MOTAR KWADAYI
By
Rash Kardam
6
Tunga wan'nan lokacin hafsat ta dawo hausa wa amina, ga wulakanci iri-iri, wata rana kawar hafsa mai suna asabe tazo nan suka kule adaki, hafsa ta bata lbr gd, asabe tace hafsatu ae bazama zakiyi ba, tashi zamuyi mushiga malamai kisamu kan mijinki(yan'uwa, wai itasamu kan maizatayi dashi? Mata muringa jin tsoron Allah zuwa gun boka ba abunda zai haifar wa mutum sai danasani da tsananin nadama, ga kuma tarin zunubi, mata muji tsoron Allah adaina biye ma kwayen banza masu bada gurbataciyar shawara, Allah ka tsare mu da zuwa gun boka ameen).
Nan hafsa tasa shewa aiko tace inaga ko yau muje,sukaje gun bika ya basu duk wani kule-kule da zai basu, tun daga wan'nan lokacin malam muhammadu ya canza wa amina, har hafsat ta haihu akasamu mace duk da baya da karfi saida tasa yayi abun fitan kunya, yarinya taci sunan Safiya.
Safiya tana samun kula daga innarta da malam, duk abinda hafsatu tasa shi yakeyi baya musu, amina kam ta dawo yar kalo a gdn bata iya katabus, abinci ma sai am samata wani sa'in, haka sukayita rayuwa a dafe har shekara tazago da watani, amina tana hakuri tana kuma rokon Allah ya bata ikon cin jarabawar da yamata.
Safiyar ranan alhamis amina ta tashi da zazazi mai zafi ga komai taci sai ta amayar dashi, ga yawan tara yawu, kwanata uku tana jin jiki kafin ranan yarta tazo dubata taga halin da take ciki, nan tayita fada sosai a gdn, kafin ta kaita asibiti, gwajin farko aka saida musu tana dauke da juna biyi na wata daya da sati 2, godia tayima Allah,( ni da candy muralna fal cikin mu, haka rayuwa take mutum yakasance mai hakuri da gode ma Allah a kowani hali kake sai ya maka sakayya da kyauta mafi kyau, kamar yanda yayi wa Amina).
Ko da suka dawo gd, aka shai da sa malam ba karamin murna yayina akasar zuciyarsa, amma afili yakasa furwa.
..........Na......
Rash Kardam
Friday, 24 February 2017
Home »
» MOTAR KWADAYI PAGE 6
MOTAR KWADAYI PAGE 6
Popular Posts
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(AUGUST 2016)* ...
-
MOTAR KWADAYI RASH KARDAM Duk launin kalan idonta, sun canza izuwa ja. Hannu tasa a tsakanin cinyanta tana mammatsewa,Bad Boy yana ga...
-
AMANA TA CE By ©Rash Kardam 1 Safiyan yau Jumma’ah antashi da sanyi, kasancewa yanayin Damina ne, Alhaji Al-hassa...
-
🐾🐾Raheenat🐾🐾 1 Yarinya ce yar kimanin shekara 12 ta yanko a guje ta fada jikin Dad...
-
MOTAR KWADAYI By Rash Kardam 21-25 Jan motar yayi, suka bar cikin Silver Sand Hotel, bai zarce da su ko ina ba, sai gid...
-
BAZATA By ©Rash Kardam 1 Yarin yace yar kimani 25 yrs ta fito daga office dinta, sanye cikin kayan l...
-
π»π»π»π»π»π»π»π» ππ»BABBAN KUSKERENππ» ππ»DANA TAFKA ππ» π»π»π» ππ»ππ» ...
-
[6/5/6:30pm] 🌲RASH KARDAM🌲🌲 & 🎋SADEEY S ADAM🎋 ...
-
°•°•°• *RUWA CIKIN COKALI*°•°•° _(Ya ishi mai hankali wanka)_ *{BASED ON TRUE LIFE STORY}* *(JULY 2016)* ...
-
π»π»π»π»π»π»π»π» ππ»BABBAN KUSKERENππ» ππ»DANA TAFKA ππ» π»π»π» ππ»ππ» ...
0 comments:
Post a Comment