New Post

Friday, 24 February 2017

MOTAR KWADAYI 61-65

MOTAR KWADAYI??????

61-65

Da safe kuwa yanda naga, idon Ayshat ya yi ja, nasan ta niku ba kad'an ba. Khaleel ko sai tarairayata yakeyi, tamkar kwai. tundaga wannan rana suka shimfid'a soyayyansu, mai cike da burgewa, komai tare sukeyi, inka gansu gwanin ban sha'awa, Khaleel ta tattala matarsa, itama tana gudun abunda zai bata masa rai.

Ayshat tayi kyau ta k'ara haske. Niko Rash "nace anya wannan ,haske haka na kalau ba". Sannu a hankali rayuwa ke tafiya dad'i da ba dad'i, kayan garansu ya kare, randa inya samo musu mai maik'o suci. Randa in bai samu ba har garin kwaki suke ci, ko kad'an Ayshat bata taba nuna fushinta ba, kulum tana cikin masa, Addu'a da fatan alkairi.

Safiyar yau ta tashi da zazzabi mai tsanani, ga jiri da ke d'ebanta. Hankalinsa ya tashi matuk'a, gashi ko si-si bai kwana dashi ba. Ko dayaje gidansu, yatarar da iyayensa, gari kwaki suke sha, ya gaida su Mamansa tace"Khaleel lafiya na ganka haka?. Cikin damuwa yace"Aysha ba lafiya kusan sati d'aya, gashi banda ki naira a hannuna.�

"Yasalama towo gashi muma haka muka wayi gari, amma ga wancan tv kaje ka sayar sai a samu a mata jinya. Tv ya d'auka yaje ya sayar dubu biyar da d'ari bakwai, sukaje asibiti a ka mata gwaji, likita ya tabbatar da tana d'auke da juna biyu, har na wata hud'u. Magunguna ya rubuta musu, sauran ya sai musu kayan abinci, rabi ya kaimusu, saura ya kai ma su Ummansa. Ko da Ayshat ta samu sauki, yace ta shirya, kaita gidansu ta gaida iyayenta, daga nan suka wuce gidansu Khaleel da murnan Umma ta tarbeta, tarinka ina zansaka dake. Da daddare da zasu tafi, "Umma ta mata nasiha sosai, da takara hak'uri da yanda mijinta ke. Ayshat"tayi godiya ma Umma suka tafi.

Khaleel result ya fito yayi kyau sosai, yanzu aiki ya dunkufa nema, kulum sai ya fita amma shiru, Ayshat ko kulum tana cikin masa addu'a da fatan alkairi.

�Safiya kam harka take ba sanya, ta maida bariki kamar rigan sakawanta, ko shakka babu, yanzu motanta biyu, kud'i kuma ta tarasu ba'a magana. Samarukanta na da duk ta canza, Abuja kuma ya dawo mata kamar gida.

Kwanki sun ja, Aysha ta shiga watar haihuwanta, Khaleel ko kula ta musamman yake bata, yana tattala yar matansa. Safiyar yau ta tashi da nakuda, hankalin Khaleel ya tashi, mai napep ya nimo suka nufi asibiti, aka shiga da ita labour room, "addu'a yaketayi Allah ya sauketa lafiya.

Wayarsa kiran nokia, irin mai tocin nan, ya kira Baban Aysha ya sanar ma, ya kira gidandu ma ya fad'a musu.

Ayshat ta kasa haihuwa da kanta, likitoci sukazo suka sanar masa dole sai an mata tiyata. Ba k'arami min tashin hankali ya shiga ba, don kud'in da ya tara 8k ne, ana haka sai ga iyayensa, nan ya sanar musu, Malam yace"abasa ruwa a kofi da ruwa, murfin flaks aka miko masa, Addu'a ya yi, dake wanda suke kanta mudulmai ne, ba'a samu matsala ba, sukabata cikin ikon Allah ba'ayi minti biyar ba, ta zankad'o yaranta guda biyu, mace da na miji. Wayyo karkuga murna gun khaleel, bayan nurses sun gyarata, ta huta suka dawo gida. Yan'uwa da abokan arziki sai murna sukeyi, Khaleel daman ya sai ragonsa yana kiwo bai samu matsalaba, ana gobe sunane aka kirasa ne, fidelity bank suka kirasa, daman ya rubuta musu Application, ya samu aiki a gurin. Cikin murna ya zo gida ya sanar musu kowa sai murna yake masa. Ko ni Rash nayi murna sosai, gaskiya yan biyu sunzo da goshi.


0 comments:

Post a Comment

Popular Posts