New Post

Saturday, 11 February 2017

ZAMAN MAKOKI PAGE 11-15

???? *ZAMAN MAKOKI*????

                  *Na*

*Rash Kardam*
          *Ummieluff*

  Page
*11~15*

Burinta kawai abinci da drinks..kowanne cikin kawayenta taji anyi rasuwa toh xai sanar da d'an uwansa.. Su d'ebi juna zuwa gaisuwa kodako basusan suba..su zarah B B da Aneesa da Munay a gaba.. Na kalli rasheeda,itama ni take kallo atare muka had'a baki wurin fad'in,```ikon Allah!``` kuma duk in ka gansu a gidan rasuwa sun iya yanka manyan loma tamkar sunyi makarantar koyan manyan loma.

Khadija tayi makarantar primary da ke Tudun wada gata da k'ok'ari sosai tun tasowarta mayyar Candy ce ita ko kud'i ka bata bata damu ba gwara ka saya mata Candy milk yafiye mata komai sai shinkafa(shefe) ko aika taje bata wuce tayin shefe.
Ma haifiyar Candy tana k'ok'arinta gun yin aikatau na gida da 'yan kule-kulen kayan miya don ta tsare mutuncinsu abu d'aya da ya musu sauki gidan kansu suke bana haya ba inda rayuwan tazo musu da sauki kenan. Candy tana da kyau nagaban kwatance don tun tana k'arama wasu ke zuwa kamun kafa akan in ta girma suna sonta amma sam Ummanta taki ta ce?sai in yarinya ta girma ta amince da kanta tukunna".

Da wannan kalaman take ja ma masu sonta burki Umma ta kan d'aura ma Candy tallan sabulu da omo lokacin tana primary haka Candy zataje ta ajiye tallan ta kama carafke ko tambo sai lokacin komawa gida yayi ta fara zare ido ga kaya ajibge, in ta koma gida Umma zatayi ta mata nasiha kuma da kud'in da tayi ciniki dashi suke sayan abunda zasu ci ga Candy bata iya hakura da carakfe. wataran kuma ta nimi tsokana azubar da sabulum ta dawo gida tana kuka.

Randa 'yan mutuncinta suke kusa tayi talla tasayar duka tukun ta dawo gida randa batayi niya ba kuma inta zaga tayi d'an ciniki sai ta je gidansu Auta ta kwanta ta shari baccinta tun Hajiya na koranta har ta gaji ta daina in ta gama baccin sai tasai sabulun naira d'ari tukun Candy ta nufi gida.

         *```TAGWAYEN MARUBUTA```*

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts