwama bace kuma abinda ka shuka shi zaka girba,, yar uwa kar kiyi ikirarin cewa sai me kudi zaki aura, da talauci da arziki duk na Allah ne, kedai kiyi adduar Allah yayi maki zabi nagari a duk abinda kika sa gaba,, Allah yasa mu dace dunia da lahira.") Ta bata shawarwari masu amfani a gareta da sauran yan uwa musulmai tace taci gaba da istigfari Allah yana son mai neman yafiya a gareshi,,, Ya Allah ka yafe mana dukkan kurakuran mu amin..sai kusan maghrib tabar gidan akan sai ta dawo duba ita nxt tym..

      Kai teemah ranar tayi dana sanin rayuwa tayi kuka tayi kuka har ta gaji ta kuma dau alkawarin duqufa ta nemi aljannar ta, dayin biyayya ga mahaifiyar ta da tilon yayan ta wanda yake uba a gareta a yanzu.

**Bayan shekara daya**

         Sai muka leka gidan su farouk inda muka hango su Rufaidah an zama yan gida hankalinta a kwance ta murmure abinta tana ta zuwa skul,, gata da kokari,,, tana birge farouk kullum ji yake yana kara kaunar ta a ranshi, komai take so shi ake mata a gidan tun daga kan mummy har su farouk,,, farouk ya kasa sanar da ita har yanzu yana sonta sai dai mummy ta gano shi kuma ita ma ta gano akwai wata a kasa don kullum suna tare in bata je skul ba daga ya dawo daga aiki,, mummy tayi deciding tayi musu maganar tunda taga alamar a tartare dasu,.

      Hakan kuwa akai ta tara su a parlour, take ce akwai magana duk suka saurare ta, tace so take ta aurad da kowa daga cikin su,, shi tayi mashi mata itama tayi mata miji,, nan fa suka fara kallon kallo,, toh fa me mummy ke nufi su dai sunsan suna son juna Amman basu gayawa juna ba gashi mummy na shirin yi masu tabargaza yaya kenan??

        Mummy tace kai farouk yar gidan Anty Laura, ke kuma rufaida dan gidan baba sani wato haisam,, nan gumi ya fara aikinsa a  jikin su, ita dai rufaida baza ta iya musawa ba duk wanda mummy ta bata zata karba, Amman fa tana kaunar ya farouk,,,. Farouk ne yayi gyaran murya mummy...... mummy..... ya kasa magana, tayi daria menene akwai magana ne? Yace ehhh tace ina jinka, daman... daman... ya kasa maganar ka fadi maganar ka ina jinka. Whl mummy ina da wadda nike so,, tayi murmushi irin na manya,, tace wacece wadda kake so din baka gayan ba sai yanzu danai maka matar ai babu fashi.

      Da sauri ya kalli rufaidah,, don Allah mummy kiyi hakuri whl inban aure ta ba zan iya shiga wani hali, ina sonta kamar raina,, wai wacece ne a ina take yar waye yar wata unguwar ce? Sai da ya gyara zama sannan yace mummy ba wata bace a cikin gidan ki take gata ma a kusa dake ya nuna Rufaidah..

      Mummy tayi daria take YAN QOTA ai daman so nake na tabbatar da abinda nike gani kuma nike ji a wurin kannan ku, toh Alhamdulillah daman haka nike son ji komai ya yi Allah ya sanya alkhairi a cikin lamarin,, yanzu sai muje neman auran ta a wurin yayarta ko,, Rufaidah da sauri tace a a mummy whl sai dai a tafi katsina daga baya a gaya mata in anje.

      Nan dai suka tsara yanda abun zai kasance zasu je katsina neman auran nata, don mummy bata son aja abun da sauri take so ayi wata daya kacal za a saka, murna a gidan ba a magana har fa yar walima aka hada....

               Urs.....
         🎋S💖B🌲R

[truncated by WhatsApp]

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts