New Post

Saturday, 11 February 2017

RUWA CIKIN COKALI..... PAGE 4

�?�?�? *RUWA CIKIN COKALI*�?�?�
    _(Ya ishi mai hankali wanka)_
*{BASED ON TRUE LIFE STORY}*
                *(JULY 2016)*

                          *NA*

*�Rashida .A. Kardam*
       
*N. W. A*
Page
*4*

_Kdeey ta d'auki ledar zuciyanta cike da tunani kala-kala ta nufi cikin gida "Assalamu'alaikum", tayi sallama Umma da ke tsakar gida ta amsa da "amin Wa'alaikumusalam" ta saki fara tare da fad'in "a'a 'yan makaranta ne sannu da dawowa, yanzu Malam ke tambayar ki kuwa asai kina hanya", Kdeey ta k'arasa cike da ladabi ta rusuna ta ce"Eh ina kan hanya ma Umma sannu da gida " Umma cikin sakin fuska ta amsa da "lafiya lau 'Yar Albarka ya karatun dai?" , Kdeey ta ce"Alhamdulilah! Barin k'arasa miki aikin", d'aki tashiga ta ajiye jakanta da hijab ta cire ta karb'i aikin ta fara._
_Umma bata zauna ba itama ta ci gaba da wasu ayyukan basu dad'e ba suka kammala aikin, d'aki suka dawo suka zauna kasancewa magriba ta k'usa Malam ne ya shigo da sallamansa su Umma da Kdeey suka amsa, Kdeey ta russana ta masa barka da yamma ya amsa cikin sakin fuska. Umma ne ta fito daga uwar d'akinta ta ce"Khadiyatu d'auko jakan makarantar ki na duba takar dunki",(Iyaye a cikin ku sauna wa Uwa take sa 'yar ta a gaba in ta dawo ta duba takardunta ko ta duba jakanta don sanin mai take fita dashi ko mai ta ajiye aciki, yana da kyau muna kula da shiga-da-ficen Yaran mu Allah ya kare mana 'Ya'Yan mu), Kdeey ta mik'e ta ce"au kinga na manta ma d'azu Aunty Samy ta min kyauta". Mik'ewa tayi tare da d'auko jakan da laidan ta ajiye a gefen Umma._
_Umma ta ce "Khadija d'auko min glass d'ina", Kdeey ta mik'e ta nufi uwar d'aki bata dad'e ba ta fito rik'e da k'aramin akwatin gilashi, sai da ta rusuna ta mik'a mata cikin ladabi da girmamawa. Umma ta janyo jakan makarantarta ta soma duba takardunta taga karatun da sukayi sannan ta cire glashi ta mayar da shi cikin ma'adaninsa._

                   *DEDICATED TO*
       *_KDEEY 'N' MRS AL'AMEEN_*

_Rash Kardam??_

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts